✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shari’ar Kisan Hanifa: An hana ’yan jarida shiga kotu

’Yan jarida sun yi curko-curko gabannin ci gaba da sauraren shari'ar a kotu.

An hana ’yan jaridar da ke daukar rahohon shari’ar kisan Hanifa Abubakar shiga kotun da ake ci gaba da sauraren shari’a a ranar Laraba.

A lokacin zaman sauraron shari’ar da ke gaban babbar kotun da Mai Shari’a Usman Na’abba, ana sa ran hukumar tsaro ta DSS za ta bayar da shaida a kan wanda ake zargi da kiran karamar yarinyar mai shekara biyar.

An sanya karfe 10 na safiyar Litinin a matsayin lokacin fara zaman kotun, amma har zuwa karfe 12 na rana ba a fara sauraren shari’ar ba.

Rahotanni sun bayyana cewa Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Lawan, ne ya bayar da umarnin hana ’yan jarida shiga kotun.

Aminiya ta rawaito cewar Gwamnatin Jihar Kano ce ta shigar da karar Abdulmalik Tanko tare wasu, kan zargin su da yin garkuwa tare da kashe Hanifa Abubakar, yarinya mai shekara biyar a duniya.

Laifin da ake zargin nasu ya saba da sashe na 97, 274, 277 da kuma 221 na kundin ‘Penal Code’.