✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar Sauyin kudi: Kotun Koli ta je hutu

Alkalan Kotun Koli da ke sauraron shari'ar sauyin kudi tsakanin gwamnatocin jihohi 13 da Gwamnatin Tarayya sun tafi hutun rabin lokaci.

Alkalan Kotun Koli da ke sauraron shari’ar sauyin kudi tsakanin gwamnatocin jihohi 13 da Gwamnatin Tarayya sun tafi hutun rabin lokaci.

Alkalai bakwai karkarshin Mai Shari’a Inyang Okoro sun ce sun tafi hutun ne domin ba wa lauyoyin bangarorin da ke shari’ar damar yin musayar takardu.

Hakan na zuwa ne bayan Jihar Ribas ta shiga jeri a matsayin ta 13 a cikin jihohin da ke kalubalantar sauyin kudin da gwamnati ta yi.

Tun da farko, Mai Shari’a Inyang Okoro, ya ce ya zama tilas kotun ta cimma matsaya a kan shari’ar a zamanta na yau.

Zama na biyu ke nan da Kotun Kolin ke sauraron karar da jihohin suka maka Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Najeriya suna neman kotun ta hana bangaren gwamnatin aiwatar da wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudin da aka sauya wa fasali.