✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shatu Garko: Bakanuwa ta lashe Gasar Sarauniyar Kyau

Shatu mai shekara 18 ita ce mace ta kadai mace mai sanya lullubi da ta shiga Gasar Sarauniyar Kyau

Shatu Garko daga Jihar Kano ta lashe Gasar Sarauniyar Kyau ta Najeriya ta shekara ta 2021 da ka gudanar.

Shatu Garko mai shekara 18, wadda ita ce kadai mace mai sanya mayafi da ta shiga gasar, ta lashe gasar ce a matsayin wadda ta wakilci yankin Arewa maso Yamman Najeriya a gasar.

Tuni aka dora mata kambi a matsayin Sarauniyar Kyau ta Najeriya ta 2021, bayan alkalan gasar sun ayyana ta a matsayin gwarzuwar gasar ta bana, inda ta doke sauran abokan karawarta 17.

A ranar Juma’a 17 ga watan Disamba, 2021, ne aka sanar da Shatu Garko a matsayin sabuwar Sarauniyar Kyau, bayan Etsanyi Tukura, daga Jihar Taraba da ta lashe gasar karo na 43 a 2019.

Kyaututtukan da ta samu na lashe gasar sun hada da kudi Naira miliyan 10 da sabuwar mota sannan za a kama mata daki na tsawon shekara daya kyauta a wani katafaren otal.

Wadda ta zo ta biyu a gasar ta bana ita ce Nicole Ikot, sai kuma Kasarachi Okoro da ta zo a matsayi na uku.

Gasar ta bana wadda ta gudanana a Cibiyar Landmark da ke Ungwar Victoria Island a Legas, ita ce karo na 44 da aka gudanar da ita a Najeriya.