✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shawara da jan hankali ga maniyyata Umarah a bana

A wannan karo hankalin GIZAGO (08065576011) ya juya ne zuwa ga al’amuran jimami da muke ciki sanadiyyar annobar Kurona. Ga shi watan Azumin Ramadan ya…

A wannan karo hankalin GIZAGO (08065576011) ya juya ne zuwa ga al’amuran jimami da muke ciki sanadiyyar annobar Kurona. Ga shi watan Azumin Ramadan ya zo, yayin da hukumomin Saudiyya suka dakatar da Umarah a bana. Dalili ke nan yake jan hankalin duk wanda ya yi niyyar Umarah ya karkatar da niyyarsa zuwa ga…

 A duk shekara sai ka je Umarah, kana barin al’amura masu matukar muhimmanci a kauyenku ko garinku. Domin a lokacin da ka debi makudan kudi ka tafi Umarah a cikin danginka na jini, da ke kanenka ne uwa daya, uba daya, wani yayanka ne, amma bai da aikin yi ko sana’ar yi, zaman kashe wando yake yi. Ko yana sana’ar ma, wannan cutar ta Kurona ta kassara masa jali.

Tunda bana babu zuwa Umarah, maimakon dukiyar da ka adana a bana don zuwa Saudiyya, kamata ya yi ka tallafa musu da jari, ko dan abin da za su yi wa iyalansu hidima a azumin nan.

Kasancewar bana babu Umarah kuma al’umma na cikin ukubar Kurona, ka sani cewa cikin makwabtanka, akwai mai yin buda- baki da tsurar-bakin-ruwa, shi da iyalinsa ba su da hatsin da za su sa a cikinsu. Ya kamata ka dauki kudin nan da ka yi niyyar tafiya Umarah, ka taimaka wa makwabcin nan naka da hatsi da dan abin da zai dadada wa iyalinsa. Babu mamaki ladar da za ka samu, ta fi ta tafiyarka Umarah, tunda Allah na taimakon duk wanda ya taimaki fakiri, balle makwabcinka.

Wannan shekara dai annobar Kurona ta hana zuwa Umarah. Malam mai burin yin ibada, ga wani babban aikin da zai maye maka gurbin Umararka ta bana – Ga matasa nan a unguwarku suna ta zaman kashe wando, babu aikin yi, babu sana’a kuma Kurona ta kara gigita su. Maimakon ka ajiye makudan kudin nan da ka yi niyyar Umarah, da za ka ware Naira dubu dari uku kadai, ka raba wa matasa uku a matsayin jari ko ka koya musu sana’a, lallai da ladar da za ka samu sai ta fi ta Umarar. Dalili kuwa shi ne, idan Allah Ya albarkaci jarin, sai ka ga sun ginu da kafafunsu, sun samu abin rayuwa.

Da haka za su yi aure, su kafa zuriya, sannan su amfanar da al’umma gaba daya. Idan suka yi haka, ka ga ka zama sanadiyyar kafa arziki ga al’umma. Ya maniyyacin Umarah a bana!

Kada ka yi takaicin rashin zuwa wannan ibada saboda matakan hanawa da hukumomin Saudiyya suka dauka. Domin kuwa za ka iya canja niyya, ka yi aikin jinkai da ita, wanda shi ake matukar bukata a wannan lokaci.

Wani ma cewa ya yi wadansu ma kudin ba na Allah-da-Annabi ba ne, dukiyar al’umma ce suke kwashewa suna bidirin gabansu. Ni kuwa na ce, haba dan uwa, a matsayinka na ma’aikacin gwamnati, don ka yi kashe-mu-raba da dan kwangila, ka wawashe dukiyar da za a sama wa al’ummarka ruwan sha ko za a gina musu asibiti, ka handame kai kadai, wai don ka tafi Saudiyya Umarah; me wannan ibadar za ta tsinana maka?

Ka tuna, mutum nawa za su fada cikin halin kaka- ni-ka-yi a yankinku a sanadiyyar rashin ruwan sha mai tsafta, tunda ka kwashe kudin da za a samar da ruwan? Ko kuwa za ka iya lissafa marasa lafiyar da za su tagayyara, a sanadiyyar kudin maganin da ka kwashe, don wai ka tafi Umarah? Ko kuwa za ka iya biyan diyyar rayukan da za su salwanta a sanadiyyar wannan son kai da ka yi, inda ka kwashe kudin al’umma, kawai domin ka tafi galarin gabanka? Da ka san alhakin da ka dauka, da ba ka yi haka ba. Da ka bar dukiyar mutane, an yi musu aikin da ya dace da ita.

Kuma wani abin takaici ma shi ne, wadansu attajiran suna tafiya Umarar ce kawai da nufin guje wa aikin alheri a yankunansu. Da zarar an fara azumi, sai su tarkata iyalinsu, su hau jirgi sai Saudiyya. Za ka samu makwabtansu suna rayuwar talauci, wadansu ma da kyar suke samun abin buda-baki. Idan Sallah ta zo ma, haka za su yi bikin ba tare da sabuwar sutura ba. Wannan a can baya ke nan, domin yanzu annobar Kurona ta kara haddasa wa al’umma kunci da yunwa.

Da abin samu ne, adadin kudin nan da ka yi niyyar tafiya Umarar nan, kamata ya yi ka yi amfani da su wajen kyautata wa ’yan uwa da makwabta. Kamata ya yi a ce ka yi amfani da kudin Umarar wajen sama wa fakirai abinci mai rai da lafiya, ka sama musu suturar da za su yi farin ciki da ita a ranar Idi. Babu shakka, irin ladar da za ka samu, na tabbatar sai ta fi ta tafiya Umarar da ba ka samu yi ba a bana.

A yau, makarantunmu na boko da na Islamiyya suna cikin matsala. Za ka ga babu kujeru da tebura, wasu ma makarantun rufinsu a kware yake, suna yoyon ruwa da damina. Babu isassun littattafan karatu da sauran kayan aikin koyarwa. Malaman suna cikin takaicin rashi ko karancin albashi.

Ga shi kuma wannan  annoba ta Kurona ta ninka matsalolin al’umma. Maimakon a ce attajiran unguwa sun zanzare sun dauki makudan kudi sun tafi Umarah, da so samu ne, su yi amfani da rabin kudin wajen inganta makarantun nan,  musamman wajen tallafar malaman da kuma gyara ko inganta makarantun. Allah kadai Ya san irin gwaggwabar ladar da mutum zai samu wajen bunkasa ilimi. Lallai ya kamata a daure a jarraba wannan babban aiki, tunda dai bana babu wannan tafiya.

Na taba samun labarin wani attajiri, wanda ya ce shi daga yau ya daina zuwa Umarah. Wata rana ce ya shirya kudinsa, ya nufi tafiya Umarah, sai Allah Ya kaddara ya makara, jirgi ya tashi ba da shi ba, da ya dawo gida, sai Allah Ya sanya masa ilhamar yin sadaka da kudin. A ranar ya sanya aka tara masa fakirai na unguwarsu wajen mutum goma, ya raba musu Naira dubu dari-dari.

A sanadiyyar wannan kyauta daya da ya yi musu, ya ce har shekarar ta dawo ba a daina gaida shi cikin mutunci ba. Ya ce sai ya koma kamar wani waliyyi a unguwar tasu. Kullum suna yi masa addu’a, wadansu kuma suka koma kamar surukansa. Haka kuma, cikin fakiran nan, akwai wadanda suka same shi, suka sanar da shi cewa sun mike da sana’o’insu, sun kuma samu alheri mai yawa.

Shin da Umarar ya tafi da kudin nan, anya wannan abin alheri da ya samu a yankinsu zai samu? Dalili ke nan duk shekara, maimakon ya tafi Umarah da irin wadannan kudade, sai ya rika tara fakirai yana yi musu hasafi. Wani lokacin kuma sai ya rika gyara makarantu ko ginawa da yashe kwatocin unguwa.

Ni Gizago, ba adawa nake da masu zuwa Umarah ba kuma ba murna nake don hukumomin Saudiyya sun dakatar da aikin Umarah a bana ba, ni dai ina nufin attajiranmu su rika sara suna duban bakin gatari. Tunda ka je Umarah sau daya kuma ka yi aikin Hajji sau daya, to dubi dan uwanka, shi ma ka huce masa takaici. Wannan shi ya fi alfanu fiye da ka ajiye kudin da ka yi niyyar kashewa a Umarar bana, alhali al’ummarka da ’yan uwanka suna cikin halin talauci da fatara.

Wannan ra’ayin Gizago ne. Idan ya dace da naka, to mu dukufa rokon Allah Ya kawo mana sauki, Ya sanya mu cikin ’yantattu a cikin wannan muhimmin wata mai albarka na Azumin Ramadan!

A sha ruwa lafiya!