✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shawarwari 50 ga matan aure

A wannan zamani mata suna cikin zullumi saboda yadda aurensu yake yawan mutuwa.

Da sunan Allah Mai gamammiyar rahama Mai jinkai. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabin rahama da alayensa da sahabbansa da dukkan wadanda suka bi tafarkinsu har zuwa Ranar Tashin Alkiyama.

Bayan haka shakka babu, a wannan zamani ’yan mata da zawarawa kai har ma da matan aure suna cikin zullumi da tsoro da rashin kwanciyar hankali, saboda yadda aurensu yake yawan mutuwa, bayan kuma an dauki dogon lokaci ana soyayya a tsakani.

Don haka, ga wasu shawarwari wadanda idan mata suka yi la’akari da su insha Allahu za a samu kyautatuwar zaman aure.

Muna addu’ar Allah Ya ba da ikon kiyayewa.

1- Aurenki ya zama domin neman yardar Allah kika yi ba don tara abin duniya ba.

2- Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin aure.

3- Ki zaba wa ’ya’yanki uba ta hanyar auren wanda kika yarda da addininsa da dabi’unsa har ma da dangantakarsa.

4- Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki.

5- Kada ki zama mai kaurace wa shimfidar mijinki.

6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.

7- Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.

8- Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya iri-iri.

9- Ki zama kwararriya wajen iya girki nau’i-nau’i.

10- Ki zama kin iya barkwanci a magana wajen bai wa mijinki dariya.

11- Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk abin da mijinki ya ba ki.

12- Ki rika wanke bakinki da safe da yamma da kuma lokacin kwanciya barci.

13- Ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki, abincinki da sauransu.

14- Ki rika girmama iyayen mijinki da ’yan uwansa da abokansa.

15- Kada ki zama mai satar kayan mijinki.

16- Kada ki zama mai satar fita zuwa unguwa.

17- Ki guji leke a gidan mijinki, don yana daga cikin abin da yake raba aure a tsakanin Hausawa.

18- Ki rika gode wa mijinki a cikin abin da ya ba ki.

19- Ki kiyaye abin da mijinki ya fi so.

20- Ki kiyaye abin da mijinki ya fi son ci da safe, rana da kuma dare.

21- Ki rika yaba wa kwalliyar mijinki.

22- Ki rika yawan neman shawarar mijinki a kan duk wani al’amari da za ki yi.

23- Ki yi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar mijinki.

24- Ki rika sanya turaren wuta a dakinki, kuma ki kasance mai sanya turare a jikinki a duk lokacin kwanciya.

25- Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki kafin dawowar mijinki.

26- Kada ki bari mijinki ya dawo ya same ki gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da kiyayya.

27- Ki zama mai yawan canja zanen kunshin kafarki da kuma zanen kitso.

28- Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abin da ba ya da ikon saye.

29- Lallai ki yi amfani da ilimi wajen yanke duk wani hukunci.

30- Ki yi shiru a duk lokacin da mijinki yake yi miki fada ko nasiha.

31- Kada ki zama almubazzara marar tattali.

32- Kada ki tara kayan wanki da yawa a daki, naki ko na mijinki suna wari.

33- Ki tanadi kayan kwalliyar gida bayan na zuwa unguwa.

34- Ki kula da yanayin da zai nuna miki cewa mijinki yana cikin nishadi ko damuwa.

35- Kada ki rika bai wa kawayenki labarin sirrin da ke tsakaninki da mijinki.

36- Idan za ki yi wa mijinki magana ki yi masa da tattaunsan harshe da murya mai karya zukata.

38- Ki zama kin iya kallo mai nuna alamun sha’awa ko soyayya.

39- Idan kika samu sabani da mijinki ki ba shi hakuri ko da kuwa ke ce da gaskiya.

40- Ki zama mai tattali a cikin duk abin da kika mallaka a gidan mijinki.

41- Kada ki zama mai kwauron bai wa dangin mijinki abin da ya umarce ki, ki ba su.

42- Kada ki zama mai yin dare wajen girki.

43- Kada ki zama uwar adashi ba tare da sanin mijinki ba.

44- Kada ki zama mai yawan fada da makwabtanki.

45- Kada ki kasance mai yawan zagi ko ashariya.

46- Kada ki rika bai wa iyayenki labarin laifin da mijinki yake miki.

47- Ki zama mai hakuri da juriya da halayyar iyayen mijinki da ’yan uwansa.

48- Idan mijinki ya yi miki laifi kada ki nuna masa bacin ranki a gaban iyayanki ko ’yan uwansa.

49- Kada ki rika daga murya sama idan kuna sa-in-sa da mijinki.

50- Kada ki rika bai wa ’yan uwan mijinki labarin laifuffukansa.

51- Kada ki ci wani abu da mijinki ba ya son warinsa misali tafarnuwa.

52- Ki rika yi wa mahafiyar mijinki ihsani da ’yan uwansa.

Mun samo rubutu ne daga shafin facebook na Ja’afar Mahmud Adam