✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shehu Danfodiyo ba ta’addanci ya yi ba —Sarkin Musulmi

Danfodiyo shugabanci ya yi ba mulki ba.

Mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa ayyukkan da Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo ya yi ba ta’addanci ba ne.

Sarkin ya ce Shehu Mujaddadi ya yi abubuwa ne na taimakon addini ba ta’addanci ba kamar yadda wasu tsirarun mutane suka fara yadawa a wasu kafofi don cin zarafinsa.

A kalamansa wajen taron Mauludin Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo karo na 14, wanda aka gudanar a harabar Masallacin Shehu a birnin Sakkwato, ya ce “muna aiki da gwamna kafada da kafada domin taimaka wa al’umma da addinin Musulinci.

“Littafan nan da muka buga, gwamnati da kanta ta dauki nauyin buga su.

“Muna kara godiya ga Gwamna da kokari da ayyukkan da ake yi, muna so kira ga wakilin gwamna ya mika gaisuwa da godiyarmu,” a cewarsa.

Ya kara da cewa, “Danfodiyo shugabanci ya yi ba mulki ba, muma ba mulki muke yi ba, akwai bambanci yanda muke yi da yadda wasu ke yi.

“Akwai littafan da muka samu na kakanninmu guda 313, mun buga 100 da aka fassara cikin harshen Turanci da Hausa da aka rubuta a cikin harshen Larabci.

“Mun raba littafai miliyan daya da 600 don a san a ayyukkan da suka yi na jagoranci sabanin abin da wasu ke fada wai sun yi ayyukkan ta’addanci.

“Da ba a yi shehu Usman ba Allah da kadai Ya san inda muke mu Musulmin kasar.

Shugaban Darikar Kadiriya na Najeriya Sheikh Karibullah Nasiru Kabara a wurin taron ya yi kira ga Musulmi a Afirka su rika sauraron magana irin ta Mujaddadi Shehu Usman don shi baiwa ce da Allah Ya kawowa yankin.

“A wannan lokaci mai rintsi ga masu addini, mu fada wa kanmu gaskiya.

“Ba abin da zai tseratar da mu da samun zaman lafiya kamar sanya karatun Mujaddadi a gaba, ana karantawa da gaskiya a makarantunmu, sannan a sanya a manhajin karatun boko.

“Hakan zai dawo da martabar Musulunci da kwarjininsa.”