✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Adam Tula: Malamin da ya shekara 80 yana karantarwa

Sheikh Adam Tula, fitaccen ahehin malamin Musulunci da ya shafe shekaru 80 yana karantarwana kasar Habasha, ya rasu yana da shekaru 110 da haihuwa. Sanarwar…

Sheikh Adam Tula, fitaccen ahehin malamin Musulunci da ya shafe shekaru 80 yana karantarwana kasar Habasha, ya rasu yana da shekaru 110 da haihuwa.

Sanarwar rasuwarsa ta bulla ne ta shafin Dokta Muhamed Salah na Facebook, bayan ya shafe shekaru 80 yana karantar da litattafan addinin Islama daban-daban.

Kungiyar Wayar da Kai Kan Shugabanci ta Kabilar Oroma (OLLAA) da margayin ke koyarwa karkashinta, ita ma ta fitar da makamanciyar sanarwar shafinta na Twitter, inda dalibansa da sauran al’ummar kasar suka yi masa addu’ar samun rahama.

Duk da har yanzu ba a bayyana musabbabin rasuwarsa ba a hukumance, rahotanni na nuna lafiya kalau ya rasu.

Shehin malamin dai ya yi fice  wajen karantar da Alkur’ani, da Hadisi ga al’ummar Habashan.

Haka zalika karkashin kungiyar OLLAA da yake karantarwa, suna wayar da kan al’ummar kabilar Oromo da tafi kowacce yawan al’mma a Habashan kan al’amuran kasar, hadi da sauran ’yan kasar da aka danne wa hakki.