✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sheikh Gumi ya sake shiga daji yawon yi wa Fulani da’awa

Shehin Malamin nan na Sunnah, Dokta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya sake shiga jeji domin fadada da’awarsa ta yi wa Fulani makiyaya wa’azi a rugagensu.…

Shehin Malamin nan na Sunnah, Dokta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya sake shiga jeji domin fadada da’awarsa ta yi wa Fulani makiyaya wa’azi a rugagensu.

Wani shafin malamin na Facebook wanda ba a tantance ba ya nuna hotunansa a wata ruga yana tsaka da wa’azi da rarraba littafai.

Shafin ya ambaci cewa fitaccen malamin ya yi wa’azin ne ranar Asabar a rugar Malam Sule da ke cikin wani jeji a Karamar Hukumar Chikun  ta Jihar Kaduna.

Kazalika, sanarwar ta ce malamin ya yi al’ummar rugar alkawarin gina musu makaranta da asibiti.

Sakon da shafin ya wallafa  ya ce, “A yau 30 ga watan Janairun 2021, Allah ya azurta Malam da sake shiga dajin Kan Rafi Rugar Malam Sule da ke Karamar Hukumar Chikun.”

“Inda ya je ya yi musu wa’azi tare da alkawarin gina musu makaranta asibiti.”

A baya bayan nan ne Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle ya nemi Sheikh Gumi ya fadada yawon da’awarsa zuwa Jihar Zamfara domin yi wa ’yan bindiga wa’azi su tuba su daina miyagun ayyuka.