✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Gumi ya yi wa El-Rufai raddi kan ’yan bindiga

Ba dalili don ba su san addini ba a kashe su, sai dai in ba ka da bambanci da Boko Haram

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi raddi ga Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da sauran masu sukar shawararsa ta yin sulhu da ’yan bindiga.

Da yake jawabi kan shawarwarin da ya bayar kan hanyoyin kawo karshen ta’addancin ’yan bindiga, malamin ya ce bai taba yin kira cewa gwamnati ta biya ’yan ta’adda diyya ba.

Sheikh Gumi ya bayyana cewa ’yan bindiga sun hada da barayi, ’yan fashi da kuma masu ta da kayar baya, wadanda ya ce su ne kashi 90% na ’yan bindiga Fulani.

Idan ba a manta ba, a ranar Litinin Gwamna El-Rufai ya soki shawarar malamin na yin sulhu da ’yan bindiga da Fulani a yankin Arewa maso Yamma da malamin kuma abokinsa ya bayar.

El-Rufai, a hirarsa da Sashen Hausa na BBC, ya ce Fulanin ba su san addini ba kuma babu wanda ya tsokane su, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi sulhu ko biyan su diyya ba sai dai ma ta yake su.

Abin da ya sa Fulani daukar makamai

A kan haka ne Aminiya ta tuntubi Sheikh Gumi, wanda ya shaida mata cewa yawancin makiyaya sun koma daukar makamai ne saboda shekarun da aka dauka jami’an tsaro na zaluntar su, suna kashe su da dabbobinsu, kona gidajensu da cin kudadensu.

Fitaccen malamin ya ce an samu gagarumar nasar a tattaunawar da ya yi da makiyaya a ziyarar da ya kai musu a cikin dazukan Jihar Zamfara.

Ya ce makiyayan sun ba shi tabbacin ajiye makamansu matukar gwamnatin jihar za ta samar musu da cikakken tsaro.

“Mutane ne da ke fama da tashin tashin hankali, don haka suka dauki makamai don kare kansu.

“Duk inda suke a matsayinsu na makiyaya suna fuskantar matsala da manoma; mun ga abin da ya faru a Oyo, inda aka kona gidajensu da shanunsu.

“Suna zaune ne a cikin bukkoki wadanda ke kashe su da rusa gidajensu kuma na zaune a gidaje na alfarma,” inji shi.

Ba hujja ba ce

Mashahurin malamin ya ce ba daidai ba ne a kai hari a kashe mutanen da ba ruwansu; kazalika kuskure ne a kona dukiyar munate don an shafa musu kashin kaji cewa masu laifi ne.

Ya bayyana cewa hanya mafi dacewa ta magance matsalar tsaro ita ce wayar da kan makiyaya da rungumar su a matsayinsu na ’yan Najeriya.

“Ba masu laifi daga cikinsu nake magana a kai ba, saboda a cikinsu akwai masu laifi kamar yadda ake da masu aikata manyan laifi, ’yan fashi, da garkuwa da mutane a cikin Yarabawa. A cikin Igbo ma akwai ’yan fashi da masu garkuwa da mutane

“Abin da nake cewa shi ne ba za a yi wa kowane makiyayi kudin goro ba saboda masu miyagun cikinsu.”

A ba su hakkinsu kafin a hukunta su

Da yake magana game da kalaman El-Rufai cewa babu wanda ya takali Fulanin don haka ba su cancanci a biya su diyya ba, Malamin ya ce:  “Ba wanda ya ce a biya masu laifi diyya, amma kashi 90% na makiyaya sun yi fama da zaluncin sojoji.

“An kashe iyayensu, sun rasa dabbobinsu da gidajensu saboda ayyukan soji don haka sai a biya su diyya.”

Ya ce rashin sanin addini daga bangaren sun ’yan bindigar ba hujja ba ce a kashe su kamar yadda El-Rufai ya ke cewa.

“Don mutum bai san addini ba, ba hujja ba ce a kashe shi, koyar da shi addini za a yi; Idan ba haka ba kuma ba ka da bambancinka da akidar Boko Haram masu kiran mutane mushirikai suna kashe su?

“Makiyayan nan an bar su cikin matsananciyar fatara, ga rashin kulawar gwamnati da nuna wariya amma kana nan kana ta surutu.

“Da kudin da za ka kashe a sayen jirgin yaki, me zai hana ka gina musu makarantu da hanyoyi da asibitoci ba. Dole ka ba su hakkinsu kafin ka fara tunanin za ka kashe su.”

Gwamnatin Kaduna ba ta taimakawa

Malamin wanda tun a watan Janairu ya fara shiga kauyukan Fulani a Jihohin Kaduna da Zamfara da Sakkwato don wayar da kansu su bar ta’addanci, ya bayyana takaicin rashin samun goyon bayan Gwamnatin Jihar Kaduna.

“Jihar Zamfara ta kira ni kan yadda zan taimaka, a Kaduna na yi kokari na gina musu makarantu daga aljihuna, amma gwamnatin ba ta taimakawa. Amma nan (Zamfara) kira ta suka yi in zo in taimaka, ta yaya za mu iya zama a inda ba a taimaka mana,” inji Sheikh Gumi.

Ya ce an riga an fara koyar da makiyaya addinin Musulunci inda aka raba musu littattafai bayan nuna sha’awarsu da neman ilimi a Zamfara.

“Ba za mu yi watsi da su ba. Ina da hotunan yadda kananan yara mata ke shan ruwa a kududdufin da dabbobinsu ke sha. Ba su da abubuwan more rayuwa; ko asibiti ba su da shi, amma muna can muna ta surutu.”