✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Ibrahim Khalil ya fice daga APC

Sai dai bai bayyana makasudin ficewar ko kuma jam’iyyar da zai koma a yanzu ba.

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Jihar Kano, kuma Shugaban Majalisar Malaman Jihar, Sheikh Ibrahim Khalil ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki.

Malamin dai ya shaida wa Aminiya cewa tuni ya rubuta takardar ficewar tasa daga jam’iyyar, ko da yake bai kai ga mika ta Shugabannin jam’iyyar na Jihar ba, saboda rikicin da ake ci gaba da fuskanta a cikinta.

“Na rubuta takardar, kuma ina jiran hukuncin kotu ne a kan rikicin jam’iyyar kafin in mika ta ga halastaccen shugabanci,” inji shi.

Shehin malamin ya ce tun a watan Nuwamban da ya gabata ya yi yunkurin ficewa, amma sa bakin da Majalisar Malamai da Gwamnatin Jihar suka yi ya sa ya jinkirta.

Sai dai ya ce ba zai bayyana makasudin ficewar tasa ba, ko kuma jam’iyyar da zai koma a yanzu.

Sheikh Ibrahim Khalil dai ya taba zama mai ba Gwamna Shawara a gwamnatin APC ta Abdullahi Umar Ganduje a Jihar Kano.

Bugu da kari, a ’yan watannin baya ya tsinci kansa a rudani a shugabancin da yake wa Majalisar Malaman Jihar.