✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Rijiyar Lemo: Bayan tsanani akwai sauki (2)

Allah Yana cewa, lallai a tare da tsanani akwai wani sauki.

Na daya: Lallai bawa idan bakin ciki ya yi masa tsanani, cututtuka da musibu suka tsananta masa, to, lallai shi yakan yanke kauna daga kowane abin halitta ya ta’allaka ga Mahalicci.

Saboda yayin da abu ya yi tsanani, mutane sun gwada wannan hanya, sun gwada waccan hanyar ba su samu sauki ba, to za su ce babu wanda zai yi musu magani, duk za su koma ga Allah.

Yayin da suka koma ga Allah, suka rike Shi, Shi kadai to a lokacin, sai a samu maganin wannan bala’i da wannan musiba da suke ciki.

Duk lokacin da mutum ya dogara ga Allah ya koma gare Shi, to Allah (SWT) Ya ishe shi komai.

“Duk wanda ya dogara ga Allah, to Allah Ya ishe shi komai. Duk wanda ya kiyaye dokar Allah kuma, to Allah zai sanya masa sauki a al’amuransa.”

To in da mutane za su gwada hanyoyin samun mafita iri-iri, su ga cewa babu mafita, babu abin da suke nema, to za su koma ga Allah ne. Suna komawa ga Allah kuma sai ka ga sauki ya zo. A

llah (SWT) Ya ba mu labarin mutum uku wadanda ba su fita Yakin Tabuka tare da Annabi (SAW) ba, wadanda aka jinkirta karbar tubarsu, suka shiga cikin wani hali mawuyaci mai tsanani.

Har suka dauka cewa kamar ma sun hallaka, sai Allah (SWT) Ya ce: “Allah Ya karbi tubar mutane guda uku wadanda aka jinkirta karbar tubarsu.

“Har yayin da kasa ta yi musu kunci, duk da yadda take da fadi, zukatansu suka yi musu kunci, suka tabbatar babu matsera daga Allah sai zuwa gare Shi, (babu inda za ka je ka tsere wa Allah, sai dai ka koma wajenSa).”

To a nan ne Allah (SWT) Ya karbi tubarsu. To haka duk sa’ar da mumini ya koma ga Allah, to, Allah zai karbi tubarsa Ya ba shi mafita.

Na biyu: Lallai bakin ciki da masifa idan suka tsananta ga bawa mumini, sai ya kasance yana fada da Shaidan.

Shaidan zai zo masa yana sa ya yanke kauna, sai ya tashi ya kama yaki da Shaidan.

In mutum ya yi addu’a, ya yi addu’a, amma bai ga an amsa ba, sai Shaidan ya zo ya rika sa masa a zuciya cewa ka fitar da rai kawai.

Ta hanyar yakar Shaidan sai ya kasance ladansa shi ne Allah zai dauke masa wannan bala’i Ya kare masa wannan cuta.

Wannan yana daga sabuban dauke bakin ciki ta hanyar tsanantar bakin ciki.

Abu na uku: Idan bawa ya yawaita addu’a ya yawaita addu’a al’amari yana kara tsananta, harkoki suna cabe masa, to, zai dawo yana zargin kansa, ya rika tunanin lallai akwai abubuwan da yake yi wa Allah, kuma ya kamata ya gyara tsakaninsa da Allah.

Wannan zargin kan nasa da zai zo yana yi, zai haifar masa da karaya a zuciya, gaba daya zai saduda ya koma ga Allah (SWT), ya yarda shi bawa ne mai laifi, ya yi i’itirafi da zunubansa a gaban Allah.

To wannan ya fi ayyukan ibada da yawa da zai yi a wurin Allah. Wannan zargin kan nasa a wurin Allah Ya fi soyuwa sama da wasu ayyukan da’a da zai yi.

Sai kuma ka ga cewa taimakon Allah ya zo masa a lokacin.

Shi ya sa wannan yanayi da ake ta fama, masifun da muke ta gani da tsananin rayuwa da kullum yake ta kara rincabewa, ga kashe-kashe, ga sace-sacen mutane, ga fitinu nan ko’ina mutane sun shiga wani hali na kaka-ni-ka-yi.

Kullum abubuwa kara tsawalla suke yi, to wannan kada ya sa mu fitar da rai daga samun sauki daga Allah (SWT). Mu kara komawa ga Allah (SWT) da gaske.

Da za mu koma ga Allah (SWT) da gaske mu ji cewa babu wanda zai iya yi mana, mu ji ba mu da wurin gudu ba mu da matsera ko mafakasai wurinSa, to za mu ga canji da izinin Allah.

Allah (SWT), Ya fi son bayinSa su koma gare Shi, wannan shi ne sharadin samun canji din, “Lallai Allah ba Ya canja wa mutane abin da ke gare su, har sai sun canja abin da suke ciki.”

Sai mun tashi mun koma ga Allah, mun yaki laifuffuka, mun yi al’amru bil ma’arufi wan nahyi anil munkar.

Wannan fitsara da take ta faruwa a tsakanin ’ya’yan Musulmi, ayyukan fitsara da ayyukan masha’a, ayyukan rashin kunya.

Abin da ba za a taba tunanin dan Bahaushe ko ’yar Bahause za ta yi shi ba, yanzu yana neman ya zama ruwan dare, ya zama kayan ado, kayan kwalliya.

To babu shakka sai mun tashi mun yaki wadannan abubuwa, mun yi amru bil ma’arufi wan nahyi anil munkar.

Da yawa daga cikin masifun da suke samun al’ummar Musulmi suna samunsu ne saboda rashin umarni da kyakkyawan aiki da hana abin ki.

Allah “Ya tsine wa Bani Isra’ila a kan harshen Annabi Dauda da Isa dan Maryam, saboda ta’addancinsu da sabon Allah da suke yi.

“Sun zama ba sa hana junansu wani mummunan aiki da suke aikatawa.”

Saboda haka abubuwan da muke gani a hotuna na rashin kunya na fitsara da ’yan mata suke sawa a shafukan sadarwa na zamani, babu shakka sai an fito an yaki wadannan.

Da yawa daga cikin masifu, Allah Yana kare mana su saboda al’amru bil ma’arufi wan nahyi anil munkar.

Kuma ina fada da yawa daga cikin abubuwan da muke ganin saukinsu a yayin da muke jin wasu wurare kamar su kama da wuta, a nan Kano,

Allah Ya kare mu, Ya tsare mu har yanzu akwai sauki in aka kwatanta shi da wasu wuraren, saboda tsayawa da alamru bil ma’arufi wan nahyi anil munkar da ake yi.

Wannan tsayawa da amru bil ma’arufi wan nahyi anil munkar, wallahi a dalilin Hisba ba karamar kariya Allah Yake yi mana ba.

Yadda (’yan Hisba) suke tsaye ba dare ba rana wajen hana wasu abubuwa, ba za su iya kawar da komai ba, ba su da iko a kan kowa, amma dan abin da za su iya suna yi.

Kada a raina wannan, wani yana iya cewa ai ga su wane su wance ’ya’yan wane sun yi kaza yaya ba ku kamo su ba?

’Yan Hisban nan sun san iya karfin da suke da shi, abin da suke iyawar shi Allah Yake kallafa musu, Allah ba Ya kallafa wa rai sai abin da za ta iya.

Ko ba za su iya hana ’ya’yan manya da ’ya’yan sarakuna ba, in za su iya hana na ’ya’yan talakawan, to, mu gode wa Allah a kan wannan.

In sun kasa yi wa masu mulki magana, in suka matsa sai a zo gaba daya a rusa su.

Mu gode wa Allah da Ya samar mana da irin wannan, domin ta haka zai kade mana masifu da dama.

Don haka mu koma ga Allah (SWT), mu gaskata tsakaninmu da shi, sai ka ga Allah (SWT) Ya kawo mana canji ta inda ba ma zato.

Allah Ya gyara mana kasarmu da sauran kasashen Musulmi.

Wadannan fitinu da tashe-tashen hankula, Allah (SWT) Ya kawo mana agajinSa ta inda ba ma zato. Ubangiji Ya canja mana halayenmu da dabi’unmu zuwa mafiya kyau.

Allah Ya sanya tausayi da adalci a cikin zukatan shugabanninmu, mu kuma Allah Ya sa mana hakuri da juriya da biyayya a cikin abin da bai saba masa ba.