✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai karrama Sheikh Rijiyar Lemo da lambar girmamawa ta OON

A ranar Talata Shugaban Kasa zai karrama fitaccen malamin da lambar girmamawa ta OON.

Gwamantin Tarayya ta ba fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Umar Sani Rjiyar Lemo lambar girmamawa ta OON 

Sanarwar bayar da lambar girmamawar na kunshe ne a cikin wata takarda da aka aike wa malamin, wacce Ministan Ayyukan na Musamman ya sa wa hannu a ranar 10 ga watan Oktoba.

Aminiya ta yi arba da takaradar sannan Malam Bashir Baban Gwale, wani na hannun daman Sheikh Umar Sani Rijiyar Lemo, ya tabbatar wa da wakilinmu sahihancin takardar sanarwar.

A ranar Talata 11 ga watan Okotoba ne ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai ba malamin lambar girmamawar a wani taro da za a yi a Fadar Shugaban Kasa a Abuja

Dokta Umar Rijiyar Lemo, malami ne a Tsangayar Koyar da Addinin Musulunci ta Jami’ar Bayero ta Kano, sannan yana gabatar da karatuttuka da wa’azi a masallatai da kuma gidajen rediyo da talabijin.