✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Sudais ya kaddamar da sabbin tsare-tsaren aikin Hajjin 2022

Al-Sudais ne ya ba da umarnin a lokacin zaman da ya yi da masu ruwa da tsaki kan ayyukan Hajji a Masallatan Harami

Hukumar Gudanarwar Masallatan Harami na Kasar Saudiyya ta ba umarnin fara aiwatar da duk shirye-shirye da tsare-tsaren tarbar alhazai da za su yi aikin Hajji a bana.

Shugaban Hukumar, Sheikh Abdulrahman Al-Sudais ne ya ba da umarnin a lokacin zaman da ya yi da masu ruwa da tsaki kan ayyukan Hajji a Masallacin Harami da Masallacin Manzon Allah (SAW).

Ya bada umarnin ne a ranar Talata bayan Majalisar Gudanar da Aikin Hajjin ta gabatar masa da jadawalin tsare-tsaren ayyukan kula da alhazai a lokacin aikin Hajjin na bana.

An tanadar da tsare-tsaren ne domin tabbatar da ganin alhazai sun samu cikakkiyar kulawa da kuma sauki wajen gudanar da ayyukan ibadar aikin Hajji.

Sheikh Sudais ya jaddada wa mahalarta taron muhimmancin su kara dagewa wajen ba wa alhazai  cikakkiyar kulawa tare da tabbatar da ganin duk hukumomi da cibiyoyin da nauyin hakan ya rataya a wuyansu suna yi wa alhazai ayyuka masu matukar inganci.

Maharta taron sun hada da Limamin Masallacin Harami, Sheikh Yasir Al-Dosary da Limamin Masallacin Madina, kuma Wakilin Shugaban Majalisar Limamai da Ladanan Masallacin Madina, Dokta Ahmad Ali Al-Huzaifi.

Sauran sun hada da Mashawardin Shugaban Majalisar Gudanarwar Majasallatan Harami, Dokta Sa’ad bin Muhammad Al-Humaidi da kuma shugabannin Majalisar Gudanar Masallacin Harami da na Masallacin Madina da Hukumominsu da kuma shugabannin sashen mata.