Shekara 12 da kisan gilla ga Sheikh Ja’afar | Aminiya

Shekara 12 da kisan gilla ga Sheikh Ja’afar

A gobe Asabar 13 ga Afrilu ne ake cika shekara 12 da kisan gilla ga fitaccen malamin Musuluncin nan Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, wanda ’yan bidiga suka harbe shi lokacin da yake jagorantar Sallar Asuba a masallacinsa a Kano ranar 13 ga Afrilun shekarar 2007.

Babban abin takaicin shi ne har zuwa yau babu wani kwakkwaran bayani daga mahukunta game da kashe wannan bawan Allah.

Yayin da muke fatar shahada ga Sheikh Ja’afar da addu’ar Allah Ya jikansa, Ya sa Aljanna ce makomarsa. Har yanzu muna yi wa hukumomin tsaro da shugabanni wadannan tambayoyi: “Yaushe za a gano makasan Sheikh Ja’afar Adam? Ko kuwa an sanya batun kisan gillar da aka yi masa a mala ce, sai mun je Lahira mu ga wadanda suka yi wannan aika-aika?”