✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 6: Buhari ya amsa gazawarsa —PDP

PDP ta bukaci Buhari ya ba da amsa kan dalilan gazawar gwamnatinsa.

A ranar Asabar 29 ga Mayu, 2021 Shugaba Buhari ke cika shekara biyu a wa’adin mulkinsa na biyu —shekara shida bayan hawansa mulki a 2015.

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci Buhari da ya yi amfani da jawabinsa na ranar, ya amsa wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa ta gaza, sabanin jawabansa na baya da ta ce suke ikirarin samun nasarori na bogi.

Sakataren yada labaran PDP, Kola Ologbondiyan, ya kuma soki jam’iyyar APC mai mulki bisa zargin neman yi wa ’yan Najeriya ikirarin samun nasarori na bogi, alhali babu wata nasara ko aiki na a-zo-a-gani da gwamnatin jam’iyyar ta yi ko ta kammala a tsawon shekara shidan da take mulki.

“Idan da gaske ne Fadar Shugaban Kasa da APC na da wata nasara da za su nuna, to mene ne na shirya gangamin wayar da kai ne don neman fahimtar ’yan Najeriya kan gazawarta?

“Abin da ya kamata shi ne ayyukansu su yi magana da kansu kamar na gwamnatin PDP wanda har yanzu ake gani a kowane bangare na rayuwa a kasar nan.

“Idan suna abin da za su nuna, shin Shugaba Buhari zai rika rokon cewa ya kamata tarihi ya yi masa adalci a kan gazawarsa? Shin zai je Paris a kasar Faransa yana cewa gwamnatinsa ta yi rashin sa’a?

“Jam’iyyarmu da kakkausar murya, tana watsi da yunkurin APC na ikirarin cewa gwamnatinta ta gaza ne saboda kalubalen da ya dabaibaye al’ummarmu; A zahiri, kamata ya yi APC da gwamnatin Buhari su dauki alhakin gazawarsu.”

Muna jiran amsa

Ologbondiyan ya bukaci Buhari da APC su fadi dalilin da ya sa suka gaza wajen yin tir da ayyukan ta’addanci a kasar da kuma rashin daukar matakan da suka dace na fatattakar ’yan ta’adda ’yan bindiga da sauran bata-gari.

“Dole ne su ba da amsoshi kan yadda suka lalata tattalin arzikinmu da ya bunkasa suka kuma mayar da kasarmu hedikwatar talauci a duniya, inda yawan marasa aikin kai maki 33.3, ’yan Najeriya miliyan 60 kuma suka rasa hanyoyin samun abincinsu a cikin shekar shidan.

“Ya kamata Buhari da APC su sani cewa ’yan Najeriya na sane da cewa su ke da alhakin masifun da kasarmu take fama da su, kuma babu wani ikirarin samun nasarorin karya ko gangamin wayar da kai da zai sauya wannan,” inji PDP.

‘Buhari ya yi warar gani’

A ranar Juma’a Fadar Shugaban kasa, ta ce yabon da Buhari zai samu bayan kammala mulkinsa shekaru da ke tafe, sai ya fi na yanzu.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya fadi haka a cikin wata sanarwa mai taken ‘Gwamnatin Buhari a shekara 6: Kidaya albarkokin daya bayan daya’.

Sanarwar ta zayyana nasarorin da Gwamnatin Tarayya mai ci a karkashin Buhari a cikin shekara shida da suka gabata.

Adesina ya ce gwamnatin ta samu nasarori sosai a bangarori daban-daban na tattalin arziki, wadanda “duk mai kishi da son gaskiya  da adalci, ba wai bangarancin siyasa da cuwa-cuwa ba zai yarda da su.”