Shekara 61 da samun ’yanci: Najeriya daga ‘tatata ta koma rarrafe’ | Aminiya

Shekara 61 da samun ’yanci: Najeriya daga ‘tatata ta koma rarrafe’

Tutar Najeriya
Tutar Najeriya
    Salihu Makera da Adam Umar, Abuja

A ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoban 2021 ne Najeriya ta cika shekara 61 da samun ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Najeriya wadda daya ce daga cikin kasashe masu arzikin man fetur kuma kasar da Allah Ya ba albarkar kasar noma da ma’adanai, inda a bayan Yakin Basasa a shekarun 1970 ta fara daura dan ban ci gaba.

Akwai bayanan da suke cewa tsohon Shugaban Kasa na Soji Janar Yakubu Gowon ya taba cewa ba kudi ne matsalar kasar nan ba, sai dai yadda za ta kashe kudin ne matsala.

Najeriya ta fara kakkafa kamfanoni da masana’antu tare da bunkasa harkar sufurin jiragen sama da na kasa da kamfanonin harhada motoci akalla guda shida da kamfanonin takin zamani da na sukari da bankuna da kuma dimbin jari a bankunan kasuwanci baya ga sauran manya da kananan masana’antu da ta kakkafa a sassan kasar nan.

Bayanai sun nuna cewa, a daidai lokacin kasar nan take da jiragen sama kusan 22 da suke sufuri zuwa sassan duniya, kasar Saudiyya tana da guda biyu ne kacal.

Sannan Najeriya ta riga Saudiyyar samun man fetur ta riga ta samun wutar lantarki, amma bayanai sun nuna cewa a yanzu haka, wutar lantarki da Saudiyya ta ware wa Dakin Ka’aba kawai ta fi rabin wutar lantarkin da Najeriya take da shi don amfani da ita a kasarta baki daya.

Zuwa 1990 Najeriya tana da kamfanonin harhada motoci guda shida a sassan kasar nan da suka hada da Fijo a Kaduna da Baswaja a Legas da Lyland a Ibadan da Fait a Kano da Styer a Bauchi da kuma Anamco a Anambra, wadanda suke samar da dukkan nau’o’in motocin da kasar nan take bukata kama daga na hawa zuwa na daukar kaya da na huda ko noma da na dakon mai ko daukar ruwa.

Sannan ga jiragen kasa da suke dakon dukkan kayayyakin da ake bukata tun daga Legas zuwa Kano da kuma Fatakwal zuwa Maiduguri.

Sai dai kuma wadannan yanzu duk sun mutu ko sun suma ta yadda ake fama wajen farfado da wasu daga ciki, yayin da ake zargin shugabanni da cefanar da wasu muhimman kamfanoni da masana’antu ga kawunansu da yaransu.

A yanzu dai in aka cire tashoshi jiragen ruwa da filayen jiragen da Bankin Manoma da matatun man fetur marasa karsashi da ’yan wasu kadarori kusan kasar nan ba ta da wani abin nunawa a duniya.

Wannan ya sa mutane da dama suke ganin Najeriya ta koma rarrafe ne daga tatata, watomaimakon ta ci gaba sai komawa da baya take yi.

Tunda sojoji suka kashe shugabannin farko suka kashe ci gaban kasar nan – Isiyaku Ibrahim Alhaji

Isiyaku Ibrahim yana daya daga cikin wadanda suka shaidi samun ’yancin kan Najeriya da fara aiki a farkon kafuwarta.

Ya shaida wa Aminiya cewa kifar da gwamnatin mulkin dimokuradiyya ta Jamhuriyyar ta Farko da soja suka yi shi ne silar koma-baya da kasar nan take fuskanta har zuwa yanzu.

Kodayake Najeriya ta samu shekara 22 da dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999, Alhaji Ibrahim ya ce tsofaffin sojoji ne da suka saje a cikin farin hula ke ci gaba da rike mulkin kasar nan.

Ya ce sojoji wadanda babban aikinsu shi ne kare iyakokin kasa daga duk wata barazana daga waje, sai ga shi a yanzu ana zaune da su a cikin al’umma ana gudanar da harkokin cikin gida tare da su.

“Misali guda da zan ba ka shi ne na kutsensu a mulkin kasa na kusa-kusa wato Jamhuriyya ta Biyu.

Zuwan gwamnatin ta kama ministoci da gwamnoni ta tsare kan zargin cin hanci da rashawa, aka kwace wa mutane dukiya sannan aka sauya kudin kasar kan zargin shugabannin gwamnatin farar hula sun yi sata.

Alhaji Isyaku Ibrahim ya kuma soki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da talauta kasa.

“A yanzu haka akwai matasa sama da miliyan 40 da ba su da aikin yi kamar yadda bincike ya nuna,” inji shi.

Alhaji Isiyaku Ibrahim ya ce aikin layin dogo da gwamnatin dimokuradiyya ta yanzu take tinkahon yi an jima da tsara wanda ya dara shi tun a lokacin Jamhuriyya ta Biyu, amma sai aka kifar da ita.

Ya ce “Umaru Dikko shi ne Ministan Sufuri a lokacin, inda ya kawo tsarin aikin layin dogo da ake kira Standard Gauge da ya hada da wanda zai kai har Jibiya da Sakkwato.

Da wanda zai kai Mubi, sannan duk a hade su da layukan dogo da suka nufi bakin ruwa wato Legas da Fatakwal.

Babban dalili kuwa shi ne saboda a Arewa ne ake da manoma, hakan zai ba da damar daukar amfanin gona ko dabbobi a yi jigilarsu zuwa Kudu, sannan kayan masana’antu da sauransu da za a dauko daga bakin ruwa a kawo su Arewa cikin sauki.

Haka muka tsara bangaren tattalin arziki, ni din nan na je na samu Shugaban Kasa Alhaji Shehu Shagari na yi masa bayani kan gazawar Arewa a harkar tattalin arziki tare da ba da shawarar a yi wa al’ummarmu damar shiga bangaren banki.”

Ya kara da cewa, “Daga nan na hadu da karamin Ministan Kudi Alhaji Ali Baba na yi masa bayani sannan ya tsara takarda aka gabatar wa Shugaba Shagari, aka tsara abubuwa tare da aiwatar da su, hakan ya samar da ci gaba sosai kafin a fara samun matsala.

Ko wannan tsari na karba-karba da na ji ake ta ce-ce-ku-ce a kai a yanzu ai a lokacin mulkin Shagari ne muka samu daidaito a kai cewa ’yan Arewa za su shekara takawas a kan mulki sannan ’yan Kudu su ma su rike na shekara takwas.”

“Hakan zai ba da damar dimokuradiyya na tsarin Shugaban Kasa mai cikakken iko ta samu zama da gindinta, amma tun ba mu kai ga gama wa’adin Arewa ba, sai ga shi a tsakaninmu ’yan Arewa ne muke cin dunduniyar juna, dan Arewa ya kwace mulki,” inji dan siyasar.

Najeriya ta fara ci gaba ta kuma koma baya – Barista Mainasara Kogo

Barista Mainasara Kogo ya ce Najeriya ta samu ci gaba a fuskar damawa da ita a siyasar duniya tare da rike manyan mukamai da suka hada da Mataimakiyar Shugaban Majalisan Dinkin Duniya wato Hajiya Amina Muhammad da Shugaban Zauren Majalisar Dinkin Duniya da ya sauka wato Farfesa Tijjani Muhammad Bande da Babban Sakataren Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man fetur (OPEC), Dokta Muhammad Sanusi Barkindo da Shugaban Bankin Raya Afirka, Dokta Akenwumi da Shugabar Kungiyar Kasuwanci ta Duniya Dokta Ngozi Nkonja-Iweala.

Ya ce Najeriya ta kuma taka rawa a fuskar samar da tsaro a kasashen duniya.

Ya ce an kuma samu nasarar hadin kan kasar a bayan sama da shekara uku ana tafka Yakin Basasa.

Sai dai ya ce kasar ta samu koma-baya ta fukoki da dama da suka hada da watsi da kyawawan al’adun al’ummarta a wajen sutura da hulda da kuma sarauta, sannan hatta a addinin ma gwamnatin kasa ta ce babu ruwanta da shi.

Haka nan ya ce darajar kudin kasar ta fadi warwas idan aka kwatanta da baya a lokacin da ake sauya Dala a kan Kwabo 80, bayan wasu manufofi da gwamnatin soja ta bullo da su a 1985 inda ta ce sai kudin kasar ya sama wa kansa daraja da kansa.

“A lokacin ne aka fitar da tsarin SAP da sauran manufofi marasa kan-gado, sannan aka rika ciwo bashi marar fasali,” inji shi.

Masanin dokoki da siyasar duniyar, ya ce kasar nan ta samu koma-baya a fuskar masana’antu sabanin shekarun baya da ake tinkaho da unguwannin masana’antu irin su Sharada da Bompai da Chalawa a Kano da Kudandan da Kakuri a Kaduna, har ma da Apapa da ke Legas.

Haka ya ce masana’antu irin su kamfanonin harhada motoci na Fijo da ke Kaduna da Styer a Bauchi da wasu a Enugu da Ibadan yanzu sun durkushe.

Ya ce durkushewar masana’antu da noma ya sa matasa sun rasa aikin yi, sannan harkar ta’addanci ta samu gindin zama inda hatta wadanda suke kokarin noman ma ba su tsira ba saboda za a bi su har cikin gona a kama su a yi garkuwa da su.

Ya ce kuma hadin kan kasar nan yana tangaltangal a yanzu.

Barista Mainasara ya ce abin mamaki ne yadda shugabannin kudu suke yi wa Arewa cin fuska a yanzu duk da rawar da yankin ya taka wajen sama wa kasar nan ’yanci da kuma tallafa wa tattalin arzikinta a farkon kafuwar kasar.

“A lokacin ba da ’yancin kai yankin Arewa ne kadai ya gabatar da jadawalin tsare-tsare da marigayi Sa Ahmadu Bello Sardauna ya gabatar wa Sarauniya da yake nuna matakin da ake son ta kai a cikin shekara 10 da 20 da 50 zuwa 100, idan ta samu ’yanci.

Sarauniya ta nuna matukar farin ciki tare da yaba wa Arewa a kan haka, sannan ta yi hasashen cewa zuwa shekara 20 da samun ’yanci, yankin na iya zama ‘Super Power a tsakanin kasashen duniya.

Yanki ne da yake da ma’adinai 148 da suka kunshi kusan kowane nau’in ma’adini a duniya.

“Sai dai kash, a maimakon a ci moriyarsu ta hanyar aiwatar da tsare-tsare da Sardauna ya samar bayan kifar da mulkinsa, sai duk abubuwan suka sauya ya kai hatta itacen sakace hakori a yau sai an shigo mana da shi,” inji shi.

Ya ce kasar nan ta samu komabayan saboda samun shugabanni marasa sanin makamar aiki har ta kai wani tsohon shugabanta ya taba cewa matsalar Najeriya ba ta kudi ba ce, sai dai ta yadda za a kashe kudin.

Ya ce maimakon a yi amfani da kudin a lokacin wajen kafa masana’antu da tono ma’adinan ana sarrafa su, sai aka kafa wani kwamitin Udoji aka rarraba kudi da sunan sun yi wa kasa yawa.

Sai dai ya ce kash, shugabanni da suka biyo baya ba ma raba kudin suke yi ba, illa sace dukiyar ko su zura ido mukarrabansu suna sacewa ba tare da daukar mataki ba.

Ya ce a yanzu an daina la’akari da cancanta wajen ba da shugabanci da ya hada da la’akari da sanin makamarsa da ilimi da dattaku da rikon amana.

“A lokjacin muna da masu halin dattaku, amma a yanzu tsofaffi kawai ake da su saboda yawan shekaru ake amfani da shi ba kima ba,” inji shi.

Ya ce a lokacin da Sa Abubakar Tafawa Balewa ya je taron shugabannin duniya a Majalisar Dinkin Duniya a 1962 ruwan sama ake yi amma al’ummar kasar suka tsaya a filin jirgin saman kasar don tarbarsa saboda dattakunsa da bajintarsa.

Ya ce bayan jawabinsa wanda ya burge duniya an yi wa Najeriya kyaututtukan abubuwa bakwai da suka hada da rukunin tashoshin wutar lantarki a Jabba da Kainji da na jiragen mayakan ruwa, da na kamafanin sufurin jiragen sama da aka fara kamfanin Nigerian Airways da su.

Sauran kyaututtukan inji shi, sun hada da kamfanin hada kayan yaki na sojoji da ke Kaduna da Makarantar Horar da Kananan Hafsosin Soji (NDA) da ke kaduna.

Ya ce shugabanni irin su Sardauna da Tafawa Balewa da Zik da Awolowo masu kishin kasarsu ne da l’ummarta inda suke gabatar da dayansu a maimakon kansu idan maganar ba da matsayi ta bijiro.

“Wannan ya saba da halin wadanda suka biyo su wadanda suka koma tsarin agwgwa, ’ya’ya na gaba, uwa na biye,” inji shi.

Gara jiya da yau – Matashin dan siyasa

Wani matashin dan siyasa mai suna Alhaji Khalid Isma’il da Aminiya ta zanta da shi a kan cika shekara 62 da Najeriya ke yi a yau, ya ce gara jiya da yau bisa la’akari da yadda ake ba da tarihin adalcin mazan jiya.

“Koma-bayan ba ta taba kazancewa ba irin na wannan lokaci da kowa yake ji a jikinsa.

Rayuwa ba ta taba yin tsada ba da zama cikin wahala irin ta yau.

Ya ce gwamnatin da ta samu nasara kan alkawuran da ta yi na samar da tsaro da yaki da cin hanci ta gaza,” inji shi.