✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 61 da samun ’yancin kai! (2)

Shin iyayen Najeriya ne suka tsine mata ta lalace haka?

A cikin wadannan shekaru da muke magana Najeriya ta shiga cikin taskun rayuwa ta fuskar gudanar da mulki.

Shugabanninta, wato wadansu daga cikin ’ya’yanta, sun kasance Fir’aunonin zamani, sun haye kanta sai sukuwa suke, kowa sai kuka da tsuwwa yake saboda mugun mulkin ’ya’yanta.

Ita kuka, sauran al’ummarta ihu. Wadansu daga cikin ’ya’yan nata (masu mulkin soja da farar hula) sun bi sai sukuwa suke a cikin kasar, sun danne, sun murkushe, sun daure, sun shakure, sun harbe, sun kashe, ba kuma abin da wani zai iya yi.

Mene ne wannan in ba alamun an tsine wa kasar ba, ’ya’yanta da jikoki sun tarwatse, sun lalace, ba su iya agazawa ko taimaka wa mahaifiyarsu?

Ba wannan ba kadai ka dubi irin tarin dukiyar da a da Najeriya ke da ita, amma da yake bakin iyaye ya bi ta, me ya faru, ta tsiyace, ta talauce, ta sangarce.

Dubi irin hanyoyin samun da ke tattare da ita a can da, noma, kiwo da sana’o’in hannu bilahaddin, amma yanzu fa, saboda tsinuwa ta yi watsi da komai da komai ta kama saba-likita.

Sabuwar sana’ar da ta kama ta sayar da mai, nan ma tsinuwar ba ta bar ta, domin komai ta taba dangane da harkar sayar da man, sai ka ga ya sukurkuce, ta kama hanyar shiga tasku, ko ma ta yi gida ta zaune a ciki.

Yanzu man fetur da Najeriya ke sayarwa ya zame mata ciwon sankara, ga arziki, amma arzikin banza, saboda lalacewa da shirmancewa idan ta sana’arta man fetur din ma, ta samu dukiya mai yawa, ba wani amfani da dukiyar ko arzikin man fetur ke yi mata ko ’ya’yanta, shi mene ne wannan in ba alamun tsinewa ba?

Wani abin kara la’akari da rayuwar Najeriya dangane da tsinuwar shi ne irin yadda komai na gidan nata ya lalace.

Abincin da za ta ciyar da ’ya’yanta ya gagare ta. Ilimin da za ta ba ’ya’yan nata, ya faskara. Hanyoyin da ake bi a cikinta sun kasance gwadabun wahala, ka bi da mota, ta lalace, ka hau su da babur, ka sha wahala, ka bi su da keke, garegaren ya malkwade, ka taka a kasa ka yi ta fama da tuntube da gwalando.

Hanyoyin dogo ko jirgin kasa duk sun lalace, jiragen sama tuni sun yi hijira daga kasar, duk wata hanyar zirga-zirga a cikin Najeriya ta gani da fada ba daya da za a ce na aiki; ina marabin wannan da wanda aka tsinewa a cikin rayuwa?

Haka kuma saboda tsinuwa na bin ’ya’ya, wata sa’a ma har da zuwa ga ’ya’ya da jikoki da alama tsine wa Najeriya da aka yi ya shafi har ’ya’yanta.

Kashi saba’in cikin dari na ’ya’yan nata ba su iya ciyar da kansu, talauci ya yi musu katutu.

Rabin ’ya’yan nata kuma ba su da aikin yi, masu dukiya daga cikin ’ya’yan an hana musu godiya, marasa dukiyar kuma an hana musu dangana.

Ba ka jin komai daga ’ya’yan Najeriya sai Allah wadai da kukan dimuwa da damuwa. Duk wannan mene ne in ba siffofin tsinuwa ba?

Idan mutum ya ce zai tsaya ya lissafe alamun da suke nuni da cewa an tsine wa kasarmu Najeriya, to sai ya cika littattafai, domin kuwa ga su nan ba sa kirguwa.

To amma ko da muke rayuwa irin ta yara a wancan lokaci, abin da mutunen da aka tsine wa ke yi shi ne su gane wanda ya tsine musu domin su nemi gafara, don a sake sabuwar rayuwa.

Tambayar da nake yi wa kaina dangane da Najeriya ita ce, ita wa ya tsine mata? Wa ta yi wa laifi har baki ya shafe ta? Wa za ta nemi afuwa wurinsa domin a yafe mata, a yaye rigar tsinuwar, domin ta koma yin rayuwar da ta dace da ita?

Shin iyayen Najeriya ne suka tsine mata ta lalace haka, har abin ya shafe mu, ’ya’ya da jikoki?

Ko kuwa wani tsoho ne daga cikin al’ummar Najeriya ta yi wa rashin kunya, har ya buda baki ya ce, je ki, kya gani?

Ko kuwa dai ita Najeriyar ce ta tsine wa kanta da kanta, domin ta sa ’ya’yanta cikin tasku da gagari, ganin cewa ’ya’yan nata ba na kwarai ba ne, wato su kasance cikin tasku da tashin hankali, saboda rashin tarbiyya da ladabi da biyayya?

Ko kuwa dai ita Najeriyar ce da kanta ta tsine wa ’ya’yan nata domin su lalace?

Najeriya a nawa tunanin ba ta tsine wa kanta ba. Wani tsoho bai tsine mata ba. Ba wani da ya yi mata baki. Ba kuma wani da za ta je wurinsa domin neman afuwa, domin ba ta yi wa ’ya’yanta laifi ba.

Najeriya tana nan a matsayinta na Najeriya, ba ta canja ba, uwa ce mai ba da mama.

Uwa ce tagari, wadda kullum take zubar da hawaye domin ta faranta wa ’ya’yanta. Uwa ce da take cikin damuwa.

Idan har kuma ta tsine wa wadansu daga cikin ’ya’yan nata to da alama, wake daya ne yake bata gari.

Saboda haka idan har kuncin rayuwa da dimuwa da garari ya damu ’ya’yanta na yanzu to da alama akwai wasu mugayen halayen da ’yan yanzu suka ko suke tafkawa da ya sa Najeriya ta dage nononta ga wadannan ’ya’ya nata. Me ya sa muka ce haka?

Za mu ci gaba