✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 61: Kasashen duniya sun taya Najeriya murna

Shugabannin kasashen sun yi Najeriya fatan alheri da kuma samun ci gaba.

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da taya Najeriya murnar cika shekara 61 da samun ‘yancin kai.

Kasashen sun aike da sakonnin taya murna cikin sanarwa daban-daban da shugabanninsu suka aike wa da shugaba Buhari a ranar Alhamis.

Daga cikin kasashen da suka taya Najeriya murna akwai Faransa, Jamus, Indiya da kuma Saudiyya.

Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce yana bukatar Najeriya da Faransa su inganta alakar da ke tsakaninsu da kowane bangare.

Ita ma shugabar kasar Jamus, Angela Merkel ta taya shugaba Buhari murna tare da fatan magance matsalolin da suka sha gaban Najeriya.

Shugaban Kasar Indiya, Ram Nath Kovinth, shi ma ya yi wa Najeriya fatan alheri da wanzuwar zaman lafiya.

“Alakar Najeriya da Indiya na da karfin gaske kuma na ci gaba da kara karfi sannan tana samun karfi ta bangarori daban-daban,” cewae Femi Adesina

Shi ma sarkin kasar Saudiyya, sarki Salman Bin Abdulaziz Al Saud, ya taya shugaba Buhari murnar cika shekara 61 da samun ‘yancin kai na Najeriya.

Sannan ya yi fatan samun ci gaba ta bangaren harkar lafiya, farin ciki da zaman lafiya a tsakanin al’umma kasar.

A yau Juma’a ce dai wadda ta yi daidai da 1 ga watan Oktoban 2021, Najeriya ta cika shekara 61 da samun ‘yancin kai daga Turawan Mulkin Mallaka na Ingila.