✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 61: Saudiyya da Indiya sun taya Najeriya murna

Kasashen duniya na taya Najeriya murnar cika shekara 16 da samun ’yanci.

Kasashen Saudiyya da Indiya da Jamus da Faransa sun taya Najeriya murna game da zagayowar ranar samun ’yancinta karo na 61.

Shugabannin kasashen hudu sun taya Najeriya murna da kuma fatan alheri ne a sakonninsu daban-daban da suka aike wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A sakonsa na taya murna, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na Saudiyya, ya yi wa Buhari addu’ar samun lafiya da kuma farin ciki da ci gaban rayuwa da daukaka ga ’yan Najeriya.

Shi ma Shugaba Ram Nath Kovind na Indiya, ya yi wa Buhari da Najeriya addu’ar samun karin cigaba.

“Alakar Najeriya da Indiya ta fadada ta kuma kara karfi ta huldodi daban-daban”, inji mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina.

Shugabar Jamus mai barin gado, Angela Merkel, ta kira Shugaban Buhari ta waya, inda ta yi masa addu’ar samun nasara a kan kalubalen da ke gabansa na jagorantar Najeriya mai al’umma sama da mutum miliyan 200.

A nashi bangaren, Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a sakonsa na taya murna, ya bayyana shakuwarsa da Najeriya, inda ya yi kira da a kara karfafa dangantaka tskanin Najeriya da Faransa ta kowane bangare.