✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara daya da rasuwar Abba Kyari: Me ya sauya a Najeriya?

Rasuwar Abba ta koyar da darasi ga 'yan Najeriya, musamman game da cutar COVID-19

Shekara guda kenan cif tun bayan rasuwar Malam Abba Kyari, Shugaban Ma’aikata na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Malam Abba Kyari, wanda ya rasu ranar 17 ga Afrilun 2020 bayan kamuwa da COVID-19, shi ne mutum na farko mai babban mukami a Najeriya da wannan cuta ta yi ajalinsa.

Alamun cutar sun bayyana a jikinsa ne bayan ziyarar da ya jagoranci wakilan Gwamnatin Tarayya suka kai kasar Jamus, inda suka tattaunawa da wakilan kamfanin Siemens a kan yadda za a habaka wutar lantarki a Najeriya.

Bayan gwajin da aka masa ya nuna yana dauke da cutar ne dai gwamnatin ta kulle dukkan iyakokin kasar a wani mataki na hana yaduwar kwayar cutar.

Kafin rasuwarsa, Abba Kyari ya sha suka da zargi iri-iri, inda har wasu ke cewa ya yi babakere a gwamnatin Buhari, shi ke sawa, shi ke hanawa.

‘Mutum ne jajirtacce’

Sai dai wasu na gani Kyari mutum ne da ya shahara wajen jajircewa a kan aikinsa, sannan mafi karfin fada-aji a cikin mutanen da suka rika mukami irin nasa a baya.

Mai yiwuwa, da rasuwarsa, ’yan Najeriya da dama sun yi tsammanin samun sauyi a yadda ake gudanar da al’amuran kasar.

Hasali ma, an yi ta hasashe iri-iri a kan yadda kamun ludayin magajinsa, Farfesa Ibrahim Gambari, zai kasance.

To ko mene ne ya sauya a tsarin tafiyar da gwamnati tun bayan rasuwar Abba Kyari?

A cewar Adnan Mukhtar Tudun Wada, wani dan siyasa kuma mai sharhi a kan al’amuran siyasa, Abba Kyari mutum ne da ya jajirce wajen yin ayyukan gwamnatin tarayya yadda ya kamata.

“Gambari na kokari irin nasa amma ba za ka hada shi da Kyari ba, saboda a zamaninsa, duk da ana shan wahala, mutane na ganin Kyari a matsayin wanda ya yi kokarin kawo sauyi a gwamnatance.

“Amma a yanzu Gambari kokarinsa bai kai na Kyari ba duk da cewar bai jima da karbar mukamin ba, amma ba za a hada Abba Kyari da Gambari ba,” inji shi.

Juya akalar gwamnati

Daya daga cikin abubuwan da aka zargi marigayi Abba Kyari shi ne yin babakere da hana komai gudana a gwamnati.

Wannan zargi ya karu lokacin da, bayan ya sha rantsuwa a karo na biyu, Shugaba Buhari ya ce duk wani minista ko babban jami’in gwamnati da ke son ganin shi ya biyo ta hannun marigayin.

Amma yayin da wasu suka yi ta Allah-wadai da wannan umarni, wasu cewa suka yi ai da ma alhakinsa ne ya kare shugaban kasar, don haka komai ta hannunsa ya kamata ya biyo.

Sai dai kuma ko bayan rasuwar Malam Abba Kyari, babu alamun an samu sauyi a yadda ake tafiyar da lamura a Fadar Shugaban Kasa.

Haka kuma, ko da yake ba kasafai akan ji an ambaci wata kungiyar mutane da ake zargin Kyari na jagoranta a Fadar ta Shugaban Kasa – wato cabal a Turance – ba, har yanzu abubuwa na ci gaba da tafiya yadda aka saba, in ban da nan da can.

Ko bayan dawowarsa daga ganin likita a Landan, sakon Shugaba Buhari ga ’yan Najeriya shi ne za a ci gaba da tafiyar lamura yadda aka saba.

Tasirin COVID-19

Wani babban darasi da Najeriya ta koya, ko ya kamata ta koya, daga mutuwar Abba Kyari, ita ce COVID-19 fa ba karya ba ce.

Bayan rasuwarsa dai manyan mutane – jami’an gwamnati da sauran masu fada-a-ji a tsakanin al’umma da dama – sun riga mu gidan gaskiya bayan an tabbatar da sun kamu da wannan cuta.

Fitattun mutanen da wannan cuta ta yi ajalinsu sun hada da Abiola Ajimobi, tsohon Gwamnan Jihar Oyo, da Wahab Adegbenro, Kwamishinan Lafiya na Jihar Ondo, da Bayo Osinowo, mai wakiltar Gabashin Jihar Legas a Majalisar Dattawa.

Akwai masharhanta da dama da ke ganin cewa da an rufe iyakokin Najeriya da wurwuri, da Coronavirus ba ta yi barnar da da ta yi ba a kasar.

Watakila, a ganin wadannan masharhanta, da ba a shiga halin matsin da aka shiga ba sakamakon yaduwar cutar tun a ranar 23 ga watan Maris, 2020, lokacin da annobar ta bulla a Najeriya, har ta tilasta gwamnatin tarayya sanya dokar kulle.

Bayan rasuwar Abba Kyari

Bayan rasuwar Abba Kyari da ayyana dokar kulle a sassan Najeriya daban-daban, abubuwa da yawa da suka shafi harkokin yau da kullum sun samu tasgaro, musamman tattalin arziki.

Kasuwanci, harkar lafiya, da sauran al’amuran yau da kullum na jama’a duka sun fuskanci koma-baya a sanadin annobar ta COVID.

Mutane da dama sun rasa ayyukansu, musamman saboda yadda dokar kulle ta tilasta kamfanoni rage ma’aikata.

Rashin aikin yi ya karu da kashi 27 cikin 100, wato adadin marasa aikin yi ya kai miliyan 21.

Ko da yake ba zai yiwu a ce rasuwar Abba Kyari ba ce ta haddasa wasu daga cikin wadannan matsaloli, babban darasin da ya kamata ta koyar da ’yan Najeriya, musamman mahukunta, shine su daina jan kafa wajen daukar mataki don kare rayuwar al’umma.

Su kuma al’umma ya kamata su fahimci yanayin da aka shiga su dauki matakan da suka dace kamar yadda masana ke nunawa.

Dokta Bashir Jamilu, wani fitaccen likita a Babban Asibitin Daura dake Jihar Katsina, na cikin masanan da ke irin wannan jan kunne.

“COVID-19 ta kawo matsaloli da dama, amma dole ne mutane su gane cewar ta zama wani bangare na rayuwarmu, dole ne a ci gaba da amfani da matakan kariya da aka bullo da su.

“Bayan matakan kariya, yanzu an kawo riga-kafin cutar wadda ita ce hanyar da mutane za su kare kansu,” inji shi.

Cece-kuce na karshe?

An dai binne Malam Abba Kyari ne a ranar Juma’a 18 ga Afrilun 2020, a makabartar gundumar Gudu a Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Amma jana’izarsa ma sai da haifar da cece-kuce bayan da aka hana wasu jami’an Gwamnatin Tarayya shiga Fadar Shugaban Kasa saboda zargin wasu mutane da aka yi da halartar jana’izar marigayin ba tare da daukar matakan kariya ba.

Duk dai da mahukunta sun ce ba za a taru yayin jana’izar ba, mutane da dama ne suka sallaci gawarsa suka kuma yi mata rakiya zuwa makabarta.

Mai yuwuwa hakan ya faru ne saboda muhimmancin marigayin a gare su – ma’ana sabanin yadda wasu suke yi masa kallon karfen kafa, Malam Abba Kyari mutumin kirki ne, mai matukar kwazo, mai kishin kasa, kuma mai son jama’a.