Daily Trust Aminiya - Shekaru 50 da yakin Biyafara: IBB ya bukaci ‘Yan Najeriya da
Subscribe

Shekaru 50 da yakin Biyafara: IBB ya bukaci ‘Yan Najeriya da su hada kai

Tsohon Shugaban Najeriya a Mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), ya bukaci daga kowanne bangare na kasarnan da su zamo masu hadin kai, domin samun dorewar zaman lafiya da ci gaba.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da BBC akan cikar yakin basasa shekaru hamsin, IBB ya ce a maimakon ‘yan Najeriya su rika kirkiro kungiyoyi da zasu kawo cikas ga zaman lafiya, gara su maida hankali wajen ayyukan da zasu kawo wa kasar ci gaba da hadin kai.

A cewarsa, “Mutanen da suke cewa a yi yaki basu san menene yaki ba. Da yawa daga cikinsu basa raye a lokacinda aka yi yakin basasa. A don haka ya kamata mu godewa Allah da Ya bamu hadin kai bayan wannan yaki da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama.”

A karshe ya ce yanzu Najeriya tana samun ci gaba, kuma zaman lafiyane zaisa hakan ya dore.

More Stories