✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekau ya tsallake rijiya da baya

Shekau ya samu mummunan rauni bayan ya yi yunkurin kashe kansa.

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya samu munanan raunuka bayan da ya yi yunkurin kashe kansa a Dajin Sambisa.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ya ce, Shekau ya samu raunukan a kokarinsa na yin kunar bakin wake domin kada mayakan ISWAP su kama shi a wani karon batta da suka yi a ranar Laraba.

“A yunkurinsa na hana a kama shi, sai Shekau ya harbi kansa a kirgi, harsashin ya fasa kafadarsa inda ya samu mummunan rauni,” a cewar wata majiyar tsaro da kamfanin dillancin labaru na AFP ya zanta da ita.

Majiyar tsaron ta ce Shekau ya yi hakan ne bayan mayakan ISWAP sun yi masa kofar rago tare da wasu mayakansa, suka nemi ya mika wuya.

Majiyar ta ce wasu daga cikin mayakan da ke tare da shi sun samu tserewa zuwa inda ba a sani ba.

Shekau ya tayar da bom

Wata majiya kuma ta ce Shekau ya samu mummunan rauni ne bayan da ya tayar da bom a lokacin da aka ritsa shi a cikin gidansa.

Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Mohammed Yerima ya shaida wa AFP cewa, “Munga gudanar da bincike,” game da labarin.

Labarin tsallake rijiya da baya da ya yi na zuwa ne bayan da farko an bayyana cewa ya kashe kansa ta hanyar kunar bakin wake.

An dade ana samu labarin rahoton mutuwar Shekau, amma daga baya ya fito ya karyata.

Ana ganin mutuwar Shekau wanda ya yi kaurin suna, musamman bayan da kungiyarsa ta sace dalibai mata sama da 200 a Chibok, zai gurgunta Boko Haram.

Tuni dai sojoji suka kassara kungiyarsa ta hanyar hare-haren sama, baya ga ballewa da kuma tubar wasu daga jikin mayakansa, ga kuma wadanda ake ta hallakawa.

Akalla mutum 40,000 ne rikicin Boko Haram ya yi ajalinsu daga 2009 zuwa yanzu, a Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.

A karkashin mulkinsa a 2009 ne kungiyar ta kara karfi ya ta wasu zuwa yankunan jihohin Arewa-maso-Gabas da kasashen yankin Tabkin Chadi, kafin a 2015 sojoji su fatattake su a yawancin yankunan.

Boko Haram da ISWAP sun sha gwabza fada kain iko da yankin Dajin Sambisa, wanda daga baya ISWAP ta rika samun galaba, tare da kai miyagun hare-hare, har da tashin sansanonin soji suna satar makamai.