✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekau ya zabi a yi masa azaba a lahira —Shugaban ISWAP

Ainihin yadda aka aika Shekau lahira daga bakin shugaban kungiyar ISWAP.

Kungiyar masu ikirarin Jihadi a Yammacin Afrika ta ISWAP, ta zayyana yadda mayakanta suka samu nasarar kawar da shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, daga doron kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa, ISWAP mai adawa da Boko Haram wacce kuma Abu Musab Albarnawi ke jagoranta, ta ce Shekau ya yi gamo da karshensa a ranar 19 ga watan Mayun 2021.

A cikin wani sakon murya wanda kamfanonin dillancin kabarai suka nada, ISWAP ta ce Shekau ya mutu ne a lokacin da ya tayar da abin fashewa a jikinsa bayan karawa tsakanin kungiyoyin biyu.

A jawabinsa, Albarnawi wanda ya bayyana Shekau a matsayin jagora marar adalci mara ladabi da biyayya da kuma rashawa, ya ce hatta mayakan da yake jagoranta sun yi farin ciki da mutuwarsa.

Ya ce Shekau wanda ya ci gaba da jagorantar kungiyar Boko Haram bayan mutuwar wanda ya assasa ta tun fil azal, Muhammad Yusuf a shekarar 2009, sun cimmai ne a cikin wani yanayi na wulakanci.

Albarnawi, wanda mahaifinsa ne ya kafa Boko Haram, ya ce sun dirar wa Shekau ne bayan samun umarnin kama shi daga uwar kungiyarsu, wato ISIS, sakamakon yadda ya mayar da ran bil Adama ba a bakin komai ba, inda yake kashe ‘masu imani’.

Ya ce Shekau ya gwammace ya dandani azabar lahira madadin ta duniya, shi ya sa ya kashe kansa, ya ki mika wuya.