✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shiga kungiyar asiri: Kotu ta aike da daliban Jami’ar Maiduguri 18 gidan yari

Alkalin ya yanke hukuncin bayan samun su da laifi dumu-dumu.

Wata Babbar Kotu a Jihar Borno ta yanke wa wasu dalibai 18 hukuncin daurin shekara shida a gidan yari saboda samun su da laifin shiga kungiyar asiri.

Daliban da suka fito daga Jami’ar Maiduguri da kuma Kwalejin Ramat, sun gurfana gaban kotun a ranar Talata.

’Yan sanda sun kama su a ranar 21 ga watan Satumban 2019 a wani otal da ke Maiduguri, bisa zargin shiga kungiyar asiri ta ‘Neo Black Movement’ wadda ake wa lakabi da ‘Black Axe’.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Umar Fadawu, ya ce daliban sun amsa cewar sun aikata laifin da ake tuhumarsu da shi na shiga kungiyar asirin.

Bayan ya saurari roko daga lauya da kuma wasu daga cikin daliban, alkalin ya yanke wa kowannensu hukuncin shekara shida kan laifukan biyu.

Kazalika, kotun ta yanke musu hukuncin ne ba tare da zabin biyan tara ba.