✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shigo-shigo-ba-zurfi

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fara waiwayar  yankin Arewacin kasar nan da wasu manyan ayyukan raya kasa, domin kuwa a ranar Larabar da ta gabata…

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fara waiwayar  yankin Arewacin kasar nan da wasu manyan ayyukan raya kasa, domin kuwa a ranar Larabar da ta gabata Majalisar Ministoci ta bayar da wasu muhimman kwangiloli guda biyu da za su daukaka matsayin shiyyar Arewa-maso-Yamma, inda daya daga cikin wadannan ayyukan kuwa shi ne na farfado da  filin jirgin saman Malam Aminu Kano, wanda za a batar da Naira sama da miliyan dubu dari shida don aiwatarwa. Gudan kuma shi ne aikin tagwayen hanyoyin  Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya, a kuma zarce da su har Kano, yayin da za a fadada su  har fallan-uku, a kuma shimfida sabuwar kwaltar nylon  a  bisansu. 

Babu shakka wadannan ayyukan za su inganta matsayin garuruwan Abuja da Kaduna da Zariya da kuma Kano  ganin cewa suna da gagarumiun muhimanci  a shiyyar Arewa-maso-Yamma da kuma Babban Birnin Tarayyar Abuja.  Inganta filin jirgin saman Malam Aminu Kano zai dawo da martabar tashar jirgin saman  a makwafinsa na daya daga  cikin filayen jiragen  sama na farko da Turawa suka kakkafa a nahiyar  Afirka  don hulda da kasarsu a zamanin da suke mulkin mallaka.  Su kuma wadancan tagwayen  hanyoyin  da za a narkar da Naira sama da miliyan dubu kari da hamsin da biyar don sabuntawa nan da shekaru uku masu zuwa za su taimaka wajen habaka tattalin arzikin garuruwan da ayyukan za su shafa,  za su kuma inganta zirga-zirgan bil-adama da kayayyakin sayarwa da na amfani a gidaje da wuraren aiki da kuma saukaka jigilar amfanin goma zuwa manyan kasuwanni.  

Hobbasar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari  ta yi dangane da haka ya biyo bayan korafe-korafe ne da mutanen da suka zurara masa fiye da rabin kuri’un da suka mayar da shi shugaban kasa a zaben shekrar 2019 suka yi ta yi ne suna cewa ya fi mayar da hankali ga shiyyar Kudu-maso-Yamma, inda aka dade da aiwatar da wasu muhimman ayyukan layukan dogon jirgi da ingantattun hanyoyin mota da kuma samar da wutar lantarki ba daukewa a dan-tsukin  garuruwan Lagos zuwa Ibadan, inda kuri’un da al’ummomin yankin suka ba shi ba su kai kashi daya bisa uku na yawan wadanda mutanen shiyyar Arewa-maso Yamma suka ba shi ba. 

Shi ya sa mutanen shiyyoyin Arewa ke cewa duk da haka nan dai an kyauta da aka waiwaye su a lokacin da ake matukar bukatar ayyukan raya yankunansu, domin a cewarsu da babu ai gara ba dadi, kuma wanda ya ba ka gutsurten goro watarana bari ma zai mika maka. To amma sai dai akwai wadanda ke ganin cewa ai akwai  ayyukan wasu  tagwayen hanyoyi masu muhimmancin gaske  da aka  faro aikinsu tun l farkon hawan  Shugaba Olusegun Obasanjo a karon farko, fiye da shekaru goma sha hudu, an kuma yi nisa da su, amma aka watsar  da aikinsu. Akwai  tagwayen hanyoyi daga Kano, wadanda suka ratsa ta cikin jihohin Jigawa da Bauchi da Yobe har zuwa Maiduguri a Jihar Barno da kuma wadanda suka tashi daga Babban Birnin Tarayyar Abuja zuwa Lokoja wadanda ke da gagarumin muhimmanci wajen bubbude shiyyoyin da suka ratsa ta cikinsu amma  ba a waiwayarsu balle a san lokacin kammaluwarsu.

Dangane da haka ne ake ganin mayar da hankali a yanzu kan wasu ayyuka a yankin Arewa  na da alaka da siyasa da kuma zaben shekarar 2019. Irin wadannan ayyukan da za a tsira, a kuma kayyade lokacin kammala su fiye da wa’adin da gwamnatin da ta tsire su za ta yi bisa mulki, su ne matattakalan da gwamnati ke son bi don ta sake hayewa a karo na biyu, saboda  idan ta fara aiwatarwa  za ta kuma dan jinkirta don ta  shafawa talakawa mai a baki cewa za ta kammala idan har  sun sake amince mata ta zarce a karo na biyu. Ta haka ne sai ta samu amincewa muddin dai  talakawan sun yarda da cewa  idan ta zarce za ta ci gaba da gudanar da aikin. To amma akwai tabbacin cewa gwamnatin za ta kuwa cika alkawarin kammala irin wadancan ayyukan da ta faro a karon farko kuwa? Ai ga shi nan haka ne ma Gwamnatin Olusegun Obasanjo ta yi game da wadancan hnyoyin daga Kano zuwa Maiduguri da kuma Abuja zuwa Lokoja, kuma har yanzu ba a kammala ba.  Irin wannan al’amari shi ake kira sayen biri a bisa  domin kuwa talakawa ba za su iya ta hikankance  sakamakon zaben da za a yi ba nan gaba.

To a yanzu an ga alamun irin kamun ludayin da gwamnatin tarayya  ke son  yi a shiyyar Arewa-maso-Gabas  game da wadancan ayyukan hanyoyi da kuma filin jirgin sama, kuma ana iya cewa ta turza. Amma ai  sauran gwamnatocin jihohi na wannan shiryar  ba su taka wata rawar da za a yaba da ita ba wajen cika alkawurran da suka dauka yayin yakin neman zabe. Alal misali a Jihar Kaduna talakawa ba su dokin kwanzarta gwamnatinsu saboda  a cewarsu babu wasu ayyukan a-zo-a-gani da ta aiwatar, sai dai ‘yan kanzaginsa ne sukacika duniya da yare a kafafen yada labarai kullu-yaumin game da ayyukan da ayyukan da ba a tabbatar da su ba, wadanda suke cewa ana ta shimfidawa a ko ina a fadin jihar.

 A takaice dai ana iya cewa babu wata hanyar mota da ta hade wata karamar hukuma da wata, wacce aka shimfida mata kwaltar nylon, wacce kuma tsawonta ya kai kilomita ashirin da biyar da gwamnatin Jihar Kaduna za ta bugi kirji ta ce ta  gina.  Wadanda ma take tinkaho ta giggina ‘yan gutsul-gutsul ne a cikin  wasu ‘yan unguwanni da aka bude su da rairayi ko  burji,  aka kuma zizara musu ‘yar kwaltar da aka hada da  kura-kuran duwatsu. Ruwan daminar da aka yi a shekaru biyun da suka shude sun wanke hanyoyin har sun koma gidan jiya  da wuya kuma masu amfani da su ke gane  bambancinsu da yadda suke tun can fil-azal.

Baicin haka nan kuma ga ayyukan tagwayen titunan cikin unguwannin Dosa da  Rigasa da Barnawa da aka faro kusan shekaru uku, amma an kasa kammalawa,  kuma tun da ya zama wajibi ababen hawa su yi zirga-zirga bisansu ba abin da haka ke haddasawa illa kurar da bulbule mazauna wuraren suna kwalliya da ita, suna kuma fama da ciwurwukar da ba su iya samun magungunan warkarwa a asibitocin da gwamnatin ta kasa kulawa da su. A tadaice dai ana zargin cewa haka nan za a  bar aikin wadancan hanyoyin unguwannin cikin garin Kaduna har sai  Gwamnatin Nasir el-Rufa’i ta kusa kai karshen wa’adinta sa’annan ne za ta waiwaye su da niyyar janyo hankulan jama’ar wuraren cewa za ta kammala musu ayyukan idan har suka amince za su sake zabenta ta koma bisa mulki. Anya kuwa talakawa za su iya amincewa da wannan shigo shigo ba zurfin?