Daily Trust Aminiya - Shigowar sanyi: Makon da gobara ta hallaka iyalai da dukiya
Subscribe

Shigowar sanyi: Makon da gobara ta hallaka iyalai da dukiya a sassan Najeriya

A cikin mako gudan nan an samu rahotannin yadda gobara ta hallaka iyalai da dukiya a sassan kasar nan, musamman bayan shiga yanayin sanyi da galibi ake samun haka. Wakilanmu sun tattaro wasu daga cikin hadduran kamar haka.

A Rigasa Jihar Kaduna:

A cikin dare a Larabar makon jiya ne wata gobara ta hallaka uwa da jaririnta da wadansu ’ya’yanta uku a Rigasa da ke a Karamar Hukumar Igabi, a Jihar Kaduna.

Gobarar ta faru da misalin karfe 2 na dare, kuma ta yi matukar tayar wa al’ummar unguwar hankali, domin ta cinye duk wani abu da ke cikin dakin matar. Babu kuma wanda ya san abin da ya jawo gobarar, sai dai an alakanta ta da wutar lantarki.

Amma bayanai daga wadansu daga cikin makwabtan gidan da ya kone, sun ce an kawo wuta da dare, wadda kuma ta zo da karfi. Wadansu na tunanin shi ya yi dalilin gobarar.

Aminiya ta samu bayanin cewa mijin matar mai suna Sani Yahaya Jumare ya kubuta daga wutar ta tagar bayi, lokacin da makwabta suka kai masa dauki.

Matar mai suna Rukayya da ’ya’yanta uku da ’yar kanwar mijinta, duk sun rasu sakamakon konewar da suka yi.

Wakilinmu ya zanta da mijin matar, bayan an sallamo shi daga asibiti, inda ya bayyana sunan ’ya’yan masa uku da suka kone, cewa akwai Rilwan (jariri) sai Rabi’atu, ’yar shekara biyu da Khadija mai shekara 6 da Hajara mai shekara 7. Sai kuma Hajara, ’yar kanwarsa da Allah Ya yi wa rasuwa a bara; wadda ta zo gidansa domin yin hutu, ita ma ta rasu a cikin gobarar.

“Ni kaina ban san zan rayu ba, domin bayan hayaki ya cika dakin sai ga wuta, sai Allah Ya sa makwabta suka taimaka wajen fito da ni ta taga.

“Amma matata da yaran, Allah bai ba su damar fitowa ba. Ban san inda nake ba lokacin da aka fito da ni, har aka kai ni asibiti,” inji shi.

Daya daga cikin wadanda suka taimaka wajen fito da shi, wanda bai ambaci sunansa ba, ya ce bai taba ganin abu irin wannan ba. “Gaskiya zan dade ban mance da wannan gobara ba, domin duk iya kokarinmu na bude kofarsu ya ci tura, sai da muka yi kusan minti 15  kafin kofar ta budu.

Koda muka bude kofar, matar da yaran duk sun rasu. Allah ne kurum Ya kawo wannan abu sai dai kurum addu’ar Allah Ya jikansu,” inji shi.

Wakilinmu ya ga yadda makwabta suka rika tururuwa zuwa yi wa mijin da danginsa ta’aziyyar wannan rashi da aka yi masa.

Shi ma mahaifin matar da ta rasu, Malam Sani Ladan ya ce babu abin da zai ce da ya wuce yi wa mamatan addu’a, domin Allah ne Ya san daidai. Ya kuma bayyana gobarar a matsayin babban bala’i, ldan aka yi la’akari da asarar dukiya da rayukan da aka yi.

“Ni na aurar da ita ga Sani, wato mijinta kuma na samu labarin abin da ya faru ne da misalin karfe 2:30 ne aka kira ni. Koda muka zo sai muka samu wannan mummunan labari, cewa ita da ’ya’yanta uku duk sun rasu. Ita kuma daya yarinyar ta zo hutu ne sai gobarar ta rutsa da ita. Abin da zafi amma haka za mu yi hakari, Allah Ya jikansu,” inji shi.

Shi ma wani mazaunin unguwar da ya ce yana daga cikin wadanda suka kai dauki cikin daren, Malam Jamilu ya ce hakika sun ga tashin hankali a wannan dare.

“Gaskiya akwai tashin hankali, domin duk kokarin ceto rayuwarsu da aka yi a daren ya ci tura. Mijin ne kawai Allah Ya sa aka fito da shi,” inji shi.

Ya ce yawancinsu ba su da lambobin wayar hukumar kashe gobara, ballantana su kira, su nemi taimakonsu.

A Ibadan Jihar Oyo:

Gobara ta hallaka kananan yara uku, wadanda iyayensu suka kulle su a cikin daki. Kananan yaran, Glory mai shekara 13 da Samuel mai shekara 8 da Darasimi mai shekara 3 sun gamu da ajalinsu da tsakar dare ranar Juma’ar da ta gabata ce lokacin da gobara ta tashi a dakinsu da ke Unguwar Molete a birnin Ibadan.

Aminiya ta jiyo daga makwabta cewa yaran sun rasu ne a dakin da iyayensu suka kulle su, lokacin da wutar ta kama suka kasa bude dakin.

Kamar yadda daya daga cikin makwabtan ya ce, “Kururuwar yaran ce ta tayar da mu daga barci da misalin karfe daya na dare,  inda muka yi iya kokarin ceto su ta hanyar balle kwadon da aka kulle dakin da shi. Amma kafin mu samu nasara, gobarar ta kone duk abin da ke cikin dakin tare da yaran.”

Makwabcin da aka sakaya sunansa ya ce, “Mahaifiyar yaran mai suna Christiana ta fita zuwa aikin dare ne da ta saba yi a wani kamfani da ke Ibadan, yayin da mijinta mai suna Tunde ya fice daga gidan domin kwana a wani wuri daban. Kuma sai da suka sanya makulli suka kulle yaran, kafin su fita.

Haka kuma wata gobarar ta daban ta tashi a garin Oyo da sanyin safiyar Lahadin da ta gabata, inda ta lashe shaguna a kasuwar Akesan; kuma wani yaro dan shekara 14 mai suna Wareed Akano ya rasa ransa dalilin harbin bindiga da aka yi a lokacin da wutar take cin kasuwar.

  ’Yan uwa na zaman makokin gobara a  Rigasa Hoto: Shehu Goro

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Shina Olukolu ya musanta zargin da ake yi wa ’yan sanda na yin harbi a kasuwar. Ya ce ’yan sanda ba su yi harbi a wannan lokaci ba amma sun hanzarta isa kasuwar domin daukar matakin kare jami’an kwana-kwana daga yunkurin hallaka su da jama’a suka yi ko kona ofisoshinsu da na ’yan sanda na Durbar da ke a kusa da konanniyar kasuwar.

Aminiya ta jiyo cewa dimbin mutane da suka yi dafifi suna kallon yadda wuta take cin dukiyar jama’a, ba tare da kawo dauki daga jami’an kwana-kwana ba ne ya harzuka jama’a suka yi kokarin cinna wa ofisoshin jami’an tsaron wuta, wanda ya haifar da harbin bindigar da ya yi sanadin mutuwar yaron, mutum 4 suka samu munanan raunuka.

Kwamishinan ’Yan sandan, wanda ya nuna bakin ciki kan rashin isar jami’an kashe gobara kan lokaci, ya shaida wa ’yan jarida a Ibadan cewa “Jami’an kashe gobara daga Ibadan ne suka garzaya zuwa garin Oyo (tafiyar awa daya) domin shawo kan wutar dalilin rashin kayan aiki da jami’an suka fuskanta.

“Mun hanzarta isa wurin ne domin tserar da jami’an kwana-kwana da ’yan sanda daga barazanar hallaka su da wadansu mutane suka yi saboda kasa shawo kan wutar kafin ta kazanta. Kuma mun yi amfani da wannan dama wajen hana miyagun mutane satar kayan da ke cikin kasuwar,” inji shi.

Haka kuma wata gobarar ta tashi a ranar, a kusa da ofishin binciken manyan laifuffuka na ’yan sanda (CID) da ke Iyaganku a birnin na Ibadan, inda shagunan sayar da gadaje da kujerun alfarma suka kone kurmus.

A garin Omi-Adio da ke kusa da Ibadan, wata gobarar ta tashi a ranar Asabar, inda aka yi asarar dukiya da kadarori na miliyoyin Naira.

Dukkan wadannan gobara 4 da aka yi a tsakanin ranakun Juma’a da Lahadi din da suka gabata, mahukunta ba su yi bayanin dalilin aukuwarsu ba, sai dai ana hasashen cewa ba za su rasa nasaba da wutar lantarki ba.

Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo da Ministan Wasanni Mista Sunday Dare da Jam’iyyar APC ta Jihar Oyo da Sanata Teslim Folarin da Aare Ona Kakanfo, Cif Gani Adams duk sun jajanta wa Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi da  ’yan Kasuwar Akesan kan wannan ibtila’in da ya rutsa da su.

Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na Jihar Oyo, Farfesa Raphael Afonja da ya ziyarci kasuwar a madadin Gwamna Makinde, ya ce gwamnati za ta sayo sababbin motocin kashe gobara na zamani guda 10 da za a girke su domin shirin ko-ta-kwana. Ya ce babu yadda za a yi a ci gaba da amfani da tsofaffin motocin kashe gobara da suka dade suna aiki a jihar.

A Jos Jihar Filato:

Hayakin gawayi ya yi sanadiyyar kashe matasa biyu a Jos, sakamakon matsanancin sanyi da ake fama da shi a halin yanzu a garin Jos da wasu sassan kasar nan. Matasan  biyu sun rasu ne, bayan shakar hayakin gawayi  da suka kunna a dakinsu don jin dumi a daren Juma’ar da ta gabata. Al’amarin ya faru ne a Unguwar Rikkos da ke garinn Jos.

Su dai wadannan matasa, Saminu Idris da Idris Dahiru dukkansu ’yan shekara 25, sun kunna gawayin ne a dakinsu da nufin su ji dumi da misalin karfe 11 na daren ranar ta Juma’a, suka kulle dakin suka kwanta. Ba su tashi ba har gari ya waye,da aka ji shiru ne aka balle dakin, aka samu sun rasu.

Da yake wa Aminiya karin bayani kan yadda lamarin ya faru, mai gidan da abin ya faru, wanda kuma yaya ne ga daya daga cikin matasan, mai suna Labiru Idris ya  ce “A ranar Juma’a da misalin karfe 11 na dare, Saminu ya kira ni a waya. Ya ce in bude masa kofar gida zai dauki kaskonsa saboda zai kunna gawayi a dakinsa, za su ji dumi.”

Ya ce nan take ya sa matarsa ta tashi ta bude kofar gidan, ta ba shi kaskon. Ya ce da  gari ya waye ya fito tsakar gida da misalin karfe 6:30 na safe sai ya ji kauri ya yi yawa a gidan. Sai ya tambayi matarsa abin da yake kauri, sai ta ce ita ma tunda ta tashi take jin wannan kauri.

Ya ce ya je ya bude dakin da ake dafa abinci, ya duba bai ga abin da yake kauri ba. Sai ya tafi kofar gida, zai bude kofar ke nan sai ya ji kaurin ya yi yawa. Saboda tagar dakin matasan tana kusa da kofar gidan. Da ya ja tagar sai ya ga hayaki yana fitowa. Sai ya kira sunan kanen nasa  sau biyu amma bai amsa ba.

“Na bude kofar gida na tafi dakin, na girgiza kofar dakin na ji a kulle saboda sun sa sakata ta ciki. Sai na je na tashi makwabta muka balle kofar, sai muka ga hayaki ya turnuke a dakin. Na yunkura na shiga, sai na ga hannun kanena ya kandare, babu alamar yana da rai, hankalina ya tashi a lokacin. Shi ne na gangaro zuwa Unguwar Gangaren Jos, gidan mahaifinmu na gaya masu abin da ya faru. Shi ne suka tafi gidan, kafin mu isa makwabtana sun fito da gawarwakinsu, sun rasu su biyun,” inji shi.

Ya ce a ranar da lamarin ya faru ba ya iya yin magana saboda tashin hankali. Ya ce amma daga bisani ya mika komai ga Allah, domin Shi ne Ya kawo wannan lamari.

A Zariya Jihar Kaduna:

A ranar Asabar da ta gabata ce mummunar gobara ta hallaka yara biyu tare da kone dimbin dukiya a Layin Dan Laura da ke Hayin Dogo Samaru a Karamar Hukumar Sabon Garin Zariya, a Jihar Kaduna.

Aminiya ta ziyarci gidan da gobarar ta faru, inda ta ga jama’a na tururuwa domin ta’aziyya ga musu gidan a kan rashin da suka yi.

Mai gidan da lamarin ya shafa Malam Abubakar Ibrahim ya ce, “A ranar Asabar da misalin karfe daya na rana, ina wajen aiki aka kira ni cewa in dawo gida da sauri. Da dawo sai na ga gidana ne ke cin wuta kuma jama’a ta taru tana ta kokarin kashewa, har motar kashe gobara ta zo. To, da zuwana sai na yi kokarin shiga domin ina da wata ajiya a dakina, sai mutane suka rike ni, ina kallo na hakura.”

Malam Ibrahim ya ce, “Zaton da muke yi, tunda wutar ta kama da rana ce kowa ya fita, ashe akwai sauran yara biyu da Allah Ya kaddari kwanansu ya kare, su ba su fita ba. Yaran su ne Ibrahim Nasiru dan shekara shida da kanensa Ahmed Nasiru dan shekara uku; dukkansu uwa daya uba daya. Baya ga asarar rai sai ta dukiya, wadda ba a san adadin abin da muka rasa ba, sai muhimman takardu, na makarantar yara, domin akwai ma takardar shiga jami’a da yarinyata ta samu; duk sun kone. Ka ji irin asarar da aka yi, sai dai kuma wannan jarrabawa ce daga Allah. Ina fata Allah Ya sa haka ya zama alheri. Su kuma jikokina da suka rasu, ina fata Allah Ya jikansu da rahama. Ina mika godiya ga makwabtana da sauran al’ummar da suka zo mana ta’aziyya da jaje.

More Stories