✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin gwamnati ta saki mayakan Boko Haram kafin ceto fasinjoji jirgin kasa?

Sojoji ne suka shige gaba wajen tattaunawa wanda a karshe aka samu nasara.

Kwamitin Yaki da Matsalar Tsaro na Shugaban Rundunar Tsaro (CDSAC), ya musanta batun cewa musaya aka yi da fursunonin Boko Haram wajen ceto ragowar mutum 23 da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Sakataren CDSAC, Farfesa Usman Yusuf ne ya musanta batun yayin wata tattaunawa da Gidan Talabijin na Arise ya yi da shi a ranar Talata.

Yusuf ya ce babu inda ya yi wani tsokaci mai alaka da musayar fursunonin su 101 da ake tsare da su a gidan yarin Kirikiri da ke Legas da kuma ragowar fasinjojin 23 da aka yi garkuwa da su.

Ya ce babu kamshin gaskiya cikin batun da ya yi zargin aikin wasu masharranta ne masu neman bata wa kwamitin suna a idon duniya.

Ya kara da cewa, ko kadan wannan ba zai hana kwamitinsu ci gaba da kokarin sauke nauyin da aka dora masa ba na yaki da matsalar tsaro a fadin kasar.

A cewarsa, sojoji ne suka shige gaba wajen tattaunawa wanda a karshe aka samu nasarar kubutar da fasinjojin da lamarin ya shafa.