Daily Trust Aminiya - Shin jinkirin nada ministoci zai iya yin illa ga ci gaban ka
Subscribe

Jinkirin nada ministoci ba zai kawo illa ba
–Yunusa Manu

Shin jinkirin nada ministoci zai iya yin illa ga ci gaban kasa?

Batun nada ministoci a kasar nan ya kasance wani abu da jama’a ke ta magana a kai, saboda yadda Shugaban Kasa ya dauki dogon lokaci bai nada su ba. Wadansu suna ganin Shugaban ya yi haka ne domin ya samu damar zakulo sahihan mutanen da zai bai wa wadannan mukamai, ganin a wannan karon ya ce zai bai wa mutanen da ya sani kuma masu kwazo da kishin kasa, sabanin nadin da ya yi a mulkinsa na farko, wanda ya ce ’bai san akasarinsu ba.Wakilanmu sun jiyo ra’ayoyin jama’a a kan wannan jinkirin na nada ministoci:

Jinkirin nada ministoci ba matsala ba ce –Umma Ibrahim

Daga Ahmed Garba Mohammed Kaduna

A gaskiya ko ba a nada ministoci da wuri ba, hakan ba zai kawo nakasu ga bunkasar tattalin arziki a kasar nan ba. Dalili  shi ne ai akwai wadanda aka dora wa alhakin kula da ma’aikatun da ke karkashin ministocin irin su manyan sakatarori  (Permanent Secretaries). Da za a ba su kudi kuma a sakar musu mara a nawa ra’ayin za su gudanar da ayyuka tamkar akwai ministoci a ma’aikatun nasu.

Sannan da yawa daga cikin ministocin da aka nada a baya babu abin da suka gudanar na ci gaban kasa, kansu kawai suka sani. Don haka da minista ko ba minista in dai akwai kudi da tsari za a samu bunkasar tattalin arziki.

Rashin nada ministoci kan iya kawo illa –Isah Abdullahi

Daga Hussaini Isah, Jos

Gaskiya duk wanda ya san gwamnati, ya san cewa tana da fika-fikai, wadannan fika-fikai kuwa su ne ministoci. Don haka matukar aka ce kasa za ta zauna babu ministoci, babu shakka zai kawo jinkiri ga  ci gaban kasa. Domin Shugaban Kasa ba zai iya aiwatar da mulkin kasa shi kadai ba, musamman kasa kamar Najeriya mai jihohi  36 da kananan hukumomi 774. Don haka muna kira ga Shugaban Kasa ya yi gaggawar nada ministocinsa. Domin rashin nada ministocin nan zai iya kawo illa ga kasar nan.

Jinkirin yana da kyau–Al-Amin Karshi

Daga Muhammad Aminu Ahmad

A ra’ayina gaskiya jinkirin yana da kyau, dalili kuwa ya kamata a ce Shugaban Kasa ya zauna ya tantance wa ya kamata a ba shi mukamin minista. Domin bai kamata a ce Shugaban Kasa ya nada ministoci haka kai-tsaye ba, don idan ba a jinkinta wannan nadin ba za a nada wadanda ba su cancanta ba, inda a maimakon su kawo ci gaban kasa sai a samu kishiyar haka. Don haka ya kamata mu kara hakuri  mu bai wa Shugaban Kasa lokaci ya zabo sahihan mutanen da zai nada a mukaman ministoci, domin wannan jinkiri zai zama alheri ne ga kasar nan.

Wannan jinkiri ba ya da amfani – Magaji Abdullahi Ibrahim

Daga Muhammad Aminu Ahmad

A gaskiya wannan jinkirin ba ya da wani amfani, a yi kokari a nada ministoci. Ba don komai na fadi haka haka ba, insha Allahu nadawar za ta sa wasu ’yan wahalhalu da ake ciki a samu afuwarsu. Saboda haka ne za a samun walwala don ma’aikatu za su samu kudin da za su ba da damar sayen abubuwa a hannun ’yan kasuwa. Kuma a dalilin nadin ministoci kowace ma’aikata za ta samu kasafin kudinta, inda harka za ta kankama. Don haka ba na goyon bayan jinkirin nada ministoci don zai iya kawo illa ga ci gaban al’umma kamar yadda na fada.

Rashin nada ministoci babbar illa ce – Amina Ibrahim

Daga Ahmed Garba Mohammed Kaduna

A gaskiya rashin nada ministoci a kan lokaci ba karamin koma-baya yake janyo wa tattalin arzikin kasar nan ba. Dubi yadda Shugaba Buhari ya shafe kimanin wata 6 a shekarar 2015 kafin ya nada ministoci, hakan ya gurgunta tattalin arziki.  Sannan yanzu rashin ministocin yana kawo cikas wajen gudanar da ayyuka.  Duk ma’aikatar da ka taba a yau sai ka ji an ce komai ya tsaya saboda babu minista. In kuwa haka ne ashe minista yana da alfanu a bunkasar tattalin arzikin kasa.

Jinkirin nada ministoci ba zai kawo illa ba –Yunusa Manu

Daga Hussaini Isah, Jos

Gaskiya a fahimtata duk abin da aka yi shi cikin gaggawa za a iya samun kuskure. Don haka duk wani abu da za a yi, yana bukatar natsuwa don haka mai yiwuwa fadar Shugaban Kasa tana shirye shiryen nada ministoci ne, don ganin ta dauko mutanen da suka kamata su zama ministocin. Domin mun san abubuwan da suka faru a baya, inda aka nada ministocin amma aka yi ta samun korafin cewa wadansu ba su cancanta ba. Don haka yanzu fadar Shugaban Kasa tana lissafi ne, domin ta samo mutane ingantattu wadanda suka dace, don guje wa irin abin da ya faru a baya. Don haka babu wata matsala dangane da wannan jinkiri na nada ministoci. Domin ana bincike ne a dauko ingantattun mutane da za a nada ministocin.

More Stories