✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin Kano maboyar miyagu ce?

A watannin baya jami’an tsaro sun yi ta kama mutanen da ake zargi da miyagun laifuka da suka boye a Kano daga wasu jihohi. Ko…

A watannin baya jami’an tsaro sun yi ta kama mutanen da ake zargi da miyagun laifuka da suka boye a Kano daga wasu jihohi.

Ko da yake jihar na fama da irin nata masu aikata laifuka iri-iri a cikin gida.

Daga cikin wadancan manyan kamu da jami’an tsaro suka yi akwai wadanda suka yi garkuwa da Magajin Garin Daura, kuma surukin dogarin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wato Alhaji Musa Umar Uba wanda aka sace shi a garin Daura a watan Mayun 2019.

Sashe na musamman na Yaki da Miyagun Laifuffuka na Ofishin Sufeto Janar din ‘yan sanda, karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda Abba Kyari da hadin gwiwar Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano suka yi nasarar kubutar da Magajin Garin Daura, daga masu garkuwa da shi bayan ya shafe wata biyu a tsare.

A jihar ce kuma ‘yan sanda suka kama wanda ake zargin kasurgumin mai garkuwa da mutane ne a Jihar Taraba wato Hamisu Bala Wadume.

Ana zargin Wadume ne rikakken mai garkuwa da mutane ne da ‘yan sanda suke nema ruwa a jallo bayan mummunan rikicin da aka yi a garin Ibbi na Jihar Taraba wanda aka yi wa ‘yan sanda uku kisan gilla baya ga raunata wasu ‘yan sanda biyar.

Bayan da ‘yan sanda sun kama shi sai kuma ya tsere daga hannunsu da taimakon wasu sojoji da suka bude musu wuta a shingen bincike.

Daga karshe ‘yan sanda suka kama Wadume a maboyarsa da ke Layin Mai Allo a unguwar Hotoro, a garin Kano.

Har ila yau a Kano aka kama wanda ya yi garkuwa da jikan babban malamin darikar Tijjaniya a Najeriya Shaikh Dahiru Usman Bauchi, kimanin kwana biyar bayan sace Dan yaron.

Dan garkuwan ya sato yaron mai kimanin shekaru uku ne a yayin da Shaikh Dariru Bauchi ya gudanar da Sallar Idi a harabar gidansa da ke garin Bauchi.

Hukumar Bincike ta Farin Kaya karkashin jagorancin Muhammad Alhassan ta kama dan garkuwar ne a wani dakin otel ne tare da kudin da ya karba a matsayin kudin fansa Naira miliyan biyu da rabi.

Jami’an sun kuma yi nasarar tserar da yaron ba tare da samun ko kwarzane a jikinsa ba.

Me ke kawo masu laifi Kano?

Wannan ya sanya Aminiya yin duba da bincike game da dalilin da ke janyo hakan da kuma abin da ‘yan sandan Kano ke yi game da shi.

Yawan jama’a

Wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Malam Abdullahi Muhammad Bashir ya danganta yadda masu aikata miyagun laifuka ke zuwa Kano da yanayin garin Kano da ke da dimbin jama’a.

“Ita Jihar Kano kasancewarta matattara ta kasuwanci ya sa ba ta kyamar baki. Mutane suna zuwa daga wurare daban-daban a ciki da wajen kasar nan inda suke zama a jihar. Wannan ya sa jihar ke cike da al’umma.

Mutum zai iya zuwa Kano ya gama iya rayuwarsa a unguwar da yake wani ma bai san da shi ba saboda yawan al’umma”.

Sabbin unguwanni

Shi kuma Malam Ali Sanusi ya danganta lamarin da karuwar sabbin unguwanni da ake samu a jihar.

“Ni ina ganin abin yana da alaka da yawan samun sabbin wurare da ake yi, ma’ana sabbin unguwanni.

“Za ka tarar cewa a kullum mutane tarewa suke a irin wadannan unguwannin, wasu gidajen nasu ne wasu kuma na haya ne.

“Shi ya sa idan an wayi gari an ga wata bakuwar fuska ba abin damuwa ba ne. Za ka samu mutane ba su damuwa da sanin makwabtansu”, inji shi.

Sakacin masa unguwanni

Malam Khalid Gambo ya bayyana cewa ba komai ke kawo hakan ba illa sakaci na masu unguwanni.

“Yawanci idan kin duba za ki ga masu unguwannin ba su damu da sanin mutumim da ya shigo unguwarsu ba.

“Wannan ya hada da mutanen da ke sayen gidajen da kuma wadanda ke kama haya.

“Za ki samu cewa masu unguwanni sun sakar wa dillalai da masu bayar da gidajen haya ragama a hannunsu su suke gudanar da komai.

“A mafi yawan lokuta za a gama cinikin fili ko gida ba tare da mai unguwa ya san masu cinikin ba. Abin da ya sani shi ne sai dai a kai masa ‘yan canji ya karba ya sa a aljihunsa ya rattaba hannu a kan takardar ciniki kawai.

“Wannan ya sanya kowane irin mutum zai iya zuwa Kano ya mallaki gida ko ya karbi haya ba tare da samun wata matsala ba”, kamar yadda ya bayyana.

Me ‘yan sanda ke yi?

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano a nata bangaren ta bayyana cewa tana samun wadannan nasarori ne ta hanyar yin amfani da kayan aiki da kuma samun hadin kai daga sauran jami’an tsaro.

Kakakin rundunr ASP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa Aminiya cewa “Babu wani abu da muke yi illa iyaka muna amfani da dabarun aiki da kuma wasu kayan aiki musamman irin na’urar da ke bin diddigin mai laifi da sauransu.

Haka kuma mu muna gudanar da aiki ta hanyar samun hadin kai da sauran abokan aikinmu na tsaro inda muke samun nasarori a kan duk wani bata gari da ya shigo Kano da sunan samun mafaka.

Haka kuma al’ummar jihar suna ba mu goyon baya wajen gudanar da ayyukanmu”.

ASP Abdullahi Kiyawa ya kuma yi kira ga al’umma da su rika sanar da rundunar idan suka ga wani abu da ba su fahimce shi ba yana faruwa ko kuma idan suka ga wani mutum da ba su amince da motsinsa ba.