✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shin ko kana son zama mutumin kirki a rayuwa? (1)

Masu karatu, assalamu alaikum. A wannan makon za mu duba wani sabon maudu’in ne na daban. Wato bayani game da halayyar zama da abokai da…

Masu karatu, assalamu alaikum. A wannan makon za mu duba wani sabon maudu’in ne na daban. Wato bayani game da halayyar zama da abokai da kawaye. Dalili ke nan ma kanun madu’in namu ya yi tambaya, shin ko kana son zama mutumin kirki a rayuwarka? Ke ma ’yar uwa, ko kina son ki zama mutunniyar kirki a rayuwarki ta duniya? To ku biyo mu a cikin wannan madu’i, domin ganin matakan da suka kamata mu dauka, mu aiwatar a rayuwarmu ta yau da kullum, domin ganin mun cimma matsayin zama na kirki a rayuwa.

A rayuwa, dan Adam ba zai iya zama shi kadai ba. Idan ma har ya amince ya zauna shi kadai din, to ba haka aka so ba, wai kanen miji ya fi miji kyau. Mutum zai iya zama shi kadai ne kawai bisa lalura, wacce ba zai iya maganinta ba. Dalili ke nan ya sanya za ka ga mutane na zaune cikin gidaje, a unguwanni, a garuruwa da kasashe daban-daban. Haka kuma ya sanya za ka samu kowane mutum na da abokai, idan mace ce, tana da kawaye. To, wajen zabe da zama da abokai da kawaye, nan ma akwai abin lura da kula sosai, domin kuwa shi zaben da kuma zaman, wani yanayi ne na rayuwa na musamman. Don haka yana bukatar a zizara masa sinadari shi ma, domin a samu fa’idar rayuwa, domin a samu rayuwa cikin dacewa da amfani.

Masu iya magana sun ce, abokin damo guza, kamar kuma yadda suka ce, abokin barawo barawo ne. Abin da wadannan karin maganganu ke nufi a fili suke, musamman idan mun danganta su da halayyar dan Adam ta fuskar rayuwar yau da kullum.

Shi mutum, kamar yadda muka dan yi bayani a sama, ba zai iya zama shi kadai ba, wannan halayya ce ta sanya kuma ya kasance mai kwaikwayo. A halayya da dabi’a, mutum ya kasance mai kwaikwayo, mai rikida kamar hawainiya. Duk inda ya samu kansa, muddin ya ladabtu da yanayin wurin, to wannan ne zai kasance halayyarsa ta rayuwa. Ke nan duk yanayin irin abokan zamansa ko abokan mu’amalarsa, to irin wannan halayya zai kwaikwaya kuma ta zama dabi’a da al’adar rayuwarsa.

Abin bukata a nan shi ne, mutum ya iya zaben abokin zamansa, wanda zai dace da yanayi da rayuwa mai fa’ida ba gurbatacciya ba. Yin haka wani sinadari ne shi ma a rayuwa. Musamman ma idan muka dauki ma’anonin wadannan karin maganganu da muka kawo misalinsu a sama.

Za mu ci gaba