Daily Trust Aminiya - Shin kun san bukatun masu zanga-zangar #EndSARS?
Subscribe

Shin kun san bukatun masu zanga-zangar #EndSARS?

Tun makon jiya jama’a a sassan kasar ke zanga-zangar neman a kawo karshen cin zali da sauran nau’ikan tauye hakki da jami’an sashen ’yan sanda na SARS ke yi.

Ana zargin jami’an sashen mai yaki da ayyukan fashi —wanda yanzu aka rushe— da yin amfani da karfi fiye kima, tsare mutane barkatai da kuma kisa ba bisa ka’ida ba, zargin da suka sha musanata.

Ga bukatu biyar na masu zanga-zangar ta #EndSARS suka gabatar wa gwamnati a kan sashen:

  • A sakin mutanen da ake tsare da su saboda zanga-zangar nan take
  • A yi adalci ga wadanda ’yan sanda suka kashe a kuma biya iyalansu diyya
  • A kafa kwamiti mai zaman kansa da zai kula da bincike da kuma hukunta ’yan sanda da ke saba ka’ida (cikin kwana 10)
  • A yi gwajin kwakwalwa da kuma sake horas da jami’an SARS kafin a sauya musu wuraren aiki
  • A kara wa ’yan sanda albashi da zai ya dace da aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin jama’a
More Stories