✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin Ronaldo ne matsalar Manchester United?

Daga zuwansa zuwa yanzu, ya ci kwallo 23 a duk wasannin da ya buga a kakar bana.

A watan Agustan bara ne Cristiano Ronaldo ya dawo Manchester United daga Juventus ta Italiya wanda daga zuwansa zuwa yanzu, ya ci kwallo 23 a duk wasannin da ya buga a kakar bana.

A Firimiyar Ingila, ya zura kwallo 17, inda Mohammed Salah ne kawai ya fi shi zura kwallo da kwallo 22. Idan aka cire fanareti kuma, Salah zai koma kwallo 17, Ronaldo 15.

A kakar 2006/2007 lokacin Ronaldo yana dan shekara 23, kwallayen da ya zura ke nan.

Idan aka yi la’akari da cewa yanzu ne Salah yake zamani, da shekarun Ronaldo, za a iya cewa Cristiano ya tabuka.

Sai dai duk da kokarinsa, kungiyar ta Manchester United yanzu ita ce ta shida, inda Arsenal da ke ta biyar ta ba ta ratar maki biyar, sannan Manchester City da ke kan teburi, akwai tazarar maki 25 a tsakaninsu.

Man U a kakar bara

A wasan Chelsea da Man U da aka tashi daya da daya, magoya bayan Manchester din murna suka yi, har wasu na mamaki ba a lallasa su ba.

A kakar bara a daidai irin wannan lokaci, Manchester United ce ta biyu a Gasar Firimiyar Ingila a lokacin da Ronaldo din bai zo ba.

A barar, Bruno Fernandes ne yake jan kungiyar, inda ya zura kwallo 27 a kakar ta bara.

A kakar bana, zuwan Ronaldo an yi tunanin za a hada karfi da karfe ne tsakanin Ronaldo da Bruno Fernandes din, amma said Bruno ya kwanta.

A kakar bana kwallo tara kacal ya ci, kuma ya barar da fanareti guda biyu masu muhimmanci.

Matsalar Manchester United

A wasan Chelsea da Manchester United da aka tashi kunnen doki, Ronaldo ne ya farke kwallon da Marcos Alonso ya jefa a ragarsu.

Tashi daga wasan ke da wuya, sai tsohon kyaftin din Manchester United Rio Ferdinand ya wallafa a shafinsa na twitter cikin barkwanci cewa “Har yanzu dai matsalar Manchester United din shi ne yake cin kwallayen.”

Wannan sakon na Ronaldo yana zuwa ne a daidai lokacin da wasu magoya bayan kungiyar suke ganin zuwan Ronaldo din koma-baya kawai ya haifar wa kungiyar.

Masu irin wannan tunanin suna ganin a kakar bara sun fi kokari, amma zuwansa da suke tunanin abubuwa su gyaru, sai suka tabarbare.

Sai dai duk da haka, idan aka cire kwallayen da Ronaldo ya ci a bana, Manchester United da yanzu tana tsakanin ta takwas ko na tara ce a teburi.

Sai dai wasu na ganin matsalar iyalan Gladzers mamallaka kungiyar ne. A kakar bana kadai an yi zanga-zangar rashin jin dadin yadda iyalan suke tafiyar da kungiyar.

Shi ma kocin kungiyar na wucin gadi, Rangnick ya bayyana rashin jin dadin yadda ake tafiyar da zawarcin ‘yan wasa a kungiyar.

Kallo ya koma sama

Yanzu da kungiyar ta dauko sabon koci, Ten Hag daga kungiyar Ajax.

Kocin yana da tarihin horar da ‘yan wasa sosai. Sannan kungiyarsa ta Ajax tana nuna bajinta sosai.

Sai dai wasu na masa kallon kocin kananan ‘yan wasa da kananan kungiyoyi.

Bai taba horar da babbar kungiya kamar Man U ba, ga kuma manyan ‘yan wasa. Yanzu haka rahotanni suna nuna cewa a rikice yake kan ci gaba da kasancewar Ronaldo a kungiyar ko kuma ya bayar da damar a sayar da shi.

Sai dai yanzu za a iya cewa kwallo ya koma, kuma ba a sanin maci tuwo, sai miya ta kare.

Wasu rahotanni da Jaridar Mirror ta wallafa na nuna cewa akwai yiwuwar Ronaldo zai koma tsohuwar kungiyarsa ta Real Madrid wadda ake jita-jitar ta soma zawarcinsa a yanzu.