✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin Shekarau ya soma shirin sauya sheka daga NNPP zuwa PDP?

Atiku zai gana da Shekarau a gidansa da ke Kano.

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya soma shirye-shiryen sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da wasu rahotanni ke cewa, dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya soma zawarcin tsohon gwamnan da wasu gwababan alkawura.

Shekarau wanda ke wakitar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP a hukumance cikin wata wasika da Shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan ya karanta a zauren majalisar a ranar 29 ga watan Yuni.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a ranar 24 ga watan Yunin da ta gabata ne Shekarau ya nemi zama mataimakin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi yayin wata ganawa da suka yi a a Jihar Legas.

Shekarau ya ziyarci Legas din ne bayan samun tikitin sake tsayawa takarar kujerarsa a jam’iyyar NNPP, wadda tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ke zaman jagoranta.

Sai dai kuma jaridar ta jiyo cewa, tattaunawar ta sha ruwa bayan da shugabannin APC da PDP suka fara zawarcin tsohon gwamnan domin karfafa shirinsu na samun nasara a Zaben 2023.

Rahotanni sun ce, tuni shugabannin jam’iyyar NNPP sun daura damarar rarrashin Shekarau, inda tawagar mutum 3 da ta hada da dan takarar gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, dan takarar Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila da kuma dan takarar Majalisar Wakilai, Kabiru Rurum, suka nemi ganawa da shi a daren Juma’a a Abuja, amma ba su samu ganinsa ba.

Wata majiya mai tushe da ke da masaniya kan wannan shiri na sirri da Shekarau ke yi inda ya rika ganawa a lokuta daban-daban da dan takarar Shugaban Kasa na PDP, Atiku Abubakar; abokin takararsa Ifeanyi Okowa, da Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyochia Ayu, ta tabbatar da cewa tuni tsohon gwamnan ya “cimma yarjejeniya” da PDP, kuma ana sa ran nan ba da dadewa ba zai bayyana ficewar sa a hukumance.

A cewar majiyar, a ranar Lahadin da ta gabata ma, Shekarau din ya kira taron gaggawa na Majalisar Shura kan harkokin siyasa, inda ya sanar da ’yan majalisar halin da ake ciki.

Bayanai sun ce, wani kwamiti mai mambobi 21 zai yi zaman gana wa a Yammacin Talatar nan domin kammala shirye-shiryen sauya shekar da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance suka da tofin Allah-tsine da magoya baya da ma sauran jama’ar gari za su yi da zarar Shekarau ya dauki wannan matakin na ba-zata.

Wata majiya da ke da masaniya kan taron ta ce, a wani bangare na shirin ficewar, Atiku zai gana da Shekarau a gidansa da ke Unguwar Mundubawa a Karamar Hukumar Nasarawan Kano domin neman dawo wa PDP kafin a fitar da sanarwar ficewar ta sa.

“Gaskiyar magana ita ce Atiku ya yi wa Mallam alkawura masu gwabi kamar na minista da na ma’aikata.

“Ya kuma yi masa alkawarin da nada shi a matsayin jagoran yakin neman zabensa a yankin Arewa maso Yamma da kuma kula da kudaden yakin neman zabe a yankin,” in ji majiyar.

Sai dai wata majiya ta kusa da Shekarau ta ce Sanatan ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar NNPP ne ya kuma ajiye takararsa ta Sanata saboda jam’iyyar ta ki bai wa yaransa takara.

“Shekarau bai ji dadin yadda NNPP ta ki bai wa yaransa takara ba, sai shi kadai kawai da ta bai wa takarar Sanata. Kaga sai su [yaransa] ga kamar kawai kansa ya ke yi wa yaki ba su ba,”