Shin talauci ne ke haddasa yin garkuwa da mutane? | Aminiya

Shin talauci ne ke haddasa yin garkuwa da mutane?

Al’amarin garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa ya ta’azzara a Najeriya, musamman a jihohin Arewa. Abin tambaya shin me ke haddasa wannan mugun aiki, talauci ko kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mabambantan mutane, wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:

 

Rashin tsoron Allah ne jigon garkuwa da mutane – Lawan Galadima

Daga Faruk Tahir Maigari

Mohammed Lawan Galadima: Maganar gaskiya abin da ya kawo karuwar garkuwa da mutane da ake fama da shi tun cikin shekarar 2015 zuwa yanzu, shi ne talauci da ya karfafa a cikin al’umma, domin talauci ba abin da ba ya haifarwa. Amma duk da haka rashin tarbiyya da tsoron Allah su ne manyan jigogin da ke sa mutane su kasa hakuri da talaucin da suke ciki, su shiga kungiyoyin batagari. Idan da mutane za su rika dangana al’amuransu ga Allah, ba shakka za a samu saukin rashin tsaro. Amma gaskiya idan talauci ya hadu da jahilci da son zuciya to yana iya haifar da komai.

 

Son cin banza ke haddasa garkuwa da mutane – Abubakar Sani Kayauki

Daga Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina

Abubakar Sani Kayauki: Tabbas, talauci na sanyawa a yi garkuwa da mutane da sauran wasu ayyukan assha. Da akwai ayyukan yi, musamman ga matasa da kuma wajen yin kiwo ga Fulanin da ke kan gaba yanzu wajen yin garkuwar da ba su yi yawo ba har su shiga wannan hali. Sannan girman kai da son cin banza da karancin kulawar iyaye da ita kanta hukumar, duk suna cikin abubuwan da suke bayar da gudunmawa wajen yin garkuwa. Sannan haduwa da batagarin abokai ma na taka rawa wajen haddasa garkuwa da mutane.

 

Ba talauci ne ke sanya garkuwa da mutane ba – Tasi’u Aminu Nababa

Daga Ahmad Ali, Kafanchan

Tasi’u Nababa: Ni a ra’ayina, garkuwa da mutane wata sabuwar hanya ce kawai ta yin fashi da makami, wadda ba talauci ne ke haddasa ta ba. Kawai sun lura da yadda mutane ba su tafiya da kudi a hannunsu, shi ya sa su ma suka canja nasu salo. Ka ga in an yi maka barazana da ran dan uwanka, dole ka nemi kudi duk inda suke ka kawo.

In da talauci ne ya kawo fashi, sai mu ce to su masu garkuwa da mutanen a ina suka samun kudaden da suke sayen makaman da suke amfani da su?

Bayan haka siyasa ma tana daga ciki, domin idan ka lura da inda abin ya fi kamari, misali Zamfara, za ka ga cewa ana kokarin a tarwatsa ’yan wannan jiha ce don a zo a kwashi ma’adinai da ke jihar. Ka ga in mutum ya ga kullum gari ba zaman lafiya, ga yin garkuwa da mutane, zai iya yanke shawarar yin kaura daga wannan gari ko jiha don samun kwanciyar hankali.

A tawa fahimtar, garkuwa da mutane, nau’i ne na ta’addanci kamar su Boko Haram da makamantansu. Abin da talauci ke iya kawowa shi ne kananan sace-sace da sauransu. Wadansu daga cikin masu garkuwa da mutane in sun shiga hannu, za ka ji suna cewa su ma sa su ake yi, wadansu kuma su ce ba da son ransu suke yi ba.

 

Wani gefen talauci na haddasa garkuwa da mutane – Sa’id Ahmad Sa’id

Daga Ahmad Ali, Kafanchan

Sa’id Ahmad: A nawa ra’ayin, talauci na daga cikin dalilan da ke sanya wadansu yin garkuwa da mutane, domin a Najeriya muna da matasa da dama da sun yi karatu ba su da aikin yi. Muna da wanda ma ba su samu damar yin karatu ba da mafi yawancinsu  ba su da aikin yi. Mafi yawancin wadannan matasa ’yan siyasa ke amfani da su a lokacin zabe. A lokuta da dama ’yan siyasa sukan samar musu da makamai da kwayoyi don su sha su bugu, su yi musu bangar siyasa. Wasu lokutan za ka ga koda sun yi laifi an kama su, su dai wadancan masu gidan nasu ke zuwa suna karbo su.

Su matasan da ma suna fama da talauci saboda karancin aikin yi sannan ga shi an koya musu ta’addanci; to me kake ganin zai biyo baya?

A irin wannan yanayi ne, bayan an gama harkar siyasa matasan sun daina samun dan abin da suke samu daga wajen iyayen gidansu, za ka ga sun koma suna amfani da wadancan makamai suna ta’addanci da ya hada da fashi da makami da  garkuwa da mutane da haddasa fitinu iri-iri a cikin al’umma.

Idan Gwamnatin Tarayya tana so ta magance wadannan matsaloli, to dole sai ta samar wa matasa ayyukan yi, an koya masu sana’a, sannan a jawo hankalin ’yan siyasar kasar nan su daina sa matasa a gurbatacciyar hanya.

 

Babu ruwan talauci– Shamsu Kabir

Daga Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina

Shamsu Kabir: Babu ruwan talauci a maganar garkuwa da mutane don amsar kudin fansa. Kawai son zuciya ne da rashin ilimi da tarbiyya da kuma rashin  dogaro da kai. Ai ba lallai sai da aikin gwamnati ba mutum zai rayu. Ba lallai sai an ci haram za a yi arziki ba. Amma saboda son zuciya da rashin tawakkali duk su suke sawa a shiga waccan harkar gami da kwadayi. Su wadanda ake gani sun yi kaurin suna a harkar yanzu, idan da sun hakura da abin da suke da shi, ai da ba su shiga cikin wannan mugun aiki ba. Ina kakanninsu? Ba su rayu cikin kwanciyar hankali ba? Kuma ina maganin talaucin da suka yi da kudaden da suke amsa? Kowane lokaci suna nan yadda suke sai ma ci baya!

 

Rashin tsoron Allah ke haddasawa – Aliyu Garba Karaye

Daga Faruk Tahir Maigari

Aliyu Garba Karaye (Babba): Tabbas, talauci yana taka muhimmiyar rawa wajen aikata miyagun laifuffuka, musamman garkuwa da mutane, lura da yadda rashin aikin yi ya mamaye matasa a kasar nan. Wannan ya sa wadansu marasa tsoron Allah shiga cikin kungiyoyin ’yan ta’adda.

Abu na gaba da ke jawo karuwar masu garkuwa da mutane shi ne ‘soshiyal midiya.’ Kafafen sada zumunta suna taka rawa wajen koya wa matasa ta’addanci. Mafi yawan lokaci a nan wadansu suke koyon dabarun kitsa yadda za su yi garkuwa da mutane, don haka ya kamata hukumomi su sa ido a kan kafafen sadarwa na zamani. Lallai ya kamata al’umma su tashi tsaye wajen rokon Allah Ya yaye mana wannan babbar musifa.