✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin ya dace a kaurace wa zabe idan gwamnati ta gaza magance matsalar tsaro?

Sheikh Nuru Khalid ya yi hudubarsa ce bisa ga madogara ta damuwa da halin da kasar nan take ciki.

A ranar Asabar da ta gabata ce dai aka dakatar da babban limamin Masallacin Rukunin Gidajen ’Yan Majalisar Tarayya da ke unguwar Apo a Abuja, Sheikh Nuru Khalid daga limanci.

Dakatarwar dai ta biyo bayan hudubar sallar Juma’ar da Shekh Khalid ya gabata a makon jiya, wadda ta haddasa suka mai tsanani, musamman a kafafen sadarwar yanar gizo.

Sheikh Nuru Khalid wanda ya bukaci jama’a kar su fito zabe matukar ba a inganta tsaro gabanin zaben ba, ya gamu da matakin kwamitin masallacin inda hatta tafsirin da ya saba na Ramadan, aka nada wani limami ya maye gurbinsa.

Sheikh Nuru Khalid a cikin hudubarsa ta ranar Juma’a, daya ga watan Afrilu, ya caccaki gwamnati kan gaza magance matsalar tsaro da kuma yawaitar kashe-kashe a Najeriya.

A cikin hudubarsa ta ranar Juma’ar da ta gabata, Sheik Nuru Khalid ya caccaki gwamnati kan gaza magance matsalar tsaro da kuma yawaitar kashe-kashe a Najeriya, inda ya yi kira ga al’ummar kasar da su kaurace wa babban zabe da ke tafe muddin ba a magance matsalar tsaron ba.

“Jinin talaka ya zama kayan kamfen a kasar nan.

“Don me ya sa duk lokacin da zabe ya kusa sai kashe-kashe su rika karuwa.

“Toh kamata ya yi talakan Najeriya ya gaya wa ‘yan siyasa ko dai ku hana kashe mu ko kuma mu ki yin zabe.

“Wannan shi ne sharadinmu. Idan ba ku sa an daina kashe mutane nan da ranar zabe ba, to mu ma ba za mu fito zabe ba.

“Domin ran mutane ya fi duk wata dimokiradiyya, duk duniya dimokuradiyya kare ran dan Adam ya kamata ta yi ba sa wa ana kashe mutane a banza da wofi ba,” inji Sheikh Nuru Khalid a hudubar tasa.

Wannan hudubar ce silar dakatar da Sheikh Khalid daga limanci, inda bayan kwana daya ya mayar da martani inda ya wallafa wata ayar Alkur’ani mai cewa: “Allah Shi ne mafi girma. Shi ke ba da mulki ga wanda Ya so, kuma Ya kwace daga wanda Ya so.”

“Ya Allah, Kai ne mai girma da daukaka, Kai ke ba da mulki ga wanda Ka so, Ka kwace daga wanda Ka so, Ka daukaka wanda Ka so, kuma Ka kaskantar da wanda Ka so. Dukkan alheri a hannunKa yake, Kai ne mai iko a kan komai,” kamar yadda ya wallafa.

Wannan martani da Sheikh Khalid ya mayar ya sanya Kwamitin Masallaci ya fitar da sabuwar sanarwa ta korarsa daga limanci baki daya.

Shugaban Kwamitin, Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau ne ya bayyana wannan sabon mataki kamar yadda BBC ya ruwaito.

A cikin wasikar da kwamitin masallacin ya fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun Sanata Dansadau, ta ce a yanzu an dauki matakin korarsa gaba daya saboda kin yin nadamar da ya nuna bayan dakatar da shi da aka yi.

Wasikar ta ce: “Akaramakallah ka fi ni sanin koyarwar Musulunci, manufar ladabtarwa ita ce don a gyara dabi’ar mutum.

“Abin takaici, martanin da ka mayar kan dakatarwarka ta nuna cewa, balle ma har ka nuna nadama kan abubuwan da ka fada.

“Shugabanci na bukatar sauke hakki ka’in da na’in. Idan kalamanmu sun bata wa ’yan kasa rai fiye da faranta musu, to akwai hakki a kanmu na daukar matakin da ya dace saboda al’umma.

“Ga dukkan alamu kuma kamar ba ka da niyyar gyara hudubarka ta ranar Juma’a ta yadda za ta yi daidai da halin rashin tsaro da ake ciki a Najeriya,” in ji sanarwar.

Sai dai a shirin Najeriya A Yau na ranar Litinin wanda Aminiya ke yadawa ta Intanet, Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri, Sarkin Malaman Duguri, Wakilin Malaman Bauchi kuma Shugaban Majalisar Malaman Abuja ya yi fashin baki a kan lamarin.

“Da farko dai sai dai na ce Inna lilLahi wa inna ilaiHi raji’un. Dalili kuwa shi ne a matsayina na wanda na san Nuru Khalid tun yana almajiri wanda yake neman ilimi har Allah Ya sa Ya zama abin da ya zama a yanzu.

“Duk da cewa na riga shi zuwa Abuja, ammq watakila tazarar da ke tsakaninmu ba ta dade ba. Kuma na san shi da kokarinsa da kwazonsa da jajircewarsa idan ya fahimci gaskiya yana tsayuwa a kanta.

“To amma sai dai kamar yadda muka sani duk lokacin da mutum ya tsayu a kan gaskiya, ko yake fadin gaskiya, toh ba kowa ke son abubuwan da yake fadi ba.

“Sannan kuma abin da ya shafi hikimar da za a bi wajen isar da ita gaskiya, toh lallai idan aka yi amfani da wasu kalmomi, watakila da wadannan abubuwa da suka faru da ba su faru ba.

“Tun da dai Allah Ya fadi mana a cikin Alkura’ni mai girma cewa Yana umartar a kirayi mutane izuwa gaskiya ta hanyar amfani da hikima.

“Amma Allah ba Yana nufin a sauya wa gaskiyar fuska ba ko kuma wata kafa ba, a’a, sai dai akwai hikimomi da kalaman da za a yi amfani da su ta yadda za su dace da halin da ake ciki kuma sako ya isa.

“Sannan kuma akwai abubuwan da yadda duk ka fade su, komai gaskiyarsu da jin dadinsu, to ba zai yi wa wasu dadi ba, musamman halin da muke ciki a kasar nan na rashin tsaro da rashin zaman lafiya da kuma sauran abubuwa.

“Duk da dai a yau wadanda kawai suka rage masu fadin gaskiya da jajircewa a kanta su ne malamai, malaman kuma na gaskiya.

“Don haka wannan abun da ya faru gaskiya ba mu ji dadinsa ba, wadda kuma akwai matakai da yawa wanda da an bi su, da ba a kai ga hakan ba.

“A tawa fahimtar, wannan kalmar shi Malam Nuru Khalid ba haka ya kamata a ce ya fade ta ba, tun da misali yaki ake yi a kan lalacewar kasa da kuma barna da abubuwa da yawa da ake zargin ‘yan siyasa ne suka haifar da su a kasa.

“Saboda haka babu yadda za a yi ka canza mummuna sai ka bi hanyoyin da ake bi a canza mummuna din, wato babu yadda ake canza gwamnati musamman mu a tsarin mulkin Najeriya ya zamo karbabbe sai ta hanyar zabe.

“Don haka zancen a kaurace wa zabe wannan ma bata taso ba.

“Domin da zaben ne za ku yi nazari ku fuskanci mutanen kirki wadanda ake kyautata musu zato na alheri wadanda suke da kishin kasa kuma suka san hukuncin Allah a kansu.

“Ma’ana ko suna kusa da malamai ko su ma kansu malaman ne, ta yadda idan aka zabo irin wannan, sai ka ga duk wata barna da muke neman tsari da ita, sai Allah Ya kawo mana saukinta ta hanyar wadanda aka zaba.

“Amma idan aka ce an kaurace wa zabe, ke nan a bar wa su wadanda suke lalatattu su ci gaba lalata kasar baki daya. Idan ba a je an yi zabe ba, ina za a samo irin wannan.

“Don haka wadanda ake zargin cewa ba mutanen kirki ba ne, ko tukunna mu din mu koma ga Allah, mu nemi gafararSa a bisa kurakuran da muka yi a baya sai Ya bamu mutanen kirki.

“Sannan kuma Shi ne zai kama hannayenmu, Ya yi mana ilhama cewa mu je mu zabi su wane.

“Sannan kuma mu din mun tuba mun koma gare shi, sai kasa ta yi kyau, duk wadanda ake gudu ko zargin ma ko abubuwan da ake sai su zamo tarihi da izinin Allah.

Ke nan kaurace wa zaben ba shi zai kawo mana sauki matsalar da muke fuskanta ba?

Sheikh Duguri ya ce “Gaskiyar magana shi ne zuwa a yi zaben shi ne zai kawo mana saukin wadannan abubuwa, domin duk wanda yake ba na kwarai ba, idan aka ce an barsu ba za a je a yi zaben domin a sauya su ba, to an goya musu baya an taimake su ke nan.

“Saboda haka kaurace wa zabe ba shi matsalar Najeriya ba kuma ba shi ne zai magance matsalolin da muke ciki a kasar nan ba.

Shi ma Farfesa Muhammad Hussain na jami’ar Modibbo Adama da ke Yola a Jihar Adamawa, mai sharhi kan abubuwan da ka je su komo, ya goyi bayan a fita a yi zabe, sai dai ya ce Sheikh Nuru Khalid ya yi hudubarsa ce bisa ga madogara ta damuwa da halin da kasar nan take ciki.