Daily Trust Aminiya - Shin ya dace a samar da ‘yan sandan jihohi?
Subscribe

Shin ya dace a samar da ‘yan sandan jihohi?

Samar da ‘yan sanda jihohi lamari ne da aka dade ana ta magana a kansa tun lokaci mai tsawo, amma sai dai a kwanakin baya ne Sakataren Gwamnatin Tarayya ya kafa wani kwamiti na mutane 14, a kan ya yi nazari game da kirkiro ‘yan sandan jihohi, duba da yadda lamarin tsaro ya tabarbare a kasar nan. Ganin hakan ne ya sa Aminiya ta jiwo ra’ayoyin mutane a kan wannan yunkuri na kirkiro ‘yan sandan jihohi.

Bana goyon bayan hakan – Lawan Aliyu

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiya bana goyon bayan hakan, domin kirkironsu babu abin da zai haifar sai karin lalacewar al’amura,na cin hanci da rashawa da kuma yin amfani da su wajen cuskunawa wanda shugaba yake da matsala dashi. Zai fi kyau a inganta wadanda muke da su na kasa, idan har suka sami horo mai kyau babu abin da ba za suyi ba, amma karin kirkiro da wasu ‘yan sanda na jihohi wani barnar kudin kasa ne.

Abu ne mai kyau – Abdul’aziz Ahmed Nababa

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiya kirkiro ‘yan sanda jihohi yana da kyau, idan aka yi du ba da yawan matasa marsa aikin yi a kasar nan, samar da ‘yan sandan na jihohi zai bawa kowacce jiha damar daukar ‘yan asalin yankunansu cikin wannan aikin, kuma har ila yau zai taimaka wajen rage aikata laifuka, domin duk wanda yayi laifi an san shi, dan wanane ko jikan waye, kuma idai akwai aikinyi a tsakanin al’umma, yawan aika ta laifuffuka zai ragu, don haka ina goyon bayan kirkiro ‘yan sandan jihohi.

Babu wani amfanin kirkiro su – Zainab Umar

Daga Faruok Tahir Maigari

Ni kam ban ga  wani amfani da kirkiro ‘yan sandan jihohi zai kawo mana ba, wanda ma muke da su na tarayyar ma, yaya aka kare da su, balle wai ‘yan sandan jihohi wannan ai an bada dama ga masu ruwa da tsaki a matakan jihohi su ci karensu babu babbaka, babu wanda ya isa yayi Magana, don haka ko su ‘yan sandan da muke da su a yanzu basa yin abin da yakamata wanda al’ummar kasa suke fatan samu daga gare su.

Kamata yayi a rinka tantance wadanda za a dauka a aikin ‘yan sanda, domin mafi yawansu basu da halayya ta kwarai, ga cin hanci, abu ne mai wahala kaga an kama mai laifi, ba a karbi na goro ba a hannunsa, a maimakon gurfanar da shi gaban sha’ria.

Sam bai cancanta ba– Usman Aliyu

Daga Muhammad Aminu Ahmad

A ra’ayina sam bai cancanta ba, domin hakan yan siyasa, kan iya yin amfani da su wajen cin mutunci abokanan adawarsu, domin su ne suke da iko da su, to kaga an yi abu domin ya taimakawa al’umma, amma sai ya zama na kuma wata kafa ta cin zarafin duk wanda wani babba baya kauna, don haka ni dai bana goyon bayan kirkiro irin wadannan ‘yan sanda. Abu na biyu kuma zai sa daraja ‘yan sanda na tarayya da muke da su ya fadi. Na uku kuma ‘yan uwan irin wadannan ‘yan sanda na jihohi kan yi amfani da wannan dama wajen cin mutunci wani.

Bana goyon bayan kirkiro ‘yan sandan jihohi – Bashir Umar

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Idan har aka kirkiro ‘yan sandan jihohi, to za a kashewa ‘yan banga karfin da suke da shi da kuma gudunmawar da suke bayarwa wajen inganta tsaro a kasar nan, da jihohi domin haka ni dai a ra’ayina bana goyon bayan kirkiro yan sanda jihohi, gara a karawa ‘yan banga karfi da basu kayan aiki, kuma gwamnati ta basu duk kulawar da ta dace, don kuwa suna taka muhimmiyar rawa wajen habaka tsaro, kuma Gwamnoni ma kan iya amfani dasu ta wajen siyasa da sauran abubuwa, ni dai nafi son a karfafa ‘yan banga a hada kai da sarakunan gargajiya domin ta hakan ne kawai za a magance matsalar halin da tsaro ya shiga a kasar nan, ba wai kirkiro ‘yan sandan jihohi ba.

Bai kamata ba–Ibrahim Ibn Sani

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiya bai kamata ba, domin a yanzu ko ‘yan sandan da muke dasu a kasar nan, babu abin da suke illa yin abin da su ka ga dama, domin idan ka duba a halin da muke ciki zaka ga dan sanda a maimakon ya kare doka sai ka ga shi ne, mai karya dokar, kai ko wani laifi aka kama wasu sun aikata sai wani lokaci  akan samu ‘yan sanda cikin masu laifin, don haka mu lallaba da wadanda muke da su a maimakon kirkiro ‘yan sanda na jihohi a matsayina na dan Najeriya.

More Stories