✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin ya dace miji ya hana matarsa amfani da kafafen sada zumunta?

Ra'ayoyin ma'aurata kan dacewa ko rashin dacewar hana mata amfani da kafofin sada zumunta.

Samuwar intanet ta kawo ci gaba ga rayuwar dan Adam, ciki har da kafafen sada zumunta da mutane ke amfani da su wajen sada zumunci, kasuwanci, bincike da sauransu.

Amma ta bangaren auratayya, akwai lokuta da aka samu cewa kafafen sada zumunta sun haddasa manyan matsaloli a tsakanin ma’aurata.

A wasu lokutan, kafafen na sada zumunta na kawar da farin ciki a tsakanin ma’aurata, idan aka yi rashin sa’a har ta kai ga rabuwa.

A kan haka ne wasu mazaje ke hana matansu amfani da kafafen sada zumunta da zarar sun yi aure, matakin da yawanci ake tata-burza a kansa.

Don sanin ya ko dace maza su ke hana matansu amfani da kafafen sada zumunta bayan aure ko akasin haka, Aminiya ta tattauna da ma’aurata maza da mata a kan wannan batu.

Da kamar wuya

Muhammad Basheer Salisu, wani magidanci a Kano ya bayyana wa Aminiya cewar, “Magana ta gaskiya muna cikin wani zamani da kusan ba mata ba, ko da ’ya’yanka hana su amfani da kafafen sada zumunta abu ne mai matukar wahala, saboda duk yadda ka kai da kulawa ba za ka zauna da su ko yaushe ba.

“Amma magana ta gaskiya idan miji ya hana matarsa ko ’ya’yansa amfani da kafafen sada zumunta ba za a ga laifinsa ba, sai dai ma a jinjina masa, duk da dai ba abu ne mai sauki ba, musamman idan mutum ya yi rashin sa’a matar tashi tana da rawar kai.

Hanawar ta fi

“A wannan zamanin za ka ga matan aure da yawa kansu na rawa, ba sa jin kunyar su zo kafafen sada zumunta su saka hotunansu ko bidiyo ko wani abu musamman a irin su TikTok da Instagram.

“Idan ka shiga za ka ga babu abin da ake sai wannan. Ko mata su saka wakar Hausa ko ba ma ta Hausa ba suna rerawa suna rawa.

Zai kashe musu sana’a

“To idan ka yi la’akari da wannan, za ka ga to mene ne amfani? Idan an hana din zai fi amfani a gare su.

“Amma wasu matan ita ce hanyar cin abincinsu; Idan ka shiga Instagram za ka ga akwai matan da ba su da aiki sai sanya hotuna na abubuwan da suke sayarwa kala-kala.

“To wadannan ka ga ba za a ce za a hana su ba, sai dai a kafa musu sharadi kan inda ya kamata su tsaya da inda bai kamata su je ba a cikin wadannan kafafen sada zumunta.

“Amma matan da ba su da wata alaka da irin wannan sai sheke ayarsu, hana su zan iya cewa wajibi ne domin idan muka yi la’akari da addininmu da al’adarmu ba su yarda da irin wadannan abubuwa ba kuma a addinance wajibi ne mutum ya zama ya taka wa matarsa burki a kan duk abubuwan da suka sabawa shari’a da dokoki irin na shari’a ko al’ada, saboda haka hanawar ma za ta iya zama wajibi a irin wannan lokaci.”

Aisha Inusa Muhammad, matar aure ce daga Jihar Ogun, ita ma ta shaida wa Aminiya ra’ayinta kan wannan dambarwa.

“A gaskiya a tunani na bai kamata a ce mazaje su rika hana matansu amfani da kafafen sada zumunta ba bayan aure, domin kuwa yadda suke kallon matsalolin da kafafen ke haifarwa, kazalika akwai alfanu mai tarin yawa a kafafen sada zumuntar da mata ke amfani da su.

“Misali za ka ga mata na koyon kwalliya, girke-girke kala-kala a kafafen sada zumunta da abubuwa da dama ma da su ke amfanuwa da su.

“Kawai dai abin da nake tunani, namiji ya kafa dokar yadda mace za ta rika amfani da wayarta sannan ya rika bibiyar mutanen da suke mu’amala a kafafen sada zumuntar, in sha Allahu idan aka yi haka ba za a samu wata matsala ba.”

Mai daki shi ya san inda ke masa yoyo

Wata matar aure a Kaduna, Rahama Aminu, ta ce, “Rayuwar da mata ke yi a kafafen sada zumunta ya zama wajibi ga mazajensu su hana su amfani da su.

“Saboda da yawan matan a yanzu za ka ga suna mu’amala da mazajen da ba muharammansu ba kuma hakan ya saba da dokar addini. Ga rayuwar karya da matan suka koya a dalilin amfani da kafafen sada zumuntar.

“Don haka ni a ganina idan miji ya hana matarsa amfani da kafafen sada zumunta bai yi laifi ba, saboda mai daki shi ya san inda ke masa yoyo,” a cewarta.

Ba mazan ba, ba matan ba

Shi kuwa Abubakar Sulaiman, dan jarida ne kuma mazaunin Maiduguri a Jihar Borno, cewa ya yi, “Kalubalen da kafafen sada zumunta ke haifarwa a tsakanin ma’aurata na da yawa, sai dai yawanci mutane sukan yi magana ne daga nesa saboda su ba ma’aurata ba ne ko bai faru a kansu ba, sun ga ya faru a kan wasu ne.

“Akan tura wa mata sakonni a kafafen sada zumunta saboda kawai an ga mata ne.  Wasu abubuwan da ke faruwa ba ma laifinsu ba ne, hakan na haifar da matsala a duk lokacin da miji ya duba wayar matarsa saboda tsaro.

“A wasu lokutan kuma akan samu akasi matar ce ke neman wani ko saurayinta ko dai wani a waje haka; Sukan yi amfani da kafafen sada zumunta, ka ga wannan ta bangaren matar ke nan.

“Ta bangaren namijin shi ma, haka za ka ga wasu daga ciki suna amfani da kafafen sada zumunta domin neman wasu matan daga waje ko kuma su sa a tura musu hotunan da ba su dace ba ta cikin wannan hanya, yayin da watakila wata rana matar ta je ta duba sai ka ga ya haifar da matsaloli.

“Ka ga wadannan su ne manyan abubuwan da ke jawo matsaloli wajen amfani da kafafen sada zumunta tsakanin ma’aurata, har ma yakan zo lokacin da zai saka zargi tsakanin juna, matar tana zargin mijin ko kuma mijin yana zargin matar kuma duk amfani da wadannan kafafen sada zumuntar ne ya jawo.

“Yanzu an wuce lokacin da za a ce kana buga waya da mace ko kina buga waya da saurayi, yanzu za ki yi shiru kina aika sako ko ya yi shiru yana aika sakonni ko ana turo masa, sai daga baya a zo a ga abubuwa sun zama abin da suka zama,” inji Sulaiman.

Bai dace ba

Nafisa Usman, matar aure ce, ita kuma ta ce bai dace maza su hana matansu amfani da kafafen sada zumunta a.

“Sai dai a raika dan duba wace irin mu’amala take yi a kafafen sada zumuntar, ka san kowace mace da yanayinta kamar yadda kowane namiji yake da yanayi.

“Wata mahaukaciya ce, wata kuma tana da tunani ta yi aure, kuma aure martaba gare shi kuma wani abu ne mai girma idan ta dauke shi ibada ta san ibada ce take yi mai girma za ta san yadda za ta rika yin mu’amala ba kamar yadda take yin mu’amala kafin aure ba. Dole ne sai ta rika duba da wa za ta yi mu’amala da wanda ba za ta yi ba.

“Kuma su ma wadanda suke mu’amala da ita din dole sai sun san cewa wannan ta yi aure, kowa zai san matsayinsa zai gane inda ya dosa.

“Wata saboda rashin tunani ko rashin mafadi, yadda take rayuwa lokacin tana ’yan matancinta haka take tunanin za ta yi da aure, sai ka ji ana kar ta yi kaza kar ta yi kaza, kuma ba hakan nan ba ne dole ne dama idan ka yi aure wasu abubuwan sai ka hakura da su, ba kamar yadda kake lokacin kana gidanku ba saboda gudun matsala.”

Ya danganci irin matar

Isma’il Mohd, magidanci ne a Kano, ya ce, “Rashin yarda ke janyo mutum ya hana matarsa amfani da kafafen sada zumunta bayan aure.

“Amma abun dubawa a nan shi ne kafafen sada zumunta an kirkire su ne don yin amfani da su ta hanyoyin da suka dace.

“Amma wasu na amfani da su wajen yin abubuwan da ba daidai ba, indai har matar da mutum ya aura tana da tarbiyya, ta san me ta ke yi, ta san yadda ya kamata ta yi amfani da kafafen, ba na tunanin akwai matsala in dai har ta san darajar aurenta.

“Kuma ya danganta da irin matar da mutum ya aura ma tun asali, wani zai auri mace shi zai iya ganin cewa ko ba ta da kamun kai ko yanayin tarbiyyar da take da ita.

“Idan matar da ka aura ka yarda da tarbiyyarta da kuma ingancinta da hankalinta ba matsala ba ne don ta yi amfani da kafafen sada zumunta, amma in har kana ganin matarka sai a hankali to, bai dace a bar ta yi amfani da su ba,” a cewarsa.

Ire-iren wadannan da ma’auratan suka tattauna da Aminiya ne ya sa wasu mazajen ke yanke hukuncin hana matansu amfani da kafafen sada zumuntar bayan aure.

Wasu sukan sauya wa mace layin waya ko wayar ma baki daya, wasu kuma sukan sanya ta rufe kafafen sada zumuntar da take amfani da su don nema wa kansu zaman lafiya.

Shin yaya kuke gani?