✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da gaske ’yan bindiga sun nada masu unguwanni a Sakkwato?

’Yan sanda a Sakkwato sun ce labarin kanzon kurege ne ake yadawa.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Sakkawto ta karyata labaran da ke yawo cewa ’yan bindiga sun fara nada masu unguwanni a wasu yankunan jihar.

A baya-bayan nan an yi ta jita-jita cewa ’yan bindiga sun fara nada shugabanni a yankin Sabon Birni na Jihar Sakkwato bayan sun addabi  mazauna yankin da hare-hare.

Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, Sanusi Abubakar, ya fitar ta ce binciken da rundunar ta gudanar ya gano babu kamshin gaskiya a labarin da ke yawo a gari.

Ya kara da cewa rundunar na aiki babu kama hannun yaro domin dawo da kwanciyar hankali a yankunan da ke fama da matsalar tsaro a fadin jihar.

“Rundunarmu na amfani da wannan dama wajen sanar da al’umma, musamman jama’ar Jihar Sakkwato cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen muttsuke ayyukan ’yan bindiga da sauran bata-gari a fadin jihar.

“Akwai kuma aikin soji da ake ci gaba da gudanarwar bisa jagorancin rundunar hadin gwiwar sojoji da ’yan sanda ta ‘Operation Hadarin Daji’.

“Nan ba da jimawa ba rundunar za ta bi wadannan ’yan bindigar har zuwa maboyarsu ta fatattake su, domin tabbatar da ganin cewa aminci ya samu a duk yankunan da ’yan bindiga suka addaba a fadin jihar nan.”