✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shin ’yan majalisa za su iya tsige Buhari?

Yaudara ce kawai, ba za su iya tsige shi ba.

A makon jiya ne sanatoci suka yi barazanar tsige Shugaban Kasa Muhammdu Buhari saboda matsalar tsaro da ta ta’azzara a kasar, inda suka ba shi wa’adin mako shida ya kawo gyara.

Sun yi barazanar ce bayan fargabar da aka shiga a Birnin Tarayya Abuja na yiwuwar kai hare-hare a ciki da wajen gari.

Wani abu da ya ja hankalin mutane shi ne yadda sanatocin jam’iyyun adawa karkashin jagorancin Shugaban Marasa Rinjaye, Sanata Philip Aduda (PDP, Abuja) suka fice daga zaman majalisar, suna cewa “Dole Buhari ya sauka” bayan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya dakatar da tattauna batun tsige shugaban.

Haka kuma ’yan Majalisar Wakilai na PDP ma sun mara wa sanatocin baya, wanda hakan ya sa lamarin ya kara zafi.

Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Ndudi Elumelu ya ce sun amince idan bayan mako shida ba a samu wani canji ba, za su tsige Shugaba Buhari.

Wannan lamarin ya zo wa wasu ’yan Najeriya da ba-zata, inda wasu ke murnar samun labarin, suke kuma addu’ar ganin ya tabbata; yanayin da wasu kuma suka yi bakin cikin ganin labarin tare da yin watsi da shi cewa ba zai yiwu ba.

Shin zai yiwu a tsige shugaban?

Da yake mayar da martani kan batun, mai magana da yawun Shugaba Buhari, Garba Shehu ya ce kan sanatocin a rabe yake kuma suna cikin rudu ne.

Hakan ce ta sa ya bukaci su mayar da hankalinsu kan magance matsalolin da kasar ke fuskanta, wanda shi kuma Elumelu ya mayar masa da martani cewa idan suka fara yunkurin tsige shugaban ne Garba Shehun zai gane cewa ba wasa suke yi ba.

’Yan Najeriya za su jira mako shidan su gani ko ’yan majalisar za su iya cika alkawarin da suka dauka, ganin hanyar tsige Shugaban Kasa tana da matukar wahala duba da shashi na 143 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya (wanda aka gyara).

Sai dai Sanata Enyinnaya Abaribe (APGA, Abia) ya ce, “Mu dai bayar da wa’adi kuma za mu jira mu ga me Shugaban zai yi.

“Idan lokacin ya yi, za mu sake komawa majalisar mu yi abin da ya dace.”

Shi kuma Sanata Gershon Bassey (PDP, Kuros Riba) ya ce duk da cewa da gaske suke yi kan batun tsige shugaban, babban burinsu shi ne tursasa Shugaba Buhari ya dauki mataki kan matsalar rashin tsaron.

“Amma idan har wa’adin ya yi bai yi komai ba, dole mu fara yunkurin tsige shugaban kawai.”

Yaudara ce kawai, ba za su iya tsige shi ba —Lauyoyi

Barista Alzubayr Abubakar lauya ne a Jihar Kaduna. Aminiya ta zanta da shi kan wa’adin ’yan majalisa na tsige Shugaban Kasa kan matsalar tsaro.

A cewarsa, wannan wata hanya ce kawai ’yan majalisar suka dauki domin nuna wa mutane cewa suna tare da su amma sun sani ba zai yiwu ba.

“Idan mako shidan suka kai, wanda ya gabatar da wannan kuduri, zai shirya wannan kudurin muna tsammanin kafin ranar da za a shiga majalisa saboda kowane dan majalisa ya samu wannan takarda.

“Zai yiwu ma watakila cikin wa’adi ya kasance a cikin hutunsu ne, ke nan yana da lokaci kafin su dawo hutu. Idan aka ba da wannan kuduri, sai kowane dan majalisa ya duba.

“Sannan sai a yi zabe, sannan a ba da lokaci ga kowane dan majalisa ya karanta ya kuma fadi ra’ayinsa a kan wannnan kuduri, sannan a yi muhawara na yarda ko rashin yarda.

“Idan aka yi muhawara za a yi zabe kafin a sake komawa a ba da rana a yi karatu na biyu.

“Idan aka yi karatu na biyu sannan a sake muhawara, bayan an yi muhawara sai a yarda da kudurin bayan an yi zabe.

“Daga nan sai a kafa kwamiti su duba muhawarar da aka yi kuma su ba da shawara a kan kudurin. Za a ba su lokaci sai a dawo a yi karatu na uku.

“A wannan karon Majalisar Wakilai ma za su bi sahu wajen yin zaben, inda za a zauna wuri daya a yi muhawara.

“Idan aka yi muhawara daga nan sai a yi zaben karshe. Ka ga wannan bayanin da na yi, za a iya daukar shekara daya kuma ka ga zangon wannan majalisar bai kai shekara daya ba.

“Don haka suma ’yan majalisar sun fada ne kawai don ’yan Najeriya su san suna tare da su. Amman sun san ba abu ne mai yiwuwa ba domin sun san lokaci ya riga ya kure.

“Sai dai su dauki matakan da ake ganin kawai suna tare da mutanen Najeriya amma tsige Shugaban Kasa abu ne mai wuya.

Da aka tambaye shi ko yaudara ce kawai suka shirya, sai ya ce, “Ai dama in ka dubi majalisun Najeriya tun daga 1999 musamman Majalisun Tarayya ba abin da suke wa ’yan Najeriya sai yaudara kuma ba gaskiya.

“Idan ka duba ’yan dokoki da aka yi wadanda za mu iya yarda cewan sun inganta rayuwar ’yan Najeriya kadan ne, idan ka dauki abin da majalisun suke yi tun daga 1999 har zuwa yanzu, wallahi bayan rudu da yaudara da kuma tumasanci ba abin da suke yi.

“Bari in ba ka misali da abu daya wanda aka kashe biliyoyin kudi a kansu.

“’Yan majalisa sun karbi biliyoyin kudi a kan za su yi gyara a tsarin mulkin Najeriya amman a kowane zango sai ya zo ya kare za su zo su cinye biliyoyin kudi kuma ba za su yi gyaran ba.

“Ko yanzu maganar da muke din nan, ai majalisar ta dauko tsarin gyaran Kundin Mulkin Najeriya, ka kara jin maganar?

“Amma biliyan nawa aka fitar domin a yi wannan maganar gyaran?

“Saboda haka ba gaskiya ba ne yawanci wadanda muke zaba ne mu ma da laifinmu saboda lokacin da za mu kada kuri’a mun yarda wadannan mutane mayaudara ne.

“A cikinsu akwai wadanda aka zabe su tun a 1999 ba su tabuka komai ba ga mutanansu amma duk zango sai an sake zabensu. Me ya sa mutane ke haka?”

Shi ma wani lauya mai suna Barista Hameed Ajibola ya ce duk da cewa akwai matsalar shugabanci a matsalolin da kasar ke fuskanta, wanda hakan ya sa ’yan majalisar ke da hujjar yunkurin tsige shugaban, amma sai dai ba su da isasshen lokacin da za su yi wannan aiki, inda ya ce sai dai shi Shugaban Kasa da kansa ya ce ya ajiye shugabancin.

Mafi yawan sanatocin sun amince da yunkurin —Sanatan APC

Sanatan APC mai wakiltar Bauchi ta Arewa, Adamu Bulkachuwa ya ce akwai takwarorinsa da dama da ke goyon bayan yunkurin tsige Muhammadu Buhari daga shugabancin Najeriya.

A wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels, Sanatan ya ce batun tsigewar kusan shi ne abu na karshe da ya rage wa ’yan majalisar.

Ya ce shi da sauran tawarorinsa sun sha yunkurin taimaka wa bangaren zartarwa da ma Shugaban Kasa kan magance matsalar tsaron amma lamarin ya ci tura.

A cewarsa, “Lokacin da muka fahimci cewa kusan duk abin da aka yi bai yi aiki ba kuma sha’anin tsaro har ma da tattalin arziki na dada tabarbarewa sai muka fahimci cewa mu kawai wani bangare ne na gwamnati da ba shi da ikon zartarwa.

“Abin kawai da za mu iya yi shi ne mu jawo hankalin bangaren zartarwa kuma mun yi kusan duk abin da za mu iya amma babu wani sakamako, watakila barazanar tsigewar ce kawai za ta sa su yi abin da ya dace,” inji Sanata Bulkachuwa.

Da aka tambaye shi ko duk sanatocin ne ciki har da na APC suka amince da yunkurin tsige shugaban, sai ya ce, “Ba za mu ce duka sanatocin amma ina tabbatar maka cewa mafi yawan sanatocin sun amince da yunkurin tsige shugaban.”

Hanyoyin tsige Shugaban Kasa

Sashe na 143 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara) ya yi bayani dalla-dalla na yadda za a bi domin tsige Shugaban Kasa daga ofis kamar haka:

1.Aika masa wasika a rubuce na zarge-zargen da ake masa na aikata ba daidai ba, wanda dole sai akalla daya bisa ukun ’yan majalisar biyu (Majalisar Dattawa da Wakilai) sun rattaba hannu.

2.Shugaban Majalisar Dattawa dole ya mika wasikar ga Shugaban Kasa da kuma dukkan ’yan majalisar a cikin kwana bakwai.

3. Shugaban Kasa yana da damar mayar da martani, sannan duk bayanan da ya yi dole a ba kowane dan majalisa a rubuce.

4. A cikin kwana 14 da mika wasikar zarge-zargen, kowace majalisa za ta zauna ta yanke amincewa ta ci gaba da binciken ko ta dakatar.

Dole wannan ya samu amincewar akalla biyu bisa uku na mambobin kowace majalisa.

5. A tsakanin kwana biyar da amincewa da kudurin, Shugaban Majalisar Dattawa zai bukaci Ministan Shari’a ya kafa kwamitin mutane masu nagarta da za su bincika zargezargen.

Mambobin kwamitin ba za su zama ma’aikata ba ko ’yan majalisa ko ’yan siyasa da suke wata jam’iyya.

6. A lokacin binciken, Shugaban Kasa yana da damar kare kansa kuma yana da damar tura lauyoyi su kare shi.

7. Kwamitin zai mika rahotonsa a cikin wata uku zuwa ga majalisun tarayya guda biyu.

8. Idan rahoton kwamitin ya nuna ba a samu gamsasshen abubuwan da za su tabbatar da zarge-zargen ba, sai a dakatar da komai.

Amma rahoton ya gano akwai gaskiya a zargezargen, majalisun sai su zauna domin amincewa da sakamakon rahoton ta hanyar mika kudurin haka.

9. Dole akalla biyu bisa uku na majalisun biyu su amince da rahoton kafin za a amince da shi. Idan kuwa aka samu hakan, suka amince da rahoton, daga nan ta tabbata an tsige Shugaban Kasa.

10. Shugaban Kasa ba zai iya kalubalantar rahoton kwamitin ba ko aikin majalisar a kotu.

11. Mataimakin Shugaban Kasa ne za a rantsar a matsayin Shugaban Kasa.