✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin Kidaya: NPC ta nemi sojoji su bai wa jami’anta kariya

Hukumar na neman kariyar sojoji ga jami'anta saboda matsalar tsaro da ke addabar Najeriya.

Shugaban Hukumar Kidaya ta Najeriya (NPC), Nasir Isa-Kwarra, ya nemi taimakon sojoji wajen gudanar da shirin kidaya na sharar fage da kuma babban shirin wanda zai gudana a 2023.

Isa-Kwarra ya bukaci hakan ne yayin ziyarar da shi da tawagarsa suka kai Hedikwatar Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya da ke Abuja a ranar Talata.

Ya ce NPC na da bukatar yin aiki tare da sojoji domin samun zarafin gudanar da aikinta yadda ya kamata duba da kalubalen da fannin tsaron kasa ke fuskanta.

Daga nan ya ce sojojin Najeriya sun saba taka muhimmiyar rawa wajen bai wa jami’an hukumar kariya musamman idan aka yi la’akari da yadda wasu sassan kasa ke fama da matslar tsaro.

A cewar Isa-Kwarra, “Mun zo ne don neman goyon bayan da kuka saba ba mu wajen aiwatar da shirin da zai jagorance mu zuwa ga shirin kidayar da za ta gudana a watan Afrilun 2023.

“Muna so mu yi aiki tare domin tabbatar da mun gudanar kidaya karbabbe ga ’yan Najeriya a 2023,’ inji shi.

Ya kara da cewa, shirin sanya wa gidaje alama ya kammala a kananan hukumomi 774 da ake da su a fadin kasa, in banda yankin Birnin Gwari na Jihar Kaduna da kuma Abadam a Borno, sakamakon matsalolin tsaro.

A nasa bangaren, Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Manjo-Janar Farouk Yahaya, ya sha alwashin rundunarsa za ta bai wa NPC cikakken hadin kan da take bukata wajen gudanar da harkokinta yadda ya kamata.