✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin shakatawa na shekara 30 zai bunkasa tattalin arziki —Sterling Bank

Gwamnatin Jihar Osun ta ce shirin bunkasa yawon bude ido da shakatawa na jihar da hadin gwiwar Bankin Sterling zai taka rawar gani wajen samar…

Gwamnatin Jihar Osun ta ce shirin bunkasa yawon bude ido da shakatawa na jihar da hadin gwiwar Bankin Sterling zai taka rawar gani wajen samar da guraben ayyukan yi da bunkasa harkokin al’ummar Jihar Osun.

Gwamna Adegboyega Oyetola na Jihar Osun wanda ya yi furucin yayin kaddamar da shirin yawon bude Ido mai taken ‘Al’ada da Tattalin Arzikin Yawon Bude Ido (CUTOSEC)’ a garin Osogbo a karshen mako.

Ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen bunkasa tattalin arzki a jihar ta hanyar zuba jari a bangare raya al’adu da yawon bude ido da ya kai na kasar Dular Larabawa.

Ya ce gwamnatin jihar ta zama jagora wajen bunkasa harkokin yawon bude ido da shakatawa ta hanyar yin dokoki kan al’adu da yawon bude ido a ajandar jihar.

Ya bayyana cewa tsarin yawon bude ido yana da wani tsari na aiwatar da tsarin shirin rage dogaro kan man fetur na jihar tare da bunkasa kudin shigar jihar.

Gwamna Oyetola ya ce: “Yayin da yawon bude ido ke kara samun tagomashi a tsarin tattalin arzikin kasa, akwai bukatar tabbatar da an sanya hankali ga alfanunsa na tsawon lokaci. Wannan mataki na bukatar tsari mai inganci ga masana’antar nan gaba.

“A matsayinmu na gwamnati mun tsunduma cikin harkar ta hanyar kafa ginshiki mai karfi don ganin an samu bangaren yawon bude ido mai inganci a Najeriya.

“Tsarinmu na bunkasa yawon bude ido ya kunshi tsare-tsare biyu na gajare da kuma dogon lokaci.

“Shirin Sterling na bunkasa yawon bude ido na da wa’adin lokaci iri biyu – na gajeren lokaci da kuma na dogon lokacin.

“Na gajeren lokacin shi ne Shirin Kudurin Bunkasa Yawon Bude Ido na Jihar Osun (OSTOV 30-30) wanda muke niyyar amfani da shi domin kafa harsashen bunkasa harkar yadda ta dace a jihar; CUTOSEC kuma shi ne mai dogon lokaci wanda zai gina a kan nasarorin OSTOV 30-30 don bunkasa bagaren yawon bude ido na dindindin.

“Kokarin da muke yi a yanzu shi ne na kawo masu saka jari a jihar don samun alfanu. Saboda muhimmancin da jihar ta ba shi, ta fitar da kudin tsarin zuba jari musamman a bangaren yawon bude ido ta kuma wallafa dukkannin irin damar da ake da ita a jihar a shafinmu na intanet kamar Dausayin Olumirin, Dausayin Ayikunnugba, Kogin Owala, filin yaki na Kiriji da sauran wuraren yawon bude ido da shakatawa a matsayin wani bangare na shirin CUTOSEC’’.

Gwamnatin ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta kuduri aniyar tsarin hadaka da bangarori masu zaman kansu da za su dauki nauyi tare da kulawa da bukatun masu ruwa da tsaki yayin da a hannu daya ta sha alwashin bunkasa masu shiga cikin shirin.

Ya ce tsarin hadakar zai magance matsalar fili da tsarin sakayya da batun haraji da makamantansu.

Ya kara da cewa tsarin zai kyautata alaka da al’ummomi, samar da guraben ayyukan yi da walwalwa ga al’ummomin yankunan a yayin da gwamnatin jihar ta bude kofarta don sasantawa game da batun.

Jami’in Kasuwanci na Yanki na Bankin Sterling, Mista Ademola Adeyemi, ya bayyana cewa shirin OSTOV yana da muhimmanci kuma yana kusa da bankinsa saboda zai samar da guraben ayyukan yi da sanya tattalin arziki ya bunkasa da bunkasa rayuwar al’ummar Osun.

“A bankin Sterling, mun yi imanin bangaren masu zaman kansu suna da rawar da za su taka wajen tallafa wa kokarin gwamnati na bunkasa rayuwa mai inganci ga al’umma da samar da guraben ayyukan yi da rayuwa mai kyau ga kowa da kowa.

“Saboda haka ne muke kokarin bunkasa bangaren masu zaman kansu don samar da sauyi a bangaren tafiye-tafiye da yawon bude ido a Jihar Osun da Najeriya baki daya.

“Yawon bude ido kamar yadda muka sani wani bangare ne na tattalin arziki da walwala da bunkasa cigaba da kuwa dorewar muhalli.

“Wani makami ne mai karfi na yakar talauci da ke samar da damarmarki na mausamman ga kowa da kowa da suka hada da talakawa da marasa karfi’’, Inji Adeyemi.

Da yake jawabin maraba, Kwamishinan Al’adu da Yawon Bude Ido, Dakta Adebisi Obawale, ya ce damrmarkin da ake da su a abubuwan da mutane suka gada da kuma alfanun da ke akwai su ne suka sanya gwamnati bunkasa yawon bude ido a matsayin daya daga cikin ginshikai na bunkasa tattalin arzikin jihar.

Obawale ya bayyana cewa tawagar masu sanya jari da kamfanonin kudi sun ziyarci jihar a watanni kadan da suka gabata don tantance wuraren yawon bude ido kuma sun gamsu da irin al’umma da al’adu da kuma albarkatu da ake da shi.

Sakamakon haka tawagar ta bayyana aniyar bunkasa wuraren yawon bude ido na jihar, inji shi.

A jawabinsa, Mataimakin Shugaban Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, Farfesa Eyitayo Ogunmodede, ya bayyana cewa Allah Ya albarkaci Jihar Osun da wuraren yawon bude ido da za su ja hankulan masu yawon bude ido a kullum.

Ya shawarci gwamnatin jihar ta fara gyarawa tare da fadada kayayyakin yawon bude ido kamar hanyoyi da kafafen sadarwa da otel-otel da wuraren saukar baki.