✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirye-shiryen Sallah: ’Yan kaji sun koka kan rashin ciniki a Kaduna

Akasarin ’yan kasuwar sun koka kan karancin ciniki a bana

Yayin da bikin Karamar Sallah ke ta karatowa, wasu masu sayar da kaji da agwagi da talotalo a Jihar Kaduna sun koka dangane da rashin ciniki a bana.

Wadanda lamarin ya shafa sun nuna damuwarsu a mabambantan hirarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya yi da su ranar Talata a garin Kaduna.

Sun ce lamarin abin damuwa ne matuka, tare da cewa suna da kyakkyawan fatan ganin sauyi da zarar ma’aikata sun samu albashinsu na watan Afrilu.

Ziyarar da wakilin NAN ya kai a fitacciyar kasuwar kaji da ke Kantin Koli cikin Babbar Kasuwar Kaduna, ya hangi tsirarun mutane da ke hada-hadar sayen kaji da sauransu.

Wani mai sayar da kaji, Kabiru Yunusa, ya shaida wa wakilin NAN cewa duk da dai farashin kaji bai tashi ba, amma duk da haka babu ciniki.

“Bisa la’akari da nauyin kaza, ana sayar da kaza tsakanin N2,500 zuwa N4,000.

“Kaji masu saka kwai kuwa, tsakanin N1,500 zuwa N2,000 farashinsu yake, kajin Turawa (broilers) kuwa, farashinsu ya tike ne tsakanin N2,500 zuwa N4,000,” in ji Yunusa.

Shi kuwa Jamilu Abubakar mai sayar da talotalo cewa ya yi, ya dan samu cinikin kaji saura na talotalo.

Ya ce, “Talotalo sun fi tsada, domin kuwa ana sayar da madaidaicin talotalo tsakanin N9,000 zuwa N15,000.

“Da ma dai mun saba ganin haka, jama’a kan zo sayayya ko da a ranar jajiberin Sallah, don haka muna tsumayar zuwansu.”

Malam Yakubu Jibril, wanda ya hada aikinsa na gwamnati da sana’ar sayar da kaji ya ce, har yanzu bai ga budin ciniki ba duk da kokarin tallata hajarsa a kafafen sada zumunta da ya yi.

“Amma duk da haka ina da yakinin zan sai da kajin nawa kwana biyu ko daya kafin Sallah saboda ban tsauwala farashina ba idan aka kwatanta da na takwarorina,” inji Jibril.

Ya kara da cewa, “Kaza ’yar wata bakwai ana saida ita daga N3,000 zuwa sama, har na N4,000 zuwa N5,000 ana samu.”

Wani ma’aikacin gwamnati da ke zaune a unguwar Kurmin Mashi, Malam Nasir Mohammed, ya fada wa NAN cewa tsadar rayuwa ta tilasta wa wasu jama’a soma tunanin sayen kifi da naman shanu a madadin kaji da danginsu a wannan bikin Sallar.