Shugaba Buhari kunnenka nawa? (2) | Aminiya

Shugaba Buhari kunnenka nawa? (2)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
    Ibrahim Malumfashi

Abubuwan da suka faru daga 1985 da Janar Babangida ya hau karagar mulki, har hawan Earnest Shonekan na rikon kwarya da yadda kwaryar ta farfashe, Abacha ya haye karagar mulki, abubuwa ne da ba sai na sake tariyo su a nan ba, ka san su, na san su, sauran al’umma da suka rayu daga wancan lokaci zuwa yau, sun san su. Da alama kuma abin nan ne da za mu iya kira da shillon Biliya, wato mutum da ya fado daga saman itacen rimi, ya zarce cikin rijiya.

Saboda haka ya Shugabana Muhammadu Buhari! Ko da aka gayyaci ’yan siyasa a 1998 zuwa 1999 don su shiga hada-hadar siyasa da zabe, kamar yadda mawakin nan Dan Shabiyu ya fada, ‘domin a dana su, don an dauka adilai ne su, ashe ba a san azzalumai ne ba,’ ban yi mamakin da ka yi zamanka gida ka ki shiga cikin wannan hargidiballe ba, domin bisa ga dukkan alamu, siyasa ba kayanka ba ce, domin kai mutuum ne mai kaifi daya, wanda ba zai iya rawa da ’yan siyasa ba. Na dauka hakan za ta kasance da rayuwarka har abada, wato ka yi ritaya daga rigingimun mulki da siyasa da neman gyara batattun lamura.

Sai dai kamar yadda na sani daga dan kusantarka da na soma yi daga baya, lokaci ne kawai bai yi ba, za ka koma ruwa, wato za a dama da kai kai-tsaye a sha’anin mulki a kasar nan, musamman ganin shekarun da ka yi kana shugabancin Hukumar PTF, karkashin mulkin Janar Abacha, inda ina jin cewa daga nan ne aka soma kara tabbatar da kai a matsayin mutum mai kamanta gaskiya, koda kuwa wadansu wadanda kake shugabancin tare da su, ba su da tabon gaskiyar tare da su.

Ya mai girma Shugaba Muhammadu Buhari! Duk da cewa wadansu daga cikin masoyanka tun kana Shugaban Kasa a tsakanin 1983 zuwa 1985, har zuwa lokacin da kake zaune a gida da kuma lokacin da ka shugabanci PTF da kafa kungiyar The Buhari Organisation (TBO), wadda ina jin ita ce tushen shigarka tsundum cikin siyasa, ba duka suka amince da gundumawarka cikin harkokin mulki da siyasar ba, domin muna ganin za a bata maka suna ne, ko a yi amfani da kai domin a cimma wasu muradu na son rai na wadansu mutane kalilan, amma wannan bai hana ka sunsunar siyasa da kuma jingina ga wasu madafun iko da mulki ba. Wannan zabinka ne, ba kuma wanda ya isa ya hana ka. Amma amsar da ka ba ni a lokacin da na taba tambayarka a gidanka, bayan ka dawo daga shugabancin PTF, bayan an rushe ta, ina jin ita ce dalilin kutsenka cikin siyasa da kuma dagewa da amincewa da batunci daga ’yan siyasar da masoya. Na san kai kila ka manta, amma ni har yau ban manta da tambayar da kuma amsar da ka ba ni ba. Na dai ce da kai ‘shin ba ka jin ka yi nadamar karbar shugabancin PTF, ganin irin tonon sililin da ake ta yi na cewa ka yi wandaka  ko kuma wadansu na kusa da kai sun yi almubazarranci da dukiyar al’umma a matsayinka na Shugaban PTF?’ A lokacin nan na san tambayar ba ta yi maka dadi ba, musamman ganin cewa ina daga cikin wadanda ba su amince da ka amshi Shugabancin PTF ba, ina kuma gudun kada ’yan Najeriya su lalata min mai gaskiyar da nake so da kauna ne shi ya sa!

Bayan ka nisa, ka kalle ni, ka ce da ni, aikin Shugabancin PTF kira ne daga kasa don in ba da gudunmawa, kuma in za a sake nemana, in sake ba da gudunmawa zan sake karba, in yi, iya yi na. Ma’ana, ba ka yi nadamar amsar wannan matsayi da mukami ba, duk da ce-ce-ku-ce da aka rika yi daga baya.

Wannan tunani ina jin shi ne ya sa ka tsunduma a cikin siyasa daga baya, domin shi ma kamar yadda na auna, kira ne daga al’umma, mabambanta, domin ka sake ba da gudunmawa ga ceto kasar nan daga halin ha’ula’in da ta samu kanta a ciki, musamman daga ‘gurbatattun’ ’yan siyasa da suka yi ta damalmala ta tun daga 1999 ko ma fiye. Ina da yakinin wannan tunani naka ya ginu ne bisa akidar da kake da ita, ta yin aiki da shugabanci tukuru domin al’umma ba don wani abu da za a samu ba.

Sai dai bisa ga dukkan alamu, hada-hadar farfajiyar siyasa da tsarin dimokuradiyya ba naka ko na irin ka ba ne, masu kaifi daya, domin siyasa ta gaji fuska biyu da munafunci da son rai da neman abin duniya, ba tare da kishin kasa ko al’umma ba, wanda ina jin suna daga cikin abin da ya sa ka kasa kai gaci cikin sauri ko kuma ka samu tarnaki wajen gudanar da mulkin kasar nan, kamar yadda ka so. Zan dawo kan wannan nan gaba.

Za mu ci gaba