✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Buhari ya gaza!

Babu shakka Shugaba Buhari ya gaza.

A karshen makon jiya ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani hoton bidiyo na mutanen da aka kama tare da yin garkuwa da su sakamakon tare jirgin kasa da ’yan bindiga suka yi a hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda suka yi garkuwa da su.

Wannan hoton bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, inda aka nuno ’yan ta’adda na cin zarafin wadannan mutane da suka yi garkuwa da su.

An nuna yadda ake musu duka na babu gaira babu dalili haka kurum, watakila laifinsu bai wuce kasancewa a Najeriya ba.

Wannan bidiyo da ya karade kafafen sadarwa na zamani, ya matukar tayar da hankali, inda mutane da dama da suka tofa albarkacin bakinsu kan faifan bidiyo suna nuna damuwa da kaduwa a kan abin da ake yi wa wadannan fasinjojin da aka yi garkuwa da su.

Ba mu san wane irin hali dangi da iyalan mutanen za su shiga ba yayin da suka kalli wannan hoton bidiyo mai taba zukata.

Babu shakka Gwamnatin Najeriya ta gaza! Duk da irin tarin nau’o’in jami’an tsaron da muke da su a Najeriya tun daga sojan sama da na kasa da na ruwa da ’yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya da sauransu.

An kasa gano maboyar wadannan mutane da kuma inda suke tsare da mutanen da suka sace, balle a je a fatattake su a kubuto da mutanen da suke hannunsu.

Wannan na faruwa ne duk da cewa mutanen nan ana magana da su ta tarho, kuma sun saki wasu daga cikin wadanda suka sace bayan sahihan bayanai sun tabbatar da cewa an biya makudan kudade wajen fanso su.

Babu shakka, akwai takaici tattare da abin da ya shafi lamarin tsaro a Najeriya. Kai ka ce ba mu da cikakkun jami’an tsaron da suke kula da rayuka da dukiyoyin al’ummar wannan kasa.

Wadannan abubuwa na sace-sacen mutane da garkuwa da su da biyan kudin fansa, wani zubin barayin ma su ce babur suke so a sayo musu mai kafa biyu, sannan su ce a kai musu, a tuka shi a kai musu, tare da duk wannan haka ake daukar makudan kudi niki-niki a shiga cikin daji a kai wa ’yan ta’adda, amma jami’an tsaro ba su iya bin sawu ba balle su gano barayin.

Kuma duk wannan babu ko mutum guda da ake zargi a cikin jami’an tsaro da yin sakaci wajen abubuwan da suke faruwa.

Yanzu duk wadannan abubuwan takaicin da suke faruwa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayinsa na Babban Kwamandan Askarawan Kasar nan, bai taba tuhumar kowa da sakaci balle ya sa a yi bincike a gano laifinsu wane ne, a hukunta su kuma a dauki matakan gyara.

Mutanen nan suna nan kullum suna karbar albashi da alawus, amma sun gagara yin aikinsu yadda ya kamata.

Abin da kawai ke faruwa idan aka ba da labarin an sace mutane ko an kai hari gari kaza da kauye kaza, shi ne Kakakin Fadar Gwamnati, Garba Shehu ya fito ya bayyana wa duniya cewa abin da ya faru ya tayar wa Shugaban Kasa hankali ko ya ce bai ji dadin abin da ya faru ba ko kuma ya ce Shugaban Kasa ya ce ba zai sassauta wa ’yan ta’adda ba, shi ke nan zancen.

Daga wannan ba abin da za ka kuma ji sai wani abu ya faru Garba Shehu ya maimaita kalaman da aka saba ji daga bakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Babban misali na gazawa da rashin iya jagoranci na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, shi ne yadda aka kai hari Gidan Yarin Kuje da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja, aka fasa gidan yarin masu laifi suka tsere aka kone motoci a cikinsa, aka yi duk abin da aka ga dama na rashin mutunci, amma ba a tuhumi kowa ba.

Abin da kawai Shugaban Kasa ya bayyana bayan ya ziyarci gidan yarin shi ne cewa “Jami’an tsaro sun ba shi kunya!”

Daga wannan kalami babu wani abu da ya faru.

Da a ce Shugaba Buhari jajirtaccen shugaba ne, daga lokacin zai bukaci dukkan jami’an da suke da alhakin kula da tsaro a Babban Birnin Tarayya Abuja su sauka daga mukamansu a gudanar da bincike a hukunta duk wanda aka samu da sakaci.

Gidan Yarin Kuje, shi ne gidan yarin da ya fi kowanne tsaro a Abuja.

Sanin kowa ne cewa a Abuja ce Fadar Shugaban Kasa take, nan ne hedikwatocin dukkan jam’an tsaron kasar nan suke, amma a samu ’yan bindiga su shigo salin-alin su aikata abin da suka ga dama su fice lafiya lau babu wanda aka kama a cikinsu.

Bayan sun saki manyan masu laifi, daga bangaren gwamnati babu wani jami’inta da aka tuhuma da laifin sakaci wajen faruwar wadannan abubuwa, domin ta hanyar tuhuma da hukunta masu sakaci da aiki ne kawai za a dauki hanyar magance irin wadannan matsaloli.

Shugaban Buhari ya sha nanata cewa, babu wata gwamnati da ta kai tasa kashe wa jami’an tsaro kudi.

Ya sha nanata cewa ya sayo wa jami’an tsaro dukkan makamai da na’u’rorin da suke bukata, tare da haka duk wani kudi da suka bukata ana ba su a kan kari, amma abu kamar almara, kusan kullum sai an kai hari ko an sace mutane ko an kashe mutane, wasu ma ko labarin ba a ji sai bayan wani lokaci.

Duk da alwashin da Shugaban Kasa ya sha yi, har yau bai taba hukunta ko mutum guda kan laifin sakaci da aiki ba.

Watakila ma Shugaban Kasar yana ganin duk abin da suke yi daidai ne. Wannan babban abin takaici ne da ban haushi.

Batun tsaro dai shi ne Shugaba Buhari ya kalubalanci gwamnatin Jonathan da ta shude, kullum maganarsa ba a yin abin da ya dace a kan batun tsato, har ya gamsar da ’yan Najeriya cewa, duk abin da ya faru a Arewar na tsaro a baya laifin gwamnatin Jonathan ne, kuma ita ke da alhakin duk rayuka da dukiyoyin da aka rasa.

Alal hakika, Najeriya ba ta taba rashin samar da Shugaban Kasa irin na yanzu ba.

Duk abin da aka fada na kwazo da kwarewa da gogewa dangane da Shugaba Buhari ya zama labari marar tushe, domin kuwa ga shi a zahiri mun ga kishiya ko akasin abin da yake fada da abin da ake fada a kansa.

Yanzu misali da a ce ba Buhari ba ne Shugaban Kasa wadannan abubuwan suke faruwa, na tabbatar da yanzu yana kiran a yi zanga-zangar Allah-wadai da gwamnati kamar yadda ya taba yi a baya, amma yanzu ga shi a tsakiya tare da komai tattare da shi, amma mutane na mutuwa a Safana da Jibiya da Batsari da Kankara da Dansadau da Birnin Gwari!

Babu shakka Shugaba Buhari ya gaza. Muna neman Allah Ya canza mana wanda ya fi shi.