✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Buhari yana jagorantar zaman Majalisar Zartarwa

Ana gudanar da taron ne ta hanyar yanar gizo inda ministoci da dama suke halarta daga nesa.

A halin yanzu Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartarwa karo na 20 da ake gudanarwa ta Intanet a babban dakin taro na Council Chambers da ke fadarsa ta Villa a Abuja.

Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Manjo Janar Babagana Monguno, na daga cikin ‘yan majalisar da ke halartar zaman da aka fara gudanarwa da misalin karfe 10 a safiyar Laraba.

Ministocin da suka hallara sun hadar da na Ma’aikatar Labarai da Al’adu, Lai Muhammad, Ministar Kudim Kasafi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed, Ministan Shari’a, Abubakar Malami; Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire; da Ministan Ruwa, Suleiman Adamu.

Sauran Ministoci da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Dokta Folasade Yemi-Esan suna halartar taro ne daga ofisoshin su ta hanyar yanar gizo.

Taron na daya daga makamancinsa da aka bullo da shi domin kiyaye dokar bada tazara da nesa-nesa da juna a matsayin matakin dakile yaduwar cutar Coronavirus.