Daily Trust Aminiya - Trump ya umurci a bude masallatai da coci-coci
Subscribe

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump

Trump ya umurci a bude masallatai da coci-coci

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bukaci gwamnonin kasar da su hanzarta bude wuraren ibada, domin yi wa kasar addu’a.

Donald Trump ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin White House a ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu.

A cewar shugaban a daidai lokacin da lokacin da gwamnatain kasar ke ci gaba da sassauta matakan kule a kasar, akwai bukatar a bude wuraren ibada domin kasar na da bukatar addu’a.

“A yau ina magana ne a kan zaurukan  bauta da suka hadar da wajen ibadar Yahudawa, da masallatai da coci-coci, wadanda wurare ne masu mahimmanci da ke samar da mahimman ayyuka.

“Ya kamata gwamnoni su yi abin da ya kamata don bude wadannan muhimman  wurare na  ibadan a karshen mako.

“Muddin gwamnonin ba su yi abin da ya dace ba, zan yi masu kutse, na bude, domin a Amurka muna da bukatar addu’a ba ‘yar kadan ba,” in ji Donald Trump.

Ya ce ya kamata a bude wuraren ibada yadda aka bude sauran muhimman wurare irinsu wuraren sayar da magunguna, kantunan abinci, wuraren sayar da kayayyakin masarufi, da asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya da wuraren sayar da barasa.

“Wasu gwamnoni sun fi bai wa wajen sayar da barasa da asibitin da ake zubar da ciki mahimmanci, amma sun yi burus da coci-coci da saura wuraren bauta, wannan ba daidai bane” inji shi.

Kasar Amurka na sahun farko a kasashen da annobar coronavirus ta fi yi wa illa a duniya, lamarin da ya janyo salwatar rayukan dubun dubatar jama’a a kasar.

More Stories