✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Armenia, Armen Sarkissian ya yi murabus

Wannan shawara ko kadan ba abin daga hankali ba ce.

Shugaban Armenia, Armen Sarkissian ya yi murabus daga karagar mulki a ranar Lahadi inda ya bayyana rashin samun cikakken ikon riko da akalar mulkin kasar a matsayin dalilin yanke wannan hukunci.

Armen ya bayyana gazawar sa na ci gaba da shugabancin kasar da cewa matakinsa na sauka daga kujerar shugabanci bayan shafe shekaru hudu ya na mulki shi ne mafi a’ala.

Cikin wata doguwar sanarwa da Sarkissian ya gabatar, ya bayyana cewa iyaka da aka yi wa akalar jagoranci da kuma karancin ikon da shugaban kasa yake da shi a kasar ya sa aikin rike mukamin shugaban kasar yana da wahalar gaske.

“Na dade ina wannan tunani, amma yanzu na yanske shawarar yin murabus daga mukamin shugaban wannan jamhuriyya bayan na yi aiki tukuru na tsawon shekaru hudu.

“Wannan shawara ko kadan ba abin daga hankali ba ce, don na yi ta ne bisa la’akari da hangen nesa da kuma dabarun da suka dace,” a cewarsa.

Kari a kan haka, Sarkissina ya nuni da yadda rashin cikakken ikon da shugaban kasa ke da shi, ya sanya ba ya iya watsi da wasu dokoki da mahangarsa ba su da madogara da ci gaban kasar.

“Muna rayuwa ne a wani yanayi na daban sabanin yadda aka saba, inda shugaban kasa ba shi da wani tasiri a kan lamurran da shafi yaki ko zaman lafiyar kasa,”inji shi.

Bayanai sun ce murabus din Sarkissian ya yi a yanzu na zuwa ne biyo bayan takaddamar da aka yi bara tsakaninsa da Firaiminista, Niko Pashinian kan batutuwa da dama.

Armen mai shekaru 68 a duniya ya rike mukamin shugaban kasar Armenia tun a watan Afrilun 2018.