✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Chadi ya nada tsohon abokin adawar mahaifinsa Fira Minista

Sau hudu tsohon madugun adawa Saleh Kebzabo yana neman kujerar shugaban kasar Chadi amma Idriss Debby yana kayar da shi.

Shugaban Kasar Chadi, Janar Mahamat Idriss Debby Itno, ya nada tsohon abokin adawar mahaifinsa, Saleh Kebzabo, a matsayin sabon fira minista.

Tsohon madugun adawa Saleh Kebzabo mai shekara 75, ya yi zawarcin kujerar shugaban kasar Chadi sau hudu, amma mahaifin Janar Mahamat, Idriss Debby Itno, yana kayar da shi.

Janar Mahamat ya nada Saleh Kebzabo ne gabanin cikar wa’adinsa na mika mulkin kasar ga farar hula kuma bayan firimiyan kasar na wata 18, Albert Pahimi Padacke, ya yi murabus a ranar Talata.

A watan Afrilun 2021 ne aka kashe Shugaba Idriss Debby a fagen yaki, kafin babban dan nasa, Janar Mahamat mai shekara 38, ya gaji kujerarsa bisa tsarin mulkin soji.

Da farko, Mahamat ya yi alkawarin gwamnatin sojin da yake jagoranta za ta mika mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula a cikin wata 18 kuma ba zai tsaya takara ba.

Amma ana gab da cikar wa’adin ya lashe amansa, inda a karshen mako gwamnatin sojin ta kara wa’adin mika mulki da wata 24, tare da nada shi ‘Shugaban Rikon Kwarya’ kuma zai iya tsayawa takara.

A ranar Litinin aka rantsar da shi kuma a lokacin ya yi alkwarin kafa ‘gwamnatin hadin kan kasa’ cikin ’yan kwanaki.

Firimiyan kasar Chadi mai barin gado bayan rike matsayin na wata 18, Albert Pahimi Padacke, mai shekara 55, ya kasance fira ministan kasar a lokacin mulkin Idriss Debby.

A ranar Talata ne ya sauka daga mukaminsa tare da jami’an gwamnatinsa.