✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban da ya shekara 43 a mulki ya sake cin zabe

’Yan adawa a kasar na zargin shugaban da nada danginsa a manyan mukaman gwamnatinsa.

Shugaban Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya sake tsawaita wa’adin mulkinsa bayan shafe shekara 43 yana shugabancin kasar.

Teodoro Obiang Nguema Mbasogo mai shekara 80 ya tsawaita wa’adin mulkinsa ne bayan ya sake lashe zaben kasar.

Mista Obiang wanda ya fi kowanne Shugaban Kasa dadewa a kan karagar mulki – ya lashe zaben da kashi 95 cikin dari na kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar makon da ya gabata.

“Zaben ya sake tabbatar mana da nasara” in ji Mataimakin Shugaban Kasar, Teodoro Nguema Obiang Mangue – wanda da ne ga Shugaban Kasar.

An samu ’yan takara a jam’iyyun adawa a zaben, to amma dama ba a yi tunanin za su iya cin zaben ba.

’Yan adawa a kasar na zargin shugaban da nada danginsa a manyan mukaman gwamnatinsa.

Mista Obiang ya karbi mulkin kasar a shekarar 1979 bayan juyin mulkin soji.

A tarihin kasar, shuganni biyu kacal aka taba samu tun bayan samun ’yancin kai da ta yi daga gwamnatin Sfaniya a 1968 – Obiang da kawunsa Francisco Macias Nguema, wanda ya yi wa juyin mulki a 1979.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na zargin shugabannin biyu da take hakkin bil adama.

Equatorial Guinea kasa ce mai arzikin mai wadda yawan al’ummarta bai wuce kimanin miliyan 1.5 ba.