✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Faransa ya kamu da COVID-19

Fadar Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron a ranar Alhamis ta tabbatar da cewa shugaban ya kamu da cutar COVID-19.

Fadar Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron a ranar Alhamis ta tabbatar da cewa shugaban ya kamu da cutar COVID-19.

Hakan dai ya biyo bayan fara bayyanar wasu alamomi a jikinsa, wanda hakan ya kawo cikas ga kokarin da yake yi na zuwa kasar Lebanon a mako mai zuwa.

Fadar shugaban ta ce zai killace kansa na tsawon mako daya, duk da yake ba ta yi cikakken bayani a kan yanayin alamun cutar ba.

Sanarwar fadar ta ce shugaban zai ci gaba da aiki daga gida.

Kazalika, rahotanni sun ce Firaministan kasar, Jean Castex shi ma za a killace she saboda an gano ya yi hulda da shugaban, ko da dai shi bai nuna alamu ba tukunna.

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel shi ma za a killace shi saboda ya halarci wani taro a birnin Paris na Faransa wanda shugaba Macron din ya halarta.

Shugabannin kasashe da dama dai ya zuwa yanzu ciki har da Firaministan Birtaniya, Boris Johnson, Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Brazil, Jair Bolsonaro duk sun taba kamuwa da cutar.

Tun barkewar cutar, sama da mutane miliyan biyu da dubu 400 ne suka kamu da cutar a kasar ta Faransa, sama da 59,000 kuma suka mutu.